Hadarin zaben ashararai da wawaye a matsayin shugabanni (3)
Saboda haka ya ku ’yan Najeriya! Mu ji tsoron Allah, kuma mu sani wallahi ba za mu kawo karshen zalunci ba, har sai mun daina goyon bayan mulkin azzalumai mulkin danniya. Sai mun kyamace su da abin da suka mallaka. Amma muddin azzalumi zai yi zalunci ya tara abin duniya ta hanyar zalunci, kuma mu […]
Saboda haka ya ku ’yan Najeriya! Mu ji tsoron Allah, kuma mu sani wallahi ba za mu kawo karshen zalunci ba, har sai mun daina goyon bayan mulkin azzalumai mulkin danniya. Sai mun kyamace su da abin da suka mallaka. Amma muddin azzalumi zai yi zalunci ya tara abin duniya ta hanyar zalunci, kuma mu je muna kwadayin wannan abin nasa, muna girmama shi saboda abin duniya, to ba yadda za a yi zalunci ya kare a cikin al’umma.
Ya ku ’yan Najeriya! Lallai zaben 2015 ya iso, wannan lokaci mai matukar muhimmanci ne ga rayuwarmu, lokaci ne mai tsada. Wane irin shiri da tanadi muka yi dominsa? Shin mun san muhimmanci da tasirin zaben shugabannin kwarai ga rayuwarmu? Shin za mu sake yarda da duk wani mayaudari? Ko za mu ci gaba da jefa rayuwarmu da ta ’ya’yanmu da jikokinmu cikin hadari? Shin har yanzu barci muke yi ko mun farka? Shin za mu yarda mu ci gaba da rayuwa cikin kaskanci da wulakanci? Shin za mu yarda mu ci gaba da rayuwa irin ta bayi? Duk amsoshin wadannan tambayoyin da sauransu za mu fahimce su ne a zaben 2015, in Allah Ya sa muna raye.
Mu duba yadda tsananin yunwa da fatara da talauci da cututtuka da rashin tsaro da rashin hanyoyi masu kyau da rashin kyakkyawan ruwan sha da rashin magani a asibiti da rashin ingantattun makarantu, yara ba karatu, marasa lafiya ba magani, addini ba kulawa, marayu da gajiyayyu an yasar da su, duk da irin dimbin arziki da masu arzikin da Allah Ya hore wa kasar nan. Wai a cikin irin wannan hali da yanayi ake son mu yi fatar tabbatuwar wannan irin bakin mulki, mulkin da babu kwarewa ba tausayi da imani a cikinsa?
Ya ku Jama’a! Lallai ya zama wajibi a kan duk wani dan Najeriya ya yi wani abu domin samun canjin shugabanci a wannan kasa. Ya zama dole mu zabi shugaba adali, mai kishin kasa, mai son ’yan kasa, mai kokarin hada kan ’yan kasa, jarumi, gwarzo, mara tsoro, wanda ya fahimci kasar nan, wanda zai bai wa kowa hakkinsa ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Dole ne mu zabi shugaba mai hankali, mai cika alkawari, mai daukar shawara, mai sauraron bukatu da matsalolin ’yan kasarsa. Shugaba wanda zai kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasarsa, shugaba wanda zai ba kowa hakki da ’yancin yin addininsa ba tare da tsangwama ko nuna bambanci ba. Shugaba wanda zai yi kokarin wadata ’yan kasa da kayayyakin inganta rayuwa, shugaban da zai yi kokarin hana satar dukiyar al’umma, ya hana cin hanci da rashawa. Shugaba wanda yake mai gaskiya, ba makaryaci ba, shugaba mai bin doka, ba mai kama-karya ba. Shugaba wanda ya fahimci cewa kasa da arzikin kasar na kowa da kowa ne ba na wani yanki kawai ba.
Ya ku ’yan Najeriya! Lallai ku sani, irin wannan shugaban ba zai taba samuwa haka nan kawai ba tare da mun tabuka komai ba. Sai dukkanmu mun a je son zuciyarmu, mun yi aiki da hankali da tunani da wayo da basirar da Allah Ya yi mana. Sai mun manta da duk wani soki-burutsu da shirme da sauransu, mu kalli cancanta da dacewa, musamman lura da halin da muke ciki.
Idan kuwa mun ki ji, mun bi soye-soyen zukatanmu, to, ba za mu ki gani ba.
Allah ba ruwanSa, Ya riga Ya ba mu dama, Ya kuma ba mu zabi, idan har muka yi amfani da damar ta hanyar da ta dace, mu ne za mu amfana, idan muka banzatar da damar, za mu ci gaba da shan wahala. Allah ba zai sauko Ya zabar mana shugabanni na kwarai ba, mu ne za mu yi don haka ya rage namu.
Ya kai dan uwa mai albarka! Ka sani, lokacin zaunawa ka rungume hannuwa ka ce kai babu ruwanka da sha’anin siyasa da shugabanci a Najeriya wallahi ya wuce, domin idan bala’o’i suna faruwa a kasa sanadiyyar rashin shugabanci nagari, ba ka isa ka ce babu ruwanka ba, domin sai ya shafe ka ko ya shafi wani naka. Sannan ka mutu ka hadu da Allah Ya tambaye ka, shin me ya sa ba ka bada gudunmawa domin tabbatar da shugabanci nagari a bayan kasa ba? Ka ga sai ka shirya irin amsar da za ka bai wa Allah Mahaliccinka. Na yi imani, ko kai Musulmi ne ko Kirista, ko marar addini, dan Kudu ne ko dan Arewa, lallai kana ji a jikinka sanadin wannan bakin mulki.
Ya ’yan uwa! Wallahi ba mu da wata hujja da za mu kare kanmu da ita a gaban Allah gobe kiyama, a kan mun cewa mutum ba ya da kwarewa ko wayewa da sanin ya kamatan da zai shugabanci kasa ko al’umma, amma mu ce dole sai mun goyi bayansa ya ci zabe, ko mu zabe shi ko mu ba shi kuri’armu don kawai kare maslahar kashin kanmu. Lallai mu sani, wallahi yin haka zai jawo mana matsala tun a nan duniya kafin mu je Lahira. Saboda haka ya zama dole mu yi karatun ta natsu, mu canja tunani mu ji tsoron Allah.
Mu ji tsoron Allah ya ku ’yan Najeriya! Muji tsoron Allah ya ku muninai! Mu nemi kusancin Mahaliccinmu ya ku bayin Allah! Da tabattuwa a kan gaskiya da yakar zalunci da azzalumai, mu tuba zuwa ga Allah baki daya, ko ma rabauta.
Ya Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka taimaki Najeriya da ’yan Najeriya, Ka kaskantar da kafirci da kafirai, Ka halakar da makiyanka makiya addininKa, wadanda ba sa son a zauna lafiya a Najeriya da duniya baki daya. Ka taimaki bayinKa salihai a duk inda suke, Ka ba mu ilimi mai amfani. Kuma Ka nuna mana gaskiya Ka ba mu ikon bin ta, Ka nuna mana karya, ka ba mu ikon guje mata.
Ya Allah ’yan uwanmu mutanen jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Ka jarabce su da fitinu da tashe-tashen hankula, Ka kawo musu saukin wanan wahala. Ya Allah Ka jikansu, Ka tausaya musu Ka sa duk wannan wahala ta zama kaffara a gare su. Ya Allah Ka albarkace su da mu baki daya da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya. Ka wadata kasarmu Ka zaunar da mu lafiya, amin.
Ina fadar wannan magana tawa ina neman gafarar Allah a gare ni da ku da dukkan Musulmi daga dukkan zunubi da kuskure, ku nemi gafararSa lallai Shi Mai gafara ne Mai jinkai.
Imam Murtada Muhammad Gusau,
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Unguwar Nagazi Okene, Jihar Kogi.
Za a iya tuntubarsa ta: 08038289761,
[email protected] ko [email protected]