Hadin kai ne mafita ga ’yan Arewa a Legas -Garba Chede
Wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Legas, Alhaji Garba Chede ya ce hadin kai ne kawai zai sa ’yan Arewa su cimma burinsu na siyasa a jihar.Alhaji Garba Chede, wanda yana daya daga cikin shugabannin ’yan Arewa a jam’iyyar APC a jihar, ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya.Ya ce, “Ya […]

Wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Legas, Alhaji Garba Chede ya ce hadin kai ne kawai zai sa ’yan Arewa su cimma burinsu na siyasa a jihar.
Alhaji Garba Chede, wanda yana daya daga cikin shugabannin ’yan Arewa a jam’iyyar APC a jihar, ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya.
Ya ce, “Ya kamata duk ’yan Arewa su zo mu hada kai mu tafi tare. Mu yi watsi da duk wani korafi, wanda yake jam’iyyar CPC da ACN da ma kowace jam’iyyar yake yi, yanzu an riga an zama daya, an hade an zama APC. Saboda haka idan mu ’yan Arewa muna so mu cimma burinmu na siyasa a Jihar Legas wajen samun manyan mukamai a jihar, ya zamanto ana damawa da mu sosai, to sai mun hada kai. Mu ajiye duk wani bambanci mu zama tsintsiya madaurinki daya. Babu shakka idan muka yi haka, za mu iya tunkarar duk wani kalubale da yake ci wa ’yan Arewa, mazauna Jihar Legas, tuwo a kwarya”.
Ya ci gaba da cewa, “Musamman ’yan Arewa ’yan uwanmu da ke cikin jam’iyyar CPC, ina kira a gare su da cewa yanzu mun zama daya a cikin jam’iyyar APC, ya kamata su zo mu hada kai mu rika yin taro muna tattauna abubuwan da suke damun mu, ta haka za mu fahimci juna mu ci nasara. Haka nan wadanda suke kasuwanci da sauran sana’o’i da kungiyoyi masu zaman kansu su zo mu tafi tare baki daya. Saboda sai da hadin kai ake samun ci gaba”.
Ya bayyana cewa duk da shugabannin da suka kafa kungiyar Kwankwasiyya ba su sanar da shi kafa kungiyar ba, ya yi fatan alheri ga kungiyar. “Ai Kwankwaso namu ne muna alfahari da shi. Saboda haka muna yi musu fatar alheri, bunkasar kungiyar zai taimaka wa jam’iyyarmu ta APC”. Inji shi.
Ya dage a kan cewa daga yanzu ’yan Arewa ba za su sake yarda kansu ya rabu ba a Jihar Legas, har ma ya bayyana cewa ’yan Arewa sun kai matsayin ma a ba su mataimakin gwamna da kwamishinoni da kuma sauran mukamai a jihar.
Dangane da furucin da Gwamna Fashola ya yi kan irin mutumin da zai gaje shi, sai ya ce suna goyon bayan furucin, wanda yake na mara wa duk wanda yake son ci gaban jihar. “Muna goyon bayan furucin gwamna na cewa sai wanda yake son ci gaban Legas zai gaje shi, ba wanda zai kawo bambacin addini ko kabilanci ba a jihar”. Inji shi.