Hadin goge fata
Kowace mace ta cancanci kula da fatarta da kuma fuskarta. Domin mace aka fi sani da kwalliya da ado.Kasancewar irin aikace-aikacen gida, kamar su shara da wanke-wanke da sauransu hakan na sanya fata dauda idan ba a kula wajen magance ta ba tana haifar da fesowar kuraje, kunar rana, gishirin fuska da maikon fuska. Domin […]
Kowace mace ta cancanci kula da fatarta da kuma fuskarta. Domin mace aka fi sani da kwalliya da ado.Kasancewar irin aikace-aikacen gida, kamar su shara da wanke-wanke da sauransu hakan na sanya fata dauda idan ba a kula wajen magance ta ba tana haifar da fesowar kuraje, kunar rana, gishirin fuska da maikon fuska.
Domin gyaran fata da jiki, dole ne a zabi daya daga cikin wadannan ababen da zan lissafo a goge fata a duk lokacin da aka yi wasu aikace-aikace a gida bayan an yi wanka. A sha karatu lafiya.
- Idan ana da hali za a iya yin wanka da ruwan madara; domin madara na dauke da sinadaran sanya laushin fata da sanya ta sulbi.
- Zuma; yawan amfani da zuma na rage gautsin fata kuma ya sanya ta laushi a kullum.
- Ruwan kwai; yana hana fuskar zama a bushe kuma yana hana fitar gishirin fuska a fuska
- Lemun tsami; yana hana kuraje fitowa kuma yana kara hasken fata.
Hadi
Cokali daya na zuma
Cokali daya na madara
Rabin cokalin ruwan kwai
Ruwan lemun tsami kadan
Ki samu kwalba a hada ruwan madara da zuma sannan a dora a kan wuta na tsawon minti goma domin su hadu. Bayan haka, sai a zuba ruwan kwai da ruwan lemun tsami a cikin hadin sai a gauraya su sosai.
A samu auduga a rika shafawa da ita a fuska musamman gefen hanci. Bayan haka, sai a jira na tsawon minti ashirin da biyar kafin a wanke.
A wanke fuska da ruwan dumi sannan a goge ta da tawul mai kyau.
Idan har a ka kasance masu yin irin wannan hadin, insha Allahu, za a rabu da kurajen fuska.