Hadin kai zai kawo wa ’yan adawa rinjaye a zaben 2015

Haduwar jam’iyyun adawa domin kawar da mulkin PDP na zalunci a Najeriya, mataki ne da ya dace, wanda tuni ya kamata a yi shi. Amman akwai wajibcin yin wani shiri na ko ta kwana, ta hanyar hada kan kungiyoyin ‘yan Najeriya masu kishin al’umma da kuma tsoron Allah, marasa kwadayi ko tsoron wanda ba Allah, […]

Hadin kai zai kawo wa ’yan adawa rinjaye a zaben 2015
Hadin kai zai kawo wa ’yan adawa rinjaye a zaben 2015

Haduwar jam’iyyun adawa domin kawar da mulkin PDP na zalunci a Najeriya, mataki ne da ya dace, wanda tuni ya kamata a yi shi. Amman akwai wajibcin yin wani shiri na ko ta kwana, ta hanyar hada kan kungiyoyin ‘yan Najeriya masu kishin al’umma da kuma tsoron Allah, marasa kwadayi ko tsoron wanda ba Allah, yadda za su zama ginshikan kawo sauyi daga zalunci zuwa adalci mai dorewa.
Kasancewar jam’iyyun siyasa komai karfinsu idan sojoji suka yi juyin mulki, sukan soke su. hakan ba ta taba faruwa a kan kungiyoyi ba. Ba zan taba mantawa da irin wuyar da wasu daga cikin shugabannin wasu kungiyoyi suka sha. a hannun sojoji a kasar nan. wannan yasa na fara gudanar fa bincike akan jam’iyyun siyasa, don shi ne dalilina na bada shawara  duk wasu kungiyoyin da ba na siyasa ba, su ma su hadu, su dunkule domin shirin ko ta kwana. Ballantana kowa ma ya ga yadda duk jam’iyyun suke kunshe da wakilan PDP, bacin mutanen da ake fitar da makudan kudi da sunan kamfanoninsu, da wasu ma’aikatan gwamnati a nemi kudin a rasa inda suka shiga, sai zabe yazo, da ma an jefa talakawa a mawuyacin hali; a kan sabulu da taliya da ashana da Naira 50. karshenta wahala ta karu, a yi ta ganin annoba iri-iri, Allah ya tsare mu Ameen.
*…Shin haka za mu kasance, mu ci gaba da zama ana yi mana mulki kama karya? ‘yan Nigeria mu farko mu ceto kasarmu tunda dai wadanda suke da ikon sauke sun zama yan’amshin shata yanzu ko wadannan abubuwa ya kamata Talakawa farar hula. Sai dai idan ba da gaske ake ba. Abin da ke faruwa a Najeriya lamari ne da ke bukatar aikin agaji na gaggawa; ga kowane dan kasa, don haka shugaban kasa ne ya kamata ya tunkari gabansa. Bai dace ya danka wa wani ragamar tafiyar da sha’anin tsaro a irin wannan lokaci ba. Wannan fa tamkar batu ne irin na asibiti.
A lokacin da babu gagarumar matsala, likitoci suna iya wakilta jami’an jinya da sauran masu taimaka wa likitoci ta hanyar ba su umarni. Amma a lokacin da a ke bukatar taimakon gaggawa, likitan ne da kansa ya ke shiga dakin tiyata ya dauki wukar fida. To, a nan ma wannan ne lokacin da ya kamata babban kwamandan askarawan kasa na Najeriya zai sanya kaki da kansa. Idan ban da lallacewar shugabanci ana ta kashe-kashe a wasu yankuna. Barno da Yobe da Adamawa da sauran sassa na kasa a ce shugaba yaki zuwa sannan aka sace ’yan mata ’yan makaranta sama da 200, shugaba bai shirya ganin iyayen yaran nan ba, sai da wata matashiya ta taso tun daga Pakistan ta ga shugaban kasa don lallacewa, sannan ya shirya ganinsu don sun ki shine ya ji haushi, to su ba su ji haushi ba, sai kai da babu ’yar ka a ciki? Allah ya kyauta! Ashe babu dadi to, da wannan nake kiran al’umma da mu yi wa musu bore.
A kullum ’yan Najeriya da yawa ne suke mutuwa, amma abin takaici shi ne wadanda ke da alhakin magance matsalar ba su san inda suka saka gaba ba.
Ida ita siyasa take bukatar mutane na kwarai, saboda da ita ake yin mulki, yanzu ta zama wulakantacciyar sana’a, duk wani mugu sai ya ce shi dan siyasa ne, ya yi ta raba kudi a zabe shi sai abin da hali ya yi, Allah ya sa mugane, mu canza.
Hadarin munafuki ya fi na makiyi, ko a lahira wutar munafukai tana karkashin ta Yahudawa.
Alamomin munafuki uku ne 1-Idan aka ba shi amana ya yi yaudara. 2-Idan ya yu magaba ya yi karya. 3-Idan ya yi alkawari yaki cikawa.Duk wani dan Najeriya mai hankali ya yadda bangaren shari’a da na zartarwa da na dokoki suka lallace, suka sukurkuce, hukumar zabe da jami’an tsaro da dimokuradiyya kanta duk sun zama akwai ya babu. duk wadanda aka zaba da masu hankoron a zabe su, saboda lalacewar al’amarin illa kalilan, da abin da ba a rasa ba. suma kusan sun bata a yamma. duk rafkanuwar da masu mulki suke yi idan ka ce, subhanallah, to ka zama makiyi, babu maganar gyarawa ko a jawo wani daga bayansa, shi ya koma baya. bacin sallah kuwadaga liman ne idan ya yi rafkanuwa aka ce subahanallah, yakan gyara, sai a jawo shi  baya wani ya zama limamin ya gyara a cigaba da yin sallar. Da ma duk wanda ya iya salla, ya san kabli da ba’adi, shi ma liman ne ko da bai saukar kur’ani ba, muddin ya cika shekarun hankali ko balaga. Ala ayyi halin maganar mulki da shugabanci magana ce ta adalci akan kowa da kowa.
Mulki shi ne karshen karfi na yin gyara ko barna, saboda haka bai kamata a danka mulki a hannun mabarnaci ba, Basidi ko hauhabu ko murakkabu. duk wata amanar mu, ya kamata mu nema mata ahalin da ya dace da ita, musamman amanar rayukanmu da lafiyarmu da dukiyarmu da mutuncinmu da adininmu. Kada mu zo duniya a banza, mu rayu a banza, mu mutu a banza. Babu abin da Allah zai canza mana sai mun canza, mun daina saba wa Allah. karshen halaka, mutum ya yarda, idan ya saba wa Allah sai Allah ya biya masa bukata. har a rika fifita wanin Allah, wa’iyazubillah.
Ga duk mawadata musamman wadanda suka mallaki rijiyoyin mai da kamfanoni sadarwa da bankuna da masana’antu su yi kyakkyawan amfani da wannan da ma su zuba jarinsu a yunkurinmu na hada kan kungiyoyin da bana siyasa ba, wadanda ba su da alaka da gwamnati. Su yi mana taimakon gaggawa tunda har yanzu muna da sauran lokaci wajen magance yunwa da cututtuka, domin rage zafin kiyayyar da ke tsakanin masu mulki da talakawa. Komai girman matsala Allah ya tanadi yadda za a maganceta cikin ruwan sanyi, har ma da yadda za a kauce mata baki daya. Idan an ki, sai a yi ta shiga halaka, fatan mu dai Allah ya tsaremu.

Anas Saminu Ja’en na Muryar Talaka, ya rubuto makalarsadag Jihar Kano.07033882307,08188742103

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya