Hadaya da shirin ceto2

Mun gani cewa zamanin da Annabi Nuhu ya yi rayuwarsa, bai bambanta da wannan zamanin ba ko kadan kafin Ubangiji Allah Ya halaka dukan duniya da ruwan Tufana. Kafin lokacin ya zo, Nuhu ya yi ta wa’azi ga mutanen zamaninsa su tuba su bar aikata miyagun ayyukansu, sun ki su ji har sai da fushin […]

Hadaya da shirin ceto2
Hadaya da shirin ceto2

Mun gani cewa zamanin da Annabi Nuhu ya yi rayuwarsa, bai bambanta da wannan zamanin ba ko kadan kafin Ubangiji Allah Ya halaka dukan duniya da ruwan Tufana. Kafin lokacin ya zo, Nuhu ya yi ta wa’azi ga mutanen zamaninsa su tuba su bar aikata miyagun ayyukansu, sun ki su ji har sai da fushin Allah ya sauko bisansu; mutum bai canja ba daga irin wannan halin har wannan zamani. A kullum Pastoci da masu bishararmu suna ta yin wa’azi a iklisiyoyinmu a cikin birane da kauyuka; suna gaya wa mutane tafarkin Allah, amma mutane da dama; koda yake sun ji bisharar Yesu Almasihu sun ki su bin umarnin Allah Mai iko duka. Maganar Allah tana koya mana cewa: “Kuma kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka nan kuma bayyanuwar dan mutum za ta zama. Gama kamar yadda suna ci, suna sha, suna aure, suna aurarwa a cikin kwanakin da ke gaban ruwan Rigyawa, har ranar da Nuhu ya shiga cikin jirgi, ba su sani ba har Rigyawa ta zo ta kwashe su duka; haka nan kuma bayyanuwar dan mutum za ta zama.” (Matta 24 : 37 – 39).
Muna fuskantar shari’ar Allah a wannan zamani. Gaskiya ce wannan duniya ta yi kusan karewa kuma Allah bai bar mu cikin duhu ba, Ya rigaya Ya nuna mana a fili alamun karshen zamanin nan. A inda muka yi karatu a cikin Littafin Matta, mun gani cewa a wannan zamanin abin da ke faruwa ke nan, mutane suna aure suna aurarwa; suna ci suna sha, sun manta da maganar Allah. A kullum ana kan yin wa’azi amma ya zama kamar zuba ruwa ne a bayan kwarya. Mutane sun ki su bari maganar Allah ta samu mazauni a cikin zuciyarsu, sun ki shirin alherin Allah domin ceton dukan ’yan Adam; abin tausayi shi ne, shirin da Allah Yake da shi ga dukan wadanda sukakki wannan shiri naSa na ceto, ba ruwa ne zai halakar da su ba, wuta ce Allah zai yi amfani da ita. dan uwana kada ka yarda ka zama abin kaito, yanzu ne lokacin gyara tsakaninka da Allah, domin ba mu san yaushe ne wannan zai faru ba, abin tunani shi ne zai iya faruwa ko a yanzu ma. Kada ka yarda ka yi wasa da maganar Allah.
Da Annabi Nuhu ya shiga jirgi da shi da iyalinsa, Allah ne da kanSa Ya rufe kofar jirgin, babu wani wanda ya isa ya bude kofar jirgi. A lokacin ne mutane suka gane cewa Allah bada wasa Yake yi ba, abin tausayi shi ne lokacinsu ya kure, sun yi latti. Haka a yau, mutane da dama  suna gani kamar suna da sauran lokaci amma gaskiyar ita ce lokaci ya kure.
Bari mu sake dawowa kan maganar da muke yi wadda ita ce Hadaya da Shirin Ceto, bayan da Allah Ya halaka duniya da ruwa, mutane duka suka mutu, da ruwan ya shanye, sai Ubangiji Allah Ya tuna da bawansa Annabi Nuhu: “Kuma Allah Ya tuna da Nuhu da kowane mai rai da dukan bisashen da ke tare da shi cikin jirgi: Allah kuma Ya ratsar da iska ta hura a bisa kasa, ruwa kuwa ya janye; ………Ana nan cikin shekara ta dari shida da daya, cikin wata na fari, daya ga wata, sai ruwa ya kafe a bisa kasa: Nuhu kuma ya kware marufin jirgi, ya duba ga fuskar kasa ta tsame. Cikin wata na biyu, bisa rana ta ashirin da bakwai ga wata kasa duk ta shanye. Allah Ya yi magana da Nuhu, Ya ce, ka fita daga cikin jirgin da kai da matarka da ’ya’yanka tare da kai. Kuma sai ka fito da kowane mai rai wanda ke tare da kai daga dukan dabbobi, su tsuntsaye zuwa bisashe zuwa kowane mai rarrafe wanda ke rarrafe a kasa; domin su hayayyafa a duniya, su yi yalwa, su dadu a duniya. Nuhu kuwa ya fita da ’ya’yansa da mata tasa da matan ’ya’yansa tare da shi: kuma kowane dabba da kowane mai rarrafe da kowane tsuntsu, iyakar abin da ke motsi a kasa, bisa ga dangunansa suka fita daga cikin jirgin. Nuhu kuma ya gina bagadi ga Ubangiji; ya diba kuma daga cikin kowane irin tsattsabtacciyar dabba da kowane irin tsattsatataccen tsuntsu, ya mika baiko na konawa a bisa bagadi. Ubangiji kuma Ya ji kanshi mai dadi; Ubangiji kuwa Ya ce cikin zuciyarSa, ba Ni kara la’anta kasa saboda mutum; gama tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga kuruciyarsa; ba kuwa za Ni sake bugun duniya mai rai dadai, yadda na rigaya Na yi.” (Farawa 8 : 1, 13-21).  Akwai abin lura guda a inda muka yi karatu yanzu, lokacin da Nuhu ya fito daga cikin jirgin sai ya mika wa Allah Hadaya ta konawa. Ubangiji Allah kuma Ya ji dadin wannan hadaya da Nuhu ya yi, Allah Ya ji kanshin wannan hadaya sai Ya yi alkawari cewa, ba zai sake hukunta wannan duniya haka nan ba kuma. Allah Ya lura cewa tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga kuruciyassa, hadayar da Nuhu ya mika ga Allah ta faranta maSa zuciyarSa. Abin koyi shi ne Hadaya takan faranta wa Ubangiji Allah zuciyarSa, duk wanda yake so ya faranta wa Allah zuciya a wancan lokaci, dole ne ya san yadda zai mika hadaya ga Ubangiji Allah. Bari mu duba sanannen bawan Allahn nan mai suna IBRAHIM.
ANNABI IBRAHIM:  Wannan bawan Allah, mutum ne wanda yake jin tsoron Allah sosai, mutum ne mai biyayya ga umarnin Ubangiji Allah, duk abin da Allah Ya ce masa ya yi, ba ya yin taurin kai, shi mai biyayya ne muddin ya san cewa umarnin Allah ne. Tun daga lokacin da Ubangiji Allah Ya kiraye shi ya zama mutum wanda zai shiga alkawari da shi, yana kasa kunnensa ya ji muryar Ubangiji Allah. “Ana nan sai Ubangiji Ya ce wa Abram, ka fita daga kasarka, daga danginka kuma da gidan ubanka, zuwa kasa da zan nuna maka: daga wurinka zan yi al’umma mai girma, zan albarkace ka kuma, in sa ka yi suna; ka zama albarka: wadanda sun albarkace ka zan albarkace su, in la’antar da wanda ya la’antar da kai: a cikinka kuma dukan duniya za su yi albarka. Abram fa ya tafi kamar yadda Ubangiji Ya fada masa; Lot kuma ya tafi tare da shi: Abram yana da shekara saba’in da biyar sa’adda ya fita Haran.” (Farawa 12 : 1– 4).
Ibrahim mutum ne wanda ya ke yin biyayya nan take; ba ya bata lokaci ko kadan. Idan Allah Ya bar mu a cikin masu rai, za mu ci gaba da wannan binciken mako mai zuwa. Kada mu manta da gode wa Allah domin taimakonSa zuwa gare mu a wannan kasa. Mun gani cewa zamanin da Annabi Nuhu ya yi rayuwarsa, bai bambanta da wannan zamanin ba ko kadan kafin Ubangiji Allah Ya halaka dukan duniya da ruwan Tufana. Kafin lokacin ya zo, Nuhu ya yi ta wa’azi ga mutanen zamaninsa su tuba su bar aikata miyagun ayyukansu, sun ki su ji har sai da fushin Allah ya sauko bisansu; mutum bai canja ba daga irin wannan halin har wannan zamani. A kullum Pastoci da masu bishararmu suna ta yin wa’azi a iklisiyoyinmu a cikin birane da kauyuka; suna gaya wa mutane tafarkin Allah, amma mutane da dama; koda yake sun ji bisharar Yesu Almasihu sun ki su bin umarnin Allah Mai iko duka. Maganar Allah tana koya mana cewa: “Kuma kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka nan kuma bayyanuwar dan mutum za ta zama. Gama kamar yadda suna ci, suna sha, suna aure, suna aurarwa a cikin kwanakin da ke gaban ruwan Rigyawa, har ranar da Nuhu ya shiga cikin jirgi, ba su sani ba har Rigyawa ta zo ta kwashe su duka; haka nan kuma bayyanuwar dan mutum za ta zama.” (Matta 24 : 37 – 39).
Muna fuskantar shari’ar Allah a wannan zamani. Gaskiya ce wannan duniya ta yi kusan karewa kuma Allah bai bar mu cikin duhu ba, Ya rigaya Ya nuna mana a fili alamun karshen zamanin nan. A inda muka yi karatu a cikin Littafin Matta, mun gani cewa a wannan zamanin abin da ke faruwa ke nan, mutane suna aure suna aurarwa; suna ci suna sha, sun manta da maganar Allah. A kullum ana kan yin wa’azi amma ya zama kamar zuba ruwa ne a bayan kwarya. Mutane sun ki su bari maganar Allah ta samu mazauni a cikin zuciyarsu, sun ki shirin alherin Allah domin ceton dukan ’yan Adam; abin tausayi shi ne, shirin da Allah Yake da shi ga dukan wadanda sukakki wannan shiri naSa na ceto, ba ruwa ne zai halakar da su ba, wuta ce Allah zai yi amfani da ita. dan uwana kada ka yarda ka zama abin kaito, yanzu ne lokacin gyara tsakaninka da Allah, domin ba mu san yaushe ne wannan zai faru ba, abin tunani shi ne zai iya faruwa ko a yanzu ma. Kada ka yarda ka yi wasa da maganar Allah.
Da Annabi Nuhu ya shiga jirgi da shi da iyalinsa, Allah ne da kanSa Ya rufe kofar jirgin, babu wani wanda ya isa ya bude kofar jirgi. A lokacin ne mutane suka gane cewa Allah bada wasa Yake yi ba, abin tausayi shi ne lokacinsu ya kure, sun yi latti. Haka a yau, mutane da dama  suna gani kamar suna da sauran lokaci amma gaskiyar ita ce lokaci ya kure.
Bari mu sake dawowa kan maganar da muke yi wadda ita ce Hadaya da Shirin Ceto, bayan da Allah Ya halaka duniya da ruwa, mutane duka suka mutu, da ruwan ya shanye, sai Ubangiji Allah Ya tuna da bawansa Annabi Nuhu: “Kuma Allah Ya tuna da Nuhu da kowane mai rai da dukan bisashen da ke tare da shi cikin jirgi: Allah kuma Ya ratsar da iska ta hura a bisa kasa, ruwa kuwa ya janye; ………Ana nan cikin shekara ta dari shida da daya, cikin wata na fari, daya ga wata, sai ruwa ya kafe a bisa kasa: Nuhu kuma ya kware marufin jirgi, ya duba ga fuskar kasa ta tsame. Cikin wata na biyu, bisa rana ta ashirin da bakwai ga wata kasa duk ta shanye. Allah Ya yi magana da Nuhu, Ya ce, ka fita daga cikin jirgin da kai da matarka da ’ya’yanka tare da kai. Kuma sai ka fito da kowane mai rai wanda ke tare da kai daga dukan dabbobi, su tsuntsaye zuwa bisashe zuwa kowane mai rarrafe wanda ke rarrafe a kasa; domin su hayayyafa a duniya, su yi yalwa, su dadu a duniya. Nuhu kuwa ya fita da ’ya’yansa da mata tasa da matan ’ya’yansa tare da shi: kuma kowane dabba da kowane mai rarrafe da kowane tsuntsu, iyakar abin da ke motsi a kasa, bisa ga dangunansa suka fita daga cikin jirgin. Nuhu kuma ya gina bagadi ga Ubangiji; ya diba kuma daga cikin kowane irin tsattsabtacciyar dabba da kowane irin tsattsatataccen tsuntsu, ya mika baiko na konawa a bisa bagadi. Ubangiji kuma Ya ji kanshi mai dadi; Ubangiji kuwa Ya ce cikin zuciyarSa, ba Ni kara la’anta kasa saboda mutum; gama tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga kuruciyarsa; ba kuwa za Ni sake bugun duniya mai rai dadai, yadda na rigaya Na yi.” (Farawa 8 : 1, 13-21).  Akwai abin lura guda a inda muka yi karatu yanzu, lokacin da Nuhu ya fito daga cikin jirgin sai ya mika wa Allah Hadaya ta konawa. Ubangiji Allah kuma Ya ji dadin wannan hadaya da Nuhu ya yi, Allah Ya ji kanshin wannan hadaya sai Ya yi alkawari cewa, ba zai sake hukunta wannan duniya haka nan ba kuma. Allah Ya lura cewa tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga kuruciyassa, hadayar da Nuhu ya mika ga Allah ta faranta maSa zuciyarSa. Abin koyi shi ne Hadaya takan faranta wa Ubangiji Allah zuciyarSa, duk wanda yake so ya faranta wa Allah zuciya a wancan lokaci, dole ne ya san yadda zai mika hadaya ga Ubangiji Allah. Bari mu duba sanannen bawan Allahn nan mai suna IBRAHIM.
ANNABI IBRAHIM:  Wannan bawan Allah, mutum ne wanda yake jin tsoron Allah sosai, mutum ne mai biyayya ga umarnin Ubangiji Allah, duk abin da Allah Ya ce masa ya yi, ba ya yin taurin kai, shi mai biyayya ne muddin ya san cewa umarnin Allah ne. Tun daga lokacin da Ubangiji Allah Ya kiraye shi ya zama mutum wanda zai shiga alkawari da shi, yana kasa kunnensa ya ji muryar Ubangiji Allah. “Ana nan sai Ubangiji Ya ce wa Abram, ka fita daga kasarka, daga danginka kuma da gidan ubanka, zuwa kasa da zan nuna maka: daga wurinka zan yi al’umma mai girma, zan albarkace ka kuma, in sa ka yi suna; ka zama albarka: wadanda sun albarkace ka zan albarkace su, in la’antar da wanda ya la’antar da kai: a cikinka kuma dukan duniya za su yi albarka. Abram fa ya tafi kamar yadda Ubangiji Ya fada masa; Lot kuma ya tafi tare da shi: Abram yana da shekara saba’in da biyar sa’adda ya fita Haran.” (Farawa 12 : 1– 4).
Ibrahim mutum ne wanda ya ke yin biyayya nan take; ba ya bata lokaci ko kadan. Idan Allah Ya bar mu a cikin masu rai, za mu ci gaba da wannan binciken mako mai zuwa. Kada mu manta da gode wa Allah domin taimakonSa zuwa gare mu a wannan kasa.