Hadin kan al’umma ce mafita ga Najeriya

Mahukuntan Najeriya da talakawanta sun tabbatar da cewa wannan kasa tamu na fama da matsalar tsaro da zamantakewa da tattalin arziki, don haka nike ganin hadin kan al’ummarta shi ne mafita ga kasar. Da zarar hukuma ta daina sauke nauyin al’umma da ya rataya a gare ta, da zarar an samu rashin doka da oda […]

Hadin kan al’umma ce mafita ga Najeriya
Hadin kan al’umma ce mafita ga Najeriya

Mahukuntan Najeriya da talakawanta sun tabbatar da cewa wannan kasa tamu na fama da matsalar tsaro da zamantakewa da tattalin arziki, don haka nike ganin hadin kan al’ummarta shi ne mafita ga kasar. Da zarar hukuma ta daina sauke nauyin al’umma da ya rataya a gare ta, da zarar an samu rashin doka da oda a tsakanin wadanda ake mulka.
Matukar muka takura tunaninmu kan bama-bamai da ake kai hare-hare da su a birane da kauyuka; ko satar shanu da halaka Fulani, tabbas babu inda za mu je a rayuwa. Domin wadannan al’amura da ke faruwa kullum suna dauke hankalin ’yan Najeriya daga matsalolin rashin wutar lantarki da ruwan sha tsaftatacce da rashin ayyukan yi a tsakanin matasa.
Mawuyacin halin da al’ummar kasar nan suka samu kansu a ciki, na nuni da cewa akwai gazawa daga shugabanni. Kuma ba wani abu ya haifar da haka ba, illa dai matsalar talaka ba tasu ba ce, tunda kamar yadda wani sharhi ke fada cewa da ’yan matan nan da aka sace akwai ’ya’yan manyan Najeriya, ai da tuni an bi duk hanyar da ta dace, an ceto su daga hannun wadanda suka kama su. Abin takaicin ma shi ne, shugabannin sun nuna shakku kan sace ’yan matan, har sai da kungiyar Kiristocin Najeriya ta baje sunayensu kowa ya gani.
Ganin cewa duk bala’in da ya shigo kasar nan a kan talakawa yake karewa, lokaci ya yi da za mu sake salo wajen zaben shugabannin da za su dauka matsalar da ta shafe mu ta su ce; karatun ’ya’yanmu ya zamo iri daya da na su; idan kamu da rashin lafiya asibiti guda za mu je da su. Mu kuma tabbbatar da cewa ba a kebe wasu muhimman wurare da ake samun kudi a aikin gwamnati ga ’ya’yan manya kawai ba. Kada mu bar makomarmu a hannun wadanda ba su damu da mu ba. Mu yunkura wajen kawo sauyi, ta hanyar zaben shugabannin da ke tunaninmu a zukatansu.
kalubalen warware wannan matsala da al’ummar Najeriya ke fama da ita, na mikata ga Jam’iyyar Adawa ta APC, musamman kungiyar ’yan kishin kasa ta APC forum. Na kuma mika wannan kalubalen ga kungiyoyin kwadago, musamman NLC da TUC. Uwa-uba al’umma, mu hada karfi wajen warware matsalolin da al’umma ke fama da su, ba tare da la’akari da bambancin kabila ko addini ko yanki ba. Wannan ita ce mafita ga Najeriya.
Alhaji Isyaku Umar danHadeja, ya rubuto daga  Malam-Madori, Jihar Jigawa.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno