Hadarin Turai a kan kasashe masu tasowa

Kowa zai yi mamaki da jin yadda kasashen Turai da Am urka ke yin barazanar janye taimakon da suke bai wa Najeriya idan gwamnati ba ta halatta wa masu luwadi da madigo yin auren jinsi ba. Bacin Allah (SWT) Mai kowa, Mai komai, wanda ya halicce mu Ya tanadar mana da duk abubuwan da muke […]

Hadarin Turai a kan kasashe masu tasowa
Hadarin Turai a kan kasashe masu tasowa

Kowa zai yi mamaki da jin yadda kasashen Turai da Am urka ke yin barazanar janye taimakon da suke bai wa Najeriya idan gwamnati ba ta halatta wa masu luwadi da madigo yin auren jinsi ba. Bacin Allah (SWT) Mai kowa, Mai komai, wanda ya halicce mu Ya tanadar mana da duk abubuwan da muke bukata mu yi kyakkyawar rayuwa, mu bauta Masa shi kadai, ba tare da yi masa kishiya ba, wanda ya halatta yin aure tsakanin mace da namiji, ya haramta zina, ya yi gargadi da kada a kusanci zina, luwadi da madigo. Ya yi umarni a yi hukuncin kisa ta hanyar rajamun ma’auratan da da suka aikata, da sauran hukunce-hukunce a kan sauran laifuka kamar yadda yake a cikin Alkur’ani Maigirma.
Ga hadisan Annabi (SAW) Khamsin bi khamsin da yake cewA: Matukar al’ummarsa (mu ken an) suna yin zina/luwadi da madigo – Allah zai saukar mana da annobar mutuwal; matukar muna yin algus da tauye mudu, Allah zai kwashe albarkar duka bin da aka samu; idan ba a cika alkawari makiya za su rinajey mu; idan ba a fitar da zakka, Allah zai jarrabemu da fari da yunwa; idan ba a yin hukunci da littafin allah Mai girma za a shiga dimuwa.
Sai ga wasu manyan malamai masu wa’azi sun yi shiru a kan wadannan, wasu ma har Amurka ake gayyatar su, su bada hadin kai, a bar dokokin Allah a koma na Amurka da Turai. Hatta Paparoma da ya kori limaman coci-coci da aka samu suna lalata samari da yara, sai ga Majalisar dinkin Duniya ta ce wannan bai wadatar ba, har sai an hukunta duk wadanda suka lalata yaran, an biya wadanda suka yi wa fyade diyya, an janye tsarin hana limaman coci-cocin yin aure yadda Allah (SWT) ya halatta a yi.
kasarmu da Allah Ya yi wa dimbin arzki wacce ake yi wa sata ta fitar hankali, waccce babu wata kasa da za a yi wa irin wannan satar ba ta rushe ba. A sata daya ake star Dala biliyan 50 a bangaren mai kurum, ba tare da an daina ba, kullum ci gaba ake yi da yin satar man babu kama hannun yaro, saboda hadin kan miyagun shugabanni azzalumai, fajirai, matsafa.
A nan nake kira ga dukkan kungiyoyi masu zaman kansu, kada su dogara da kowane irin taimakon Amurka da Turai wajen gudanar da ayyukansu na alkhairi da ba su saba wa dokokin Allah ba. Misali, kungiyarmu ta Rundunar Adalci ta Najeriya – Mobement for Justice in Nigeria (MOJIN), karkashin shugabancina, ta sha karbar bakuncin wasu manyan mutane daga Amurka da Turai sun ziyarce ni a ofishina na Beuirut Road – Kano, inda na fhaimci suna kokarin su rika taimaka mana duk lokacin da muke bukata. Muhimmai daga ciki sun hada da tsohon Jakadan Amurka da aka yi wa canji daga Saudiyya zuwa Najeriya, lokacin Janar Sani Abacha, kafin ya je ofishin Ministan Harkokin Waje, Tom Ikimi, sai da ya zo ofishina muka dauki sa’o’i fiye da uku muna tattaunawa; haka ya hakura ya tafi ba tare da samun hadin kaina ba. Haka abin ya kasance da na Ingila, shi ma da ya zo muka shafe sa’o’i fiye da uku bai samu hadin kaina ba. Sun sha ganin rubuce-rubuce da hirar da na sha yi a jaridu da mujallu, sun ga kundin tsarin gudanar da Rundunar adalci ta Najeriya, al’amarin da ya kunshi wasu muhimman abubuwa har da amsoshin wasikun da muka rubuta wa duk manyan alkalan kasar da kwmaishinonin ’yan sanda har da Sufeto Janar, musamman amsoshin da alkalin alkalan Najeriya, da wasu manyan alkalan jihohi da suke manne a cikin kundin.
Rashin hadin kan da ba su samu ba, ya biyo bayan aunawa da na yi, idan har suka ba mu taimako muka karba, suna iya yin tasiri a kanmu duk lokacin da suke so su yi amfani da mu wajen yin abubuwan da ba su dace da addininmu/da al’adarmu ba. Hakan shi ne bambanci tsakanin Rundunar Adalci ta Najeriya – MOJIN da wasu kungiyoyi masu neman tiamakon Turai da Amurka da sauran masu aikata barna (kishiyar adalci), da suka dauke mu barazana a garesu. Ga shi wasu malamai ma masu wa’azi ba sa iya yin katabus a kan sai an rika hukunta masu zina da/luwadi da/madigo da auren jinsi, wasunsu ma suna ganin haddin zai shafe su kai tsaye, duk yawancin masu gudunmu wannan shi ne dalili. Sun fi so su ji kunyar lahira a kan su ji ta duniya. Saboda ba su da alamar yin imani da lahira, tunda ba su jin tsoron Allah, balle su ji kunyar idon mutane. Sun fi karkata ga Amurka da Turai tunda sun yi tarayya kan saba wa Allah. \
Muna fata Allah Ya shiryemu, mu gane mu rabu da kowa mu kama Allah, mu yi riko da igiyar Allah kada mu rarraba. Mu tsaya a kan Kitab wassunnah, da imani na tsarkin zuciya, ta yadda za mu samu taimakon Allah (SWT), tun daga duniya zuwa tashin alkiyama. Yin hakan shi ne mafita daga sharrin Turai da Amurka da hadarin yin wata ma’amala da Yahudawa da Nasara da munafukai, masu burin yi mana musaya da auren jinsi, maimakon musayar fasahar kere-kere (technology). Suna ta jawo annobar mutuwa da ci baya tun daga duniya, ga tabewa a lahira. Allah Ya tsaremu, amin!
Alhaji AbdulKarim dayyabu, shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN) 08023106666, 08060116666.