Hadarin zaben ashararai da wawaye a matsayin shugabanni (2)
Masallacin Juma’a, Nagazi, Okene, Jihar Kogi Ya ku bayin Allah! Mu sani lallai asalin shugabanci shi ne; a shugabantar da wanda ake ganin ya dara kowa ilimi da adalci da gaskiya da amana da lafiya da rashin nuna bambanci ga ’yan kasa, mai kokarin hada jama’ar kasa da rashin son kai, mai kishin kasa kuma […]
Masallacin Juma’a, Nagazi, Okene, Jihar Kogi
Ya ku bayin Allah! Mu sani lallai asalin shugabanci shi ne; a shugabantar da wanda ake ganin ya dara kowa ilimi da adalci da gaskiya da amana da lafiya da rashin nuna bambanci ga ’yan kasa, mai kokarin hada jama’ar kasa da rashin son kai, mai kishin kasa kuma gogagge, gwarzon namiji, jarumi da sauransu. To amma a yau abin ba haka yake ba, domin fasikai, mutanen banza, ashararai, mayaudara, mashaya, barayi, wadanda ba su san kimar dan Adam ba, ke shugabantarmu. Saboda suna da kudi, ko don dangartakarsu, ko wani matsayi da suke da shi, ko saboda tsabagen rashin kunyarsu, ko don ’ya’yan manya, amma ba don cancanta ba. Duk wannan saboda lalacewar al’amura ko saboda mutanen kirki sun yi saranda, sun rungume hannuwa, sun zama matsorata, sun mika wuya, sun ce su babu ruwansu da siyasa, sun yarda mutanen banza sun ci su da yaki.
Ya ku ’yan Najeriya! Awfu bin Malik (RA) ya ruwaito Hadisi cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafifitan shugabanninku su ne wadanda kuke kauna, kuma suke kaunarku, kuke yi musu addu’ar alheri, su ma suke yi muku. Sannan mafi lalacewar shugabanninku, su ne wadanda kuke fushi da su, suke fushi da ku, kuna la’antarsu, su na la’antarku.” (Muslim ya ruwaito).
Saboda haka ya ku al’umma! Wallahi ya zama wajibi a gare mu, manyanmu da shugabannin siyasarmu da sarakunanmu da shugabannin addinanmu da manyan masu kudinmu da ’yan kasuwarmu da ’yan bokonmu da talakawanmu da jami’an tsaronmu da ’yan jaridarmu da duk wani mai ruwa da tsaki game da samar da shugabanci nagari a kasar nan, mu hada hannu da karfi mu ga cewa lallai wannan kasa tamu mai albarka Najeriya, ta samu shugabanci nagari. Idan ba haka ba, wallahi dukkanmu Allah zai kama mu da laifin yin sakaci, gobe kiyama.
Saboda haka mu ji tsoron Allah! Ya ku muminai mu koma ga Allah! Mu nemi kusancin Mahaliccinmu. Mu roki Allah shiriya da tabbatuwa a kan gaskiya, mu tuba zuwa ga Allah baki daya, ko ma samu rabauta.
Huduba ta Biyu:
Bayan yabo da godiya ga Allah.
Ya ku bayin Allah! Lallai na daga cikin abin da hudubarmu ta yau take tsokaci a kai cewa; “Ba za ka taba samun mutanen kirki masu gaskiya suna zabe ko goyon bayan zulunci da azzaluman shugabanni ba.”
Ya ku bayin Allah masu girma! Mu sani, Allah (SWT) Ya yi umarni da adalci da goyon bayan adalai a duk inda suke, kuma Ya yi hani da zalunci da goya wa zalunci da azzalumai baya a duk inda suke. Allah Ya fada a cikin LittafinSa Mai girma cewa: “Lallai Allah Yana yin umurni da adalci da kyautatawa da umarni a bai wa ma’abucin zumunta, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci. Yana yi muku gargadi, tsammaninku kuna tunawa.” (Nahli: 90)
Allah Yana cewa: “Kada ku karkata zuwa ga (ku goyi baya/ko ku zabi) wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku. Kuma ba ku da wadansu majibinta baicin Allah, sannan kuma ba za a taimake ku ba.” (Hud:113).
Ya ku Musulmi! Lallai cikin wadannan ayoyi masu girma, mun ga yadda Allah Ya umarce mu da tsaida adalci da kuma cewa kada mu yarda mu goyi bayan azzalumai. Mahaliccinmu Ya tabbatar da cewa in muka ki bin umurninSa, to, lallai azabar wuta za ta shafe mu tare da azzaluman da muka goyi bayansu.
Mu kalli rayuwarmu a yau, shin muna bin umurnin Allah? kiri-kiri za ka ga mutum ya goyi bayan azzalumi ba don komai ba, sai don jam’iyyarsu daya ko yarensu daya, ko addininsu daya, ko garinsu daya, ko jiharsu daya, ko kasarsu daya, ko yanki daya suka fito. Shin wannan mummunar dabi’a za ka same ta a wurin mutumin kirki? Yau an wayi gari ba mu kyamar zalunci da azzalumai saboda kwadayin abin duniya da son zuciya.
Mu kalli yadda cin hanci da rashawa suka yi katutu a Najeriya, Allah Ya albarkaci wannan kasa da duk nau’o’in albarkatu, amma saboda zalunci da cin hanci da rashawa da rashin adalcin shugabanni, an wayi gari kasar tana neman rushewa. A yau kowane fanni ka duba za ka ga ba inda zalunci bai yi katutu ba. Bayan wannan, babban bala’in ma shi ne goyon bayan masu zaluncin don abin duniya, ko wata bukata ta kashin kai. Wannan ya jawo ba a gudun aikata zalunci domin mutane sun san duk zaluncin da za su yi, duk satar da za su yi, matukar suna da abin hannu, to al’umma za ta karbe su hannu bibiyu, a girmama su, a ba su sarautun gargajiya ko digirin girmamawa ko wani matsayi a cikin al’umma.
Ku sani lallai idan aka wayi gari al’umma ta zama haka, to sai dai a ce Allah Ya kiyaye, domin tabbas Allah zai jarrabi al’umma da abubuwa marasa dadi masu yawa, kamar yadda muke gani a yau.
Lokaci ya yi da za mu dakatar da wannan mummunar dabi’a domin Allah Ya dube mu da idon rahama, Ya tausaya mana, Ya kawo muna karshen wadannan bala’ o’i da suka addabe mu musamman rashin tsaro da sauransu.
Saboda munin zalunci, Allah Ya ce lallai Ya haramta wa kanSa zalunci, kuma Ya sanya shi ya zama haramun a tsakaninmu, saboda haka ya ce, kada mu zalunci juna. Amma duk mun manta da umarnin Allah, an wayi gari muna goyon bayan azzalumi saboda dan uwana ne, ko addininmu daya, ko dan jami’yyata ce, ko yarena ne, ko don kwadayin abin hannunsa. Kuma da wannan mummunar dabi’a, wai mu ce mu Musulmin kwarai ne, ko mu ce mu mutanen kirki ne! Shin muna nufin za mu yaudari Allah ne? Ya kamata mu shiga taitayinmu domin Allah ba abin wasa ba ne.
Imam Ibnu Kasir a yayin da yake bayani game da ayar da ta yi hani a kan goyon bayan azzalumai da ke cikin Suratul Hud: 113, ya ce: “Fadin Allah cewa, “Kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku.” Aliyu bin dalha ya ruwaito daga dan Abbas cewa, ma’anarta: “Kada ku mika wuya ga azzalumai.”
Imam Al-Aufiy ya ruwaito daga dan Abbas (RA), cewa: ma’anarta ita ce, “Kada ku karkata da goyon bayan shirka da zalunci.” Kuma Abul-Aliyah ya ce, ma’anarta, “Kada ku yarda da aikin zalunci da ayyukan azzalumai.” Shi kuwa Imam Ibnu Jarir ya ruwaito daga dan Abbas (RA) cewa, ma’anarta: “Kada ku karkata ku goyi bayan azzalumai.” Daga karshe Ibnu Kasir ya ce, zance mafi kyau game da fassarar ayar, shi ne; “Kada ku taimaki azzalumai a kan zaluncinsu, ta hanyar goyon bayansu. Domin duk wanda ya aikata haka, to ya yarda da aikinsu na zalunci ke nan.”
Lallai mu san wannan aya ta kai matuka wajen hani a kan zalunci da goyon bayan azzaluman shugabanni. To idan Allah Ya yi tanandin azabar wuta ga wanda ya karkata ga azzalumai, to ina ga wanda ya yi dumu-dumu cikin goyon bayansu ta hanyar yi musu kamfen na siyasa da sauransu don abin da zai samu a hannunsu?
Lallai ko shakka babu goyon bayan zalunci da azzalumai haramun ne, Allah Ya hana. Sannan yana daga zunubai masu girma, (Kaba’irai). Domin Allah Ya yi alkawarin narkon azaba a kan wannan. Sannan mu sani, abin da kawai ya halatta mu yi ga azzalumi, shi ne mu taimake shi mu hana shi yin zaluncin, idan shugaba ne mu hana shi ci gaba da shugabancin ta hanyar da doka ta yi tanada, (kamar zabe).
Imam Al-Zamakhshari ya ce: “Hani a kan goyon bayan azzalumai ya hada da kada ka shiga cikin bin son zuciyarsu, ka nisance su, kada ka yi abokantaka da su, kada ka zauna da su, kada ka ziyarce su, kada ka yi shiru a kan zaluncinsu, kada ka nuna amincewarka a kan zaluncinsu, kada ka yi kamanceceniya da su, kada ka kwaikwaye su ta kowace fuska, kada ka yi kwadayin abin hannunsu, kada ka yabe su ka nuna cewa su masu girma ko mutunci ne, kada ka nemar musu jama’a da magoya baya (yi musu kamfe).”
Kuma an ruwaito cewa: “Babban malami daga cikin magabata da ake kira Al-Muwaffik, wata rana yana Sallah a bayan wani limami, sai limamin ya karanta Suratul Hud, da ya kawo daidai aya ta 113 inda Allah ke maganar “Kada ku karkata ku goyin bayan azzalumai, idan kun yi haka wuta za ta shafe ku.” Sai Al-Muwaffik ya fadi a kasa magashiyyan ya suma, a lokacin da ya farfado sai aka tambaye shi, gafarta Malam me ya faru ne? Sai ya ce, “Wannan ayar tana nufin Allah zai azabtar da wanda ya goyi bayan azzalumi ne, to ina ga azzalumin kansa?” Sai ya ce wannan shi na tuna sai ya tsoratar da ni, hankalina ya tashi ya sa na suma.”