Hadin kai ne babbar nasarar da muka samu – kungiyar MFE

kungiyar dalibai Masu Nazarin Fannin Tsimi da Tanadi ta kasa, reshen Jami’ar Abuja, wacce a takaice ake kira (MFE), ta ce, babban  nasarar da ta cimma ita ce ta hadin kai a tsakanin ’ya’yanta.Shugaban kungiyar, Chukwueme Kennedy, shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja a karshen makon jiya.Ya ce […]

Hadin kai ne babbar nasarar da muka samu – kungiyar MFE
Hadin kai ne babbar nasarar da muka samu – kungiyar MFE

kungiyar dalibai Masu Nazarin Fannin Tsimi da Tanadi ta kasa, reshen Jami’ar Abuja, wacce a takaice ake kira (MFE), ta ce, babban  nasarar da ta cimma ita ce ta hadin kai a tsakanin ’ya’yanta.
Shugaban kungiyar, Chukwueme Kennedy, shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja a karshen makon jiya.
Ya ce duk da kalubalen da kungiyar ta fuskanta, kungiyar ta cimma nasarori masu yawan gaske.
“Babu shakka mun cimma nasarori masu yawan gaske wadanda suka hada da hadin kan ’yan kungiyarmu ta fuskar ilimi da wayar da kansu kan fannin tsimi da tanadi musamman kan abin da ya shafi tattalin arzinkin kasar mu Najeriya da sauran kasashen duniya,” inji shi.
Ya kara da cewa kungiyar ta yi fice a kasa baki daya saboda tsarin shugabanci da take da shi tun daga sama har kasa.
“Idan ka kwatanta mu da sauran takwarorinmu da ke jami’ar Abuja da sauran kungiyoyi da ke kasa baki daya za ka ga mun fi kowace kungiya tsari da iya tafiyar da shugabanci,” inji shi.
Ya dage a kan cewa hakan shi ke kara janyo wa kungiyar farin jini da samun karin masoya a jami’ar Abuja da kasa baki daya.
Ya bayyana cewa abin da yake so ya cimma a matsayinsa na shugaban kungiyar shi ne a samu dorewar kungiyar ko da bayan sun kammala karatunsu a jami’ar.
“Babban burinmu shi ne mu ga cewa kungiyarmu ta tsaya da kafafunta ta yadda za ta ci gaba da dorewa ko da bayan mun kammala karatunmu ya zamana ’ya’yanmu da jikokinmu za su amfana da ita,” inji shi.
Ya yi kira ga sauran mambobin kungiyar su ci gaba da bayar da goyon bayansu ga shugabannin kungiyar don samun bunkasa da dorewar kungiyar a jami’ar baki daya.