‘Hadin kai shi ne babban makaminmu’
kungiyar wayar da kan ’yan Arewa mazauna jihohin Kudu maso Yamma ta kafu ne saboda gano cewa rashin hadin kai tsakaninsu yana musu babbar illa. An dade ana tafiya yaki da su, amma daga bisani sai a bar su da kuturin bawa, don haka yanzu sun gane, an sha su sun warke, kuma sun yi […]

kungiyar wayar da kan ’yan Arewa mazauna jihohin Kudu maso Yamma ta kafu ne saboda gano cewa rashin hadin kai tsakaninsu yana musu babbar illa. An dade ana tafiya yaki da su, amma daga bisani sai a bar su da kuturin bawa, don haka yanzu sun gane, an sha su sun warke, kuma sun yi alwashin ba za su bi kowa ba, sai sun tantance mazan kwarai sannan su mara musu baya.
Wasu daga cikin matsalolin da suke fuskanta, su ne korarsu da ake yi daga wuraren da suka raya da kuma rashin samar wa ’ya’yansu guraben ilmi daidai da na ’ya’yan da ke yankin, alhali baya ga masu masaukin nasu, ba wata al’umma da ta yi yawansu, amma kuma su ne ake warewa a duk lokacin da abin amfanar baki ya zo. Kodayake daga cikin manya-manyan abubuwan da suke alfahari da shi shi ne suna zauna lafiya tsakaninsu da masu masaukin nasu.
Shugaban kungiyar, Grema Mohammed Harun ya ce daga lokacin da suka samar da kungiyar har zuwa lokacin zabe za su tabbatar duk inda ’yan Arewa suke sun neme su sun gana da su kuma sun nuna musu muhimmancin hadin kai duk da yake siyasa ’yar ra’ayi ce kuma kowa na da damar zaben wanda yake so, amma idan ya tashi zabe, akwai bukatar ya zabi nagari, wanda ke da alama yana da zuciyar son taimakon jama’a.
Shi ma sakataren kungiya, Abdulkarim Murtala Zariya cewa ya yi kuskuren da suka yi a da, ba za su sake yarda su tafka irinsa ba, domin shugabanninsu, musamman sarakunan Hausawa su ne suka yi biris suna kallo da yawan jama’ar Arewa na shan wahalar da suke sha. Samar da kungiyar zai taimaka wajen kawo sauki, domin daga yanzu ba tilas ba ne su bi ra’ayin sarakunan Hausawa a duk inda suke a cikin jihohin Kudu maso Yamma.
Shi ma Malam Umar Mohammed Azunge da ya wakilci mutanen Badun, cewa ya yi wannan yunkurin yekuwar da suka dauri aniya, ba za su gaza ba domin sa kai ya fi bauta ciwo, za su jajirce har sai sun ga hakarsu ta cimma ruwa. “Shi ya sa muke jaddada cewa wannan kungiyar ba ta da nasaba da addini ko kabilanci ko kuma siyasa, manufarta ita ce duk inda dan Arewa yake a Kudu maso Yamma, to ya tabbatar ya zabi nagari, wanda zai kare shi, idan bukatar hakan ta taso”. Inji shi.