Hadaya da shirin ceto1

Bari mu sani cewa tsayuwa bisa gaskiya ma tana da nata kalubale, idan ba ka yi shiri ka tsaya kan gaskiya koda mene ne zai biyo baya, sai ka yi tunani da kyau; domin mutane da yawa ba sa son gaskiya ko mai son rike amana. Mene ne laifin shi Yusufu? Ya ki ya ci […]

Hadaya da shirin ceto1
Hadaya da shirin ceto1

Bari mu sani cewa tsayuwa bisa gaskiya ma tana da nata kalubale, idan ba ka yi shiri ka tsaya kan gaskiya koda mene ne zai biyo baya, sai ka yi tunani da kyau; domin mutane da yawa ba sa son gaskiya ko mai son rike amana. Mene ne laifin shi Yusufu? Ya ki ya ci amanar maigidansa, shi ne kawai; kin aikata zunubin da ya yi, ya kawo ma shi wahala ba kadan ba, ya kai shi har ga kurkuku. Mai yiwuwa ne ka sha tsanani domin ka fadi gaskiya, idan kuwa haka ne, to kada ka damu, domin bada dadewa ba Allah zai fifita ka bisa dukan marasa adalci da ke kewaye da kai, za ka ci nasara a kansu. Mu yi kokari mu ci gaba da yin ayyukan da za su gamshi Ubangiji Allah, kada mu ji tsoron mutum; mu ji tsoron Allah. Yusufu ya sha wahala sosai, amma Allah cikin alherinSa Ya shi ya zama daya daga cikin masu mulki a kasar Masar; Allah kadai ke da ikon wannan. Hikima da basirar da Allah Ya ba shi ne ya sa ya shigo cikin fadar kasar Masar. Yaya Yusufu ya shigo cikin masarautar Masar? “Ana nan bayan shekara biyu suka cika, Fir’auna ya yi mafarki: sai ga shi, yana tsaye a bakin kogi. Sai kuma ga shanu bakwai suka fito daga cikin kogin, kyawawan ne masu kiba. Suna kuwa kiwo cikin tsatsen iwa. Sai kuma ga wadansu shanu bakwai suka fito bayansu daga cikin kogin, munana, ramammu; suka tsaya kusa da wadancan shanu a gefen kogi. Su munanan shanun nan ramammu suka cinye bakwai din shanu kyawawa masu kiba. Fir’auna fa ya farka. Ya yi barci kuma, ya sake yin mafarki: sai ga zangarniya bakwai suka hudo a kara daya, kaurara, kyawawa kuwa. Sai kuma ga zangarniya bakwai, ramammu, wadanda iskar gabas ta kekasa, suka hudo a bayansu. Su ramammun zangarniyoyin kuma suka hadiye bakwai din zangarniyoyin kaurara cikakku. Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne. Ana nan da gari ya waye ya damu a ransa; ya aike a kirawo dukkan masu sihiri na Masar da dukkan masu hikima na cikinta: Fir’auna kuwa ya fada musu mafarkansa; amma daga cikinsu an rasa mai fasararsu ga Fir’auna……………..Sa’an nan Fir’auna ya aike a kirawo Yusufu da garaje fa suka fito da shi daga kurkuku, suka kai shi: ya yi aski, ya sake tufafinsa, ya shiga wurin Fir’auna. Fir’auna kuwa ya ce wa Yusufu, na yi mafarki, ba kuwa mai fasararsa: na ji ana ambatonka, cewa , idan ka ji mafarki, ka iya fassararsa. Yusufu ya amsa wa Fir’auna, ya ce, ba a gareni yake ba: Allah za Ya amsa wa Fir’auna da jawabin salama.” (Farawa 41: 1-8; 14-16).
Yusufu ya gaya wa Fir’auna cewa shi a karan-kansa bai isa ya bada fassarar mafarkin Fir’auna ba; amma ya san Allah Mai iko duka wanda ya san dukkan komai, Shi zai ba shi fassarar. Bayan da Yusufu ya ji mafarkin Fir’auna sai “Yusufu ya ce wa Fir’auna, mafarkin Fir’auna abu daya ne, abin da Allah Yana shirin yi, shi ne Ya nuna wa Fir’auna. Kyawawan shanun guda bakwai shekara bakwai ne; zangarniyoyin nan bakwai kuma kyawawa shekara bakwai ne: mafarkin abu daya ne. su ramammun shanu kuma munana da suka fito a bayansu shekara bakwai ne da kuma zangarniya bakwai soshiya wadanda iskar gabas ta kekasa; su za su zama shekara bakwai na yunwa. Abin da na fada wa Fir’auna ke nan: Abin da Allah Yana shirin yi, Ya bayana wa Fir’auna. Ga shekara bakwai na koshi suna zuwa cikin dukkan kasar Masar: bayansu kuma shekara bakwai na yunwa za su zo; dukkan koshin nan za ta manta da shi cikin kasar Masar; yunwa za ta cinye kasar; ba kuwa za a tuna da koshi cikin kasar ba saboda yunwan nan da ke biye; gama za ta yi zafi kwarai. Saboda wannan aka maimaita mafarkin sau biyu ga Fir’auna, domin a wurin Allah matsalar ta tabbata, yanzu kuwa Allah Ya farar da ita. Sai Fir’auna ya nemi mutum mai basira mai hikima, ya sanya shi bisa kasar Masar. Bari Fir’auna ya yi wannan, ya sanya wakilai kuma bisa kasar, ya karbi humusin amfanin kasar Masar a cikin shekara bakwai din nan na koshi. Kuma su tattara dukkan abinci na wadannan shekaru nagargaru masu zuwa, su ajiye hatsi a hannun Fir’auna domin abinci cikin birane, su tsare shi kuma. Abincin za ya zama ajiya ke nan domin kasar, tanajin shekarun nan bakwai na yunwa, wadanda za su faru cikin kasar Masar; domin kada kasa ta halaka da yunwa. Abin nan fa ya yi kyau ga Fir’auna da dukkan bayinsa. Fir’auna kuwa ya ce wa bayinsa, ma iya samun mutum irin wannan, wanda ruhun Allah ke cikinsa? Fir’auna ya ce wa Yusufu, tun da Allah Ya nuna maka wannan duka, babu wani mai basira mai hikima kamarka: kai ne za ka kasance a bisa gidana, bisa ga faddnka kuma za a mallaki dukkan mutanena: a wajen kursiyi kadai zan fi ka girma. Fir’auna ya ce wa Yusufu, ga shi, na sanya ka bisa dukkan kasar Masar. Fir’auna ya kwance zobe mai hatimi daga hannunsa, ya sa wa hannun Yusufu, ya kuma yafa masa tufa na linen mai kyau, ya rataya sarka ta zinariya a wuyansa. Ya hawar da shi bisa karusa ta bimakin-nasa, suka rika kirari a gabansa, ku durkusa: ya sa shi kuma a bisa dukkan kasar Masar. Fir’auna kuma ya ce wa Yusufu, ni ne Fir’auna, kuma ba wanda za ya tada hannunsa ko kafarsa cikin dukkan kasar Masar sai da yardarka.”
Wannan wani irin daukaka ne Allah Ya yi wa Yusufu? ’Yan uwansa sun ki shi, suka jefa shi cikin rijiyar da ta bushe, suka ciro shi suka sayar da shi, ya zama bawa a gidan Potiphar, matar maigidansa ta nemi ta sa shi cikin zunubi ya ki; dalilin da ya sa aka sa shi kurkuku, daga cikin kurkuku Allah cikin ikonSa Ya ciro Yusufu zuwa cikin fadar Sarki Fir’auna: Allah kadai ke iya yin wannan. Rayuwar Yusufu ta zama da albarka sosai ba ga kasar Masar kadai ba, amma ga sauran duniya gaba daya; domin da aka soma yunwar, ta shafi ko’ina, kuma kasar Masar ce kawai ta yi tanadin abinci domin shawarar da Yusufu ya ba Fir’auna. Idan ba domin shawarar da ya bayar ba; da har su Misirawan ma za su fuskanci yunwa kwarai.