Hadin kai tsakanin Ali Nuhu da Adam Zango zai dinke barakar Kannywood —Maishadda
Idan ana so a samu zaman lafiya mai dorewa, dole kowa ya tsaya a matsayinsa
Fitaccen furodusa a masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda ya ce burinsa shi ne ya ga masana’antar ta dinke ta zama tsinstiya madaurinki daya.
Maishadda ya bayyana hakan ne a zantawarsa da Aminiya, inda ya ce, “fatarmu ke nan in sha Allahu, muna fata a daina wadannan rigingimun domin ba su da wani amfani. Kuma suna jawo tawayar arziki a masana’antar.”
Da aka tambaye shi wane kokari yake yi wajen kawo karshen rigingimun, sai ya ce, “kasancewar kusan duk akwai ganin girma a duk wajen mutumin da na taba aiki ko kuma nake mu’amala da shi.
“To yawanci duk mutumin da na ba shawara ko kuma na yi masa nuni, yana kokarin dauka. Akwai wannan fahimtar.”
A batun ko sulhu da hadin kai tsakanin Ali Nuhu zai iya taimakawa wajen dinke barakar masana’antar, sai ya ce, “sulhun tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango zai matukar dinke matsalar Kannywood kwarai da gaske.”
Maishadda ya kara da cewa idan ana so a samu zaman lafiya mai dorewa, dole kowa ya tsaya a matsayinsa.
Furodusa ya tsaya a matsayinsa na furodusa, darakta ma ya tsaya a matsayinsa na darakta, sannan a daina katsalandan.