Hadarin zaben ashararai da wawaye a matsayin shugabanni (1)
Huduba ta Farko: Hamdala da taslimi:Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ina yi muku wasiyya da ni kaina da jin tsoron Allah, domin babu tsira a duniya da Lahira, sai da tsoron Allah, kuma tsoron Allah shicne tushen dukkan alheran duniya da Lahira.Ya ku’yan Najeriya! Ya kamata mu tuna cewa a halin yanzu muna tunkarar […]
Huduba ta Farko:
Hamdala da taslimi:
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ina yi muku wasiyya da ni kaina da jin tsoron Allah, domin babu tsira a duniya da Lahira, sai da tsoron Allah, kuma tsoron Allah shicne tushen dukkan alheran duniya da Lahira.
Ya ku’yan Najeriya! Ya kamata mu tuna cewa a halin yanzu muna tunkarar zaben bana, (2015). Idan ba mu ji tsoron Allah muka yi abin da ya kamata na zaben nagartattun shugabanni ba, ina tabbatar muku (Allah Ya kiyaye) cewa abin da muke ji ko gani a yau na bala’i da talauci da zubar da jini da cin hanci da rashawa da rashin iya shugabanci da raba kan ’yan kasa da sunan addini ko kabilanci da sauransu, zai zama wasan yara. Kuma ba zubar da hawaye ba, wallahi idan ba mu yi hankali ba har kukan jini sai mun yi.
Gashi nan dai ya bayyana, duk abin da muke gaya wa mutane ya fito fili karara. Kowa na kallo da jin abin da ke gudana a wannan kasa tamu mai albarka Najeriya. Saboda haka, yanzu ya rage namu, kodai mu sadaukar da duk abin da Allah Ya hore mana na ilimi da dukiya da karfi da lokaci da wayo da dabara da hankali da gogewa da sauransu, mu ceto kasar nan daga rugujewa, mu ceto ta daga rubabben shugabanci na danniya da rashin kwarewa da Fir’aunanci da duniya ta shaida, ko kuma dukkanmu sai mun yi da-na-sani.
Idan muka ci gaba da zama wawaye ko makwadaita, marasa kishin kasa da al’umma, to ya rage namu. Saboda haka, ’yan siyasa da sarakuna da malamai da fastoci da shugabannin addini Musulmi da Kirista da ’yan kasuwa da shugabannin al’umma da talakawa da jami’an tsaro, ku sani hakkin ceton kasar nan ya rataya a wuyanku. Ku manta da kwadayin abin duniya, ku manta da bambance-bambance, mu hadu mu yi aiki tare, domin ganin wannan kasa tamu mai albarka ta dawo mai mutunci da zaman lafiya da kwarjini a idon duniya.
Ku sani bala’i da talauci da masifa, babu ruwansu da ko kai wane ne. Babu ruwansu da kai Musulmi ne ko Kirista, babu ruwansu da yarenka ko jiha ko yankin da ka fito.
Ya ku ’yan Najeriya! Don Allah ku kalli yadda kasarmu ta zama yau, ku kalli yadda mutuncin jami’an tsaronmu ke neman zubewa. An ki a ba su kyakkyawar kular da ta dace da kayan aiki domin tunkarar matsalar rashin tsaron da ke addabar kasarmu. Ku kalli yadda ran dan Adam ya zama arha a kasar nan sakamakon rashin shugabanci nagari da zai kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shin za mu ci gaba ne da dora maslaharmu a saman maslahar al’umma baki daya? Ta ya ya za mu yi ta cika masallatai da coci-coci kullum da sunan ibada, amma duk na neman zama na banza, saboda mun kasa hada kai mu tabbatar da shugabanci nagari a kasarmu, har an wayi gari kasarmu na neman zama abin dariya a idon duniya? Shin mun manta cewa dukkanmu za mu mutu mu bar abin da muka tara a nan duniya ne? Mun manta za mu tashi a gaban Allah gobe kiyama mu amsa tambayoyi a kan yadda muka aiwatar da rayuwarmu a duniya ne?
Ya ku ’yan Najeriya! Ku sani, lallai shekarar 2015 ita ce shekarar da za mu gane cewa shin mun yi hankali ko kuwa har yanzu muna nan gidadawa, sako-tumaki-balle jakai? Ita ce shekarar da za mu gane, shin mun koyi darasi a jikin da muke ji, ko har yanzu ba mu gane komai ba? Ita ce shekarar kwatar kai, ita ce shekarar da in har ba mu samar da canji a wannan kasa ba, to, babu lokacin da za mu iya samar da shi.
Ya ku ’yan Najeriya sama da miliyan 170! Lallai mu sani, gyaruwar al’umma ta ta’allaka ne a kan gyaruwar shugabanni, kuma lalacewar al’umma ta ta’allaka ne a kan lalacewar shugabanni. A duk lokacin da shugabanni suka zama na kirki, masu kishin kasa da al’ummarsu, ana sa ran mutane su zama na kirki. Haka duk lokacin da shugabanni suka zama na banza, tambadaddu, to lallai mutane haka za su kasance domin a inda akuyar gaba ta sha ruwa, ta baya ma nan za ta sha. Shi ya sa Musulunci ya ba da muhimmanci sosai a kan cewa shugabanni su zamo mutanen kirki ba ashararai ba, adilai ba azzalumai ba, yin haka zai sa zaman lafiya da ci gaba su yawaita a kasa, soyayya da kaunar juna su watsu.
Hakika Annabi (SAW) ya ba da labari cewa; yana daga alamomin tashin Alkiyama; ya kasance ana shugabantar da mutanen banza, jahilai, wadanda ba sa neman shiriya da Littafin Allah da Sunnar ManzonSa (SAW), kuma ba sa jin nasiha, ba sa wa’aztuwa, ba sa kwatanta adalci a tsakanin ’yan kasa kuma ba sa daukar shawara.
Imamu Ahmad da Al-Bazzar sun ruwaito Hadisi daga Jabir dan Abdullahi (RA), ya ce; “Lallai Annabi (SAW) wata rana ya ce wa Ka’ab bin Ujrata (RA): “Allah Ya tsare ka, Ya kiyaye ka, ya kai Ka’ab daga riskar shugabancin ashararai, wawaye; sai Ka’ab ya ce: “Mene ne shubagancin ashararai, wawaye, ya Manzon Allah?” Sai Annabi ya ce: “Wasu shugabanni ne da za su zo nan gaba, ba sa bin shiriyata, kuma ba sa bin tafarkina. Saboda haka duk wanda ya gaskata su a kan karyarsu kuma ya taimake su a kan zaluncinsu, to, ba ya tare da ni, kuma ba na tare da shi, kuma ba zai taba shan ruwan tafkina ba. Kuma duk wanda bai gaskata su a kan karyarsu ba, kuma bai taimake su a kan zaluncinsu ba, to wadannan suna tare da ni, kuma ina tare da su, sannan za su sha ruwan tafkina.” Annabi (SAW) ya ci gaba da cewa:”Ya Ka’ab bin Ujrata! Ka sani azumi garkuwa ne, kuma sadaka tana kau da zunubi, Sallah neman kusanci ne zuwa ga Allah, ko kuma hujja ce. Ya Ka’ab bin Ujrata! Ka sani duk wata tsoka da ta ginu da haram, to har abada ba za ta shiga Aljanna ba, kuma wuta ita tafi cancantarta. Ya Ka’ab bin Ujrata! A kullum mutane suna yin sammako, akwai wanda zai sayar da rayuwarsa, akwai wanda zai ’yanto ta, ko ya halakar da ita.” (Ahmad da Bazzar suka ruwaito)
Ya ku mutane! Ku sani, shi mutumin banza, jahili, shi ne mai karancin hankali, mai karancin tunani, mara hangen nesa, wanda ko kansa ba zai iya shugabanta ba, balle ya shugabanci waninsa. To ’yan uwa, irin wannan mutum yaya za a yi ya shugabanci sama da mutum miliyan 170? Idan ’yan kasa suka yi sakaci zai yi, amma kasar za ta susuce ta tabarbare ta lalace!
A wani Hadisin, Annabi (SAW) ya ce: “Alkiyama ba za ta tsayu ba har sai ya kasance munafukan cikin al’umma da wawayenta su ne suke yin shugabanci.” (dabarani ya ruwaito).
Munafukai da wawaye za ka same su masu karancin imani, masu karancin tsoron Allah, makaryata, jahilai, azzalumai, mayaudara, barayi, marasa tausayi, wadanda kansu kawai suka sani, sai ’ya’yansu da iyalansu da abokansu. Babu ruwansu da sha’anin talakawa da al’umma.
Ya ku bayin Allah! Lallai idan aka wayi gari shugabanni sun kasance ashararai, mutanen banza, jahilai, wawaye, to, lallai al’amari zai lalace! Sai a wayi gari ana girmama mutanen banza a gwamnati, ana wulakanta mutanen kirki. A yarda da mayaudara, a wulakanta masu amana, ya kasance jahilai marasa mutunci, tsageru, ’yan ta’adda da suka kware wajen iya cuta da magudi da sharri, su ne masu fada-a-ji a gwamnati. Masana dattawa mutanen kirki ba su da bakin magana, ko sun yi ba ta da tasiri da matsayi a wurin gwamnatin, saboda gwamnati ce ta ’yan iska, gwamnati ce ta barayi, ’yan ta’adda, mashaya jinin dan Adam, ’yan giya, marasa mutunci!
Babban malami Imam Sha’abiy (RH) yana cewa; “Alkiyama ba za ta tsayu ba har sai an wayi gari ilimi ya koma ana kallonsa jahilci, jahilci kuma ana kallonsa ilimi.” Wannan duk zai faru ne a zamanin da al’amura suka birkice, suka lalace, suka rincabe aka rasa shugabanni nagari.
Kuma Annabi (SAW) ya fada a Hadisin Abdullahi dan Umar (RA) cewa: “Lallai yana daga alamomin kusantowar Alkiyama; za a dankwafar da mutanen kirki, kuma a daukaka mutanen banza, ashararai.” (Hakim ya ruwaito a Al-Mustadrak).
Ya ku ’yan Najeriya! A yau duk wanda yake raye shaida ne a kan cewa lallai duk abin da Annabi (SAW) ya ba da labari shi ne ke faruwa. Domin an wayi gari mafi yawan wadanda ke shugabantarmu ashararai ne, sai fa ’yan kadan daga cikinsu.
Saboda haka ya zama wajibi a gare mu kowa ya yi kokari ya ba da gudunmawa gwargwadon ikonsa, don ya zamo wadanda za su shugabance mu a nan gaba, (musamman a zaben 2015) mutanen kirki ne.
’Yan uwana ’yan Najeriya! Mu sani, wallahi lokacin yin shiru ya wuce, ba zai yiwu ba a ce mutanen banza ke jagorantar mu. Mu sani, dukkanmu Allah Zai kama mu da laifin rashin tabuka komai, a kan samar wa al’umma nagartattun shugabanni. A yau dukkanmu shaidu ne kan irin halin da kasarmu da yankinmu mai albarka na Arewa suka shiga, saboda rashin shugabanci nagari. To abin da ya faru ya riga ya faru, yanzu abin tambaya shi ne; me muke yi domin kokarin samar da shugabanni na kwarai, masu amana? Ko har yanzu barci muke yi ba mu farka ba?