Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu

Tanka ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya.

Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu

Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu.

Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar.

Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da gidan Galadiman Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhininsa kan rasuwar Galadanci, tare da bayyana irin rawar da ya taka a gwamnatinsa.

“Rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci babban rashi ne ga gwamnatina da Jihar Kano baki ɗaya.

“Za a yi rashinsa saboda jajircewarsa da ƙwazon da ya nuna wajen inganta harkokin sadarwarmu,” in ji gwamnan.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, ’yan uwa da abokan arziƙi.