Hadin kai ya faskara a Arewa
Hadin kan ‘yan Arewa ya zame mawuyacin al’amari, kuma hakan ne ke haddasa yawancin matsalolin da yankin ke fama da su, wadanda kuma ke kokarin kai shi kasa a halin yanzu. To amma Arewar ba ta shiga wannan halin ba sai a ‘yan shekarun baya, sa’ilin da manyan kasashen duniya suka bullo da sabon tsarin […]
Hadin kan ‘yan Arewa ya zame mawuyacin al’amari, kuma hakan ne ke haddasa yawancin matsalolin da yankin ke fama da su, wadanda kuma ke kokarin kai shi kasa a halin yanzu. To amma Arewar ba ta shiga wannan halin ba sai a ‘yan shekarun baya, sa’ilin da manyan kasashen duniya suka bullo da sabon tsarin mallake kasashen duniya masu tasowa wadanda za su bi su tattatse don habaka tattalin arzikinsu. Dabara, ko kuma yaudarar da suka bullo da ita ce ta tursasa wa kasashen bin tafarkin dimokuradiyya bayan sun daga rakiyar mulkin soja da suke sanya ‘yan korensu na hambarar da gwamnatocin da ba su goyon bayan Yahudu da Nasara. Ta haka ne suke daure wa wasu gafalallu da jabun ‘yan siyasa gindin yin takarar shugabancin kasa, domin idan sun kai ga mulki su daga masu kafa don su yi watanda da arzikin kasar.
To, amma sun fahimci cewa wannan manufa ta bin tafarkin karkacciyar dimokuradiyya don biyan munanan bukatunsu ba za ta kai su gaci ba, sai idan sun bullo da wata sabuwar kutungwilar da za ta rarraba kawunan jama’a. Wannan kutungwilar kuwa ita ce ta yin amfani da addini don shiga tsakanin jama’a, ta yadda hakan zai dinga haddasa rigingimu da fitintinu daban-daban a tsakanin jam’iyyun siyasa, domin bai wa ‘yan takara goyon baya, ba bisa akidarsu ba sai dai don addininsu. Wannan ne halin da kasar ke ciki a halin yanzu, abin da kuma ya hana yankin Arewa zaman lafiya ke nan, al’ummomin cikinta kuma na zaman doya da manja, suna yi wa junansu kallo hadarin kaji.
Ta haka ne siyasar bambancin addini ta samu gindin zama a Najeriya, sa’annan kuma kabilanci da tsabar son kai da biye wa zuciya suka kankama a ko ina, kuma illolinsu sai a lokutan zabubbuka suke bayyanuwa, an kuma kasa maganinsu, domin kuwa su ne matakan da wasu ke bi don kai wa ga haramtacciyar nasarar zabe. Wannan ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da yadda Yahudu da Nasara suka mayar da bambancin addini da kuma akida makamar yakar al’ummomin kasashen Musulmin duniya, suna farraka tsakanin mabiya addinin Islama, suna kuma goyon bayan bangaren da zai fi biya musu bukata a kasashe daban-daban. Idan a waccan kasar suna goyon bayan mabiya Sunni ne, suna dakile mabiya Shi’a, sai ka taras suna dasawa da ‘yan Shi’an a wata kasa, suna kuma takura wa ‘yan Sunni. Su babu abin da ya dame su da wani bangare na Musulunci, burinsu shi ne su tauye Musuluncin, su kuma shiga tsakanin Musulmi, su raunana su, don kada su hada kai, su yi karfin da za su buwaye su.
Shi ya sa a kasar Iran su ke artabu da ‘yan Shi’a, kuma a kasar Saudiya suna goyon bayan Sunni ( Wahabiyawa), a makwabciyar kasar Iraki kuma ba su kaunar ‘yan Sunnin kasar, hada baki ma suke da kasar Saudiya don a ruguza su. To, idan har da gaske Yahudu da Nasaran na so mulin dimkuradiyya ya gauraye kasashen duniya, har suna amfani da karfin soji kan kasashen da suka ki bin wannan tafarkin, me ya hana su tursasa kasar Saudiya koma wa dimokuradiyya, su kuma dage lallai sai ta kakkafa jam’iyyun siyasa, ta rubuta sabon kundin tsarin mulki, maimakon Alkur’ani Mai girma da Mahaliccinsu ya ba su, suke kuma aiki da shi don dacewarsa? Ba wannan ne ya damu Yahudu da Nasara ba, su idan har za su samu sukunin tatsar arzikin Saudiyya kamarn yadda mahukuntar kasar suka mika musu wuya, ba abin da zai dame su da yadda ake gudanar da harkokin addini da na mulkin kasar.
To a nan Najeriya kutungwilar Yahudu da Nasara ta yi tasiri saboda bambancin addini ya yi katututu a zukatan jama’a, har ta kai ga Musulmi da Kiritocin yankin sun yi hannun riga da juna, kuma ko a siyasance ba a hada kai don a gudu tare, a kuma tsira tare. Ga dai misali nan an gani kuru-kuru a shekarar 2011 sa’ilin da sakamakon zabe ya nuna yadda Kiristocin Arewa suka hada kai da Kiristocin Kudu aka kafa gwamnatin da ta komo tana muzguna wa daukacin al’ummomin Musulmi da Kiristan Arewa. Amma abin mamaki gami da haka shi ne yadda Kiristocin Arewa suka kasa gane illar haka, balle su gane cewa ‘yan kudu ba kaunarsu suke ba, duk kuwa da cewa addininsu guda ne. Su Arewar ce dai ba su kauna.
Wannan babbar illa ce, domin kuwa ya kara ba ‘yan Kudu damar kara jan damarar wargaza hadin kan Musulim Umma a Arewa, suna haddasa gaba da kiyayya tsakanin malaman darika da kuma na Sunni, wadanda suka dukufa, ido rufe, suna daukan matakan da za su kara nisanta su da juna, don neman girma da daukaka daga wajen jama’a da shugabannin gwamnatoci, sun manta da martabar addininsu da kuma irin zagon kasar da ake yi masa don a raunana mabiyansa. To ya kamata fa a fahimci cewa sake haurowar mulki zuwa Arewa zai yi wuyar gaske, domin kuwa an rigaya an yi amfani da addini an shiga tsakanin Musulmi da Kiristocin yankin, hadin kai tsakaninsu ya faskara. Muddin ba Musulmin Arewa sun hada kawunansu wuri guda ne ba, ‘yan Kudu za su yi ta samun galba a kansu cikin ruwan sanyi.