Hadimin Gwamnan Kano ya sauya sheƙa zuwa APC

Hadimin ya bayyana cewar ya koma gidansa na asali a siyasar Kano.

Hadimin Gwamnan Kano ya sauya sheƙa zuwa APC

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karɓi hadimin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar NNPP.

Dambo, wanda ya taɓa riƙe shugabancin Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano sau biyu, ya sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa APC, yayin ziyarar da ya kai wa Sanata Barau a gidansa da ke Abuja a ranar Litinin.

A ranar 13 ga watan Agusta, an naɗa Dambo a matsayin mai bai wa Gwamnan Kano Shawara na Musamman kan Zuba Jari, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sa hannu kansa a takardar naɗin nasa.

Yayin sanar da ficewarsa daga NNPP, Dambo ya yi alƙawarin yin aiki tare da jam’iyyar APC a Kano da kuma matakin ƙasa baki ɗaya.

“Na gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da ya shiryar da ni, ya kuma ba ni ikon dawowa gida. Na kasance a cikin wannan gida kafin na koma NNPP, amma yanzu na dawo APC.

“Za mu ci gaba da tallafa wa wannan tafiya tare da ƙoƙarinmu na kasancewa masu biyayya ga APC a Kano da kuma matakin ƙasa baki ɗaya.

“Zan yi amfani da dukkanin basirata da ƙwarewata wajen tallafa wa nasarar APC. Ina fatan Sanata Barau zai samu nasara. Kazalika, ina miƙa gaisuwata ga Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje. Allah ya ci gaba da masa jagoranci,” in ji Dambo.

Har wa yau, ɗaya daga cikin manyan jagororin NNPP a ƙaramar hukumar Kabo a Jihar Kano, Alhaji Rabiu Alhassan Durum, ya koma jam’iyyar APC.

Yayin da yake maraba da ’yan siyasar biyu zuwa jam’iyyar APC, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yaba musu bisa wannan hukunci da suka yanke.

Sanata Barau, wanda kuma shi ne Mataimakin Kakakin ƙungiyar ECOWAS, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC ke jagoranta na magance ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.

“Waɗannan mutanen ƙwarai sun nuna ƙwazo da jajircewa wajen ci gaban jiharmu da ƙasarmu. Wannan jajircewar tasu tana tafiya kafaɗa da kafaɗa da manufofin jam’iyyar APC na kawo sauyi ga ƙasar nan.

“Za mu yi aiki tare da su da duk waɗanda ke da niyyar ciyar da ƙasarmu gaba da manufar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ‘Renewed Hope Agenda’. Mu haɗa kai don magance ƙalubalen da ke fuskantarmu a matsayin al’umma,” in ji shi.

NAFDAC ta gano wani jabun maganin malaria da ke yawo a Najeriya

Kotu za ta karɓi shaidar wakilin Aminiya a shari’ar garkuwa da mutane

An daƙile harin ’yan ta’adda a Borno

An bai wa tsofaffin ’yan bindiga 6 shaidar tuba a Yobe