Hadin Kan Kasa: Malaman Musulunci 300 sun hallara a Kwara

Sun yi taron ne domin tattaunawa kan ayyukansu da naunyin da ya rataya a wuyansu na samar da hadin kan kasa

Hadin Kan Kasa: Malaman Musulunci 300 sun hallara a Kwara

Sama da limamai da manyan malaman Musulunci kimanin 300 sun yi taro domin tattaunawa kan ayyukansu da naunyin da ya rataya a wuyansu na samar da hadin kan kasa.

Shirin mai taken ‘limami na gari, mamu na gari, al’umma ta gari’ Cibiyar Musulunci ta Daru-s Sa’aadah ce ta shirya shi a yankin Ajase-Ipo da ke jihar Kwara.

Karo na farko da taron ke gudana a jihar tun shekarar 2016 da cibiyar da ke Jihar Ogun ta fara shirin, wanda Babban Mufti na Majalisar Malamai, Sheikh Dhikrullah Shafi’i, yake daga cikin amintattun kungiyar.

A jawabansu na bude taron, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya Atoloye Alebiosu da babban limamin al’umma, Sheikh Taofik Aliyu Atoloye, sun ce taron da horaswa zai taimaka wajen kiyaye koyarawar addinin Musulunci ta hanyar wayar da kan malamai wadanda su kuma za su taimaka wajen shiryar da mutane zuwa ga takawa.

Sun kara da cewa taron zai canza tare da inganta yanayin aiki da fahimta na limamai da kuma yin addinin Musulunci a aikace.

Daya daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi, Farfesa AbdulRasaq Abdulmajeed Alaro, ya bayyana cewa matsayin malamai na alhaki ne ba wai suna kawai ba.

Don haka ya bukace su da farge kan ayyukansu na jagorantar jama’a zuwa ga tafarki madaidaici daidai da koyarwar Islama.

Farfesa Alaro, mashawarcin babban bankin kasa CBN kan harkokin bankin Musulunci, ya bukaci limamai da su farfado da masallatai domin biyan bukatunsa na ilmantarwa da magance rikice-rikicen addini da sauransu, ta hanyar “Imam yana jagorantar jama’a Sallah da kuma wa’azinsa, ya zama abin koyi kuma jagora.”

A nasa bangaren, Babban Limamin Babban Masallacin Lekki da ke Legas, Dakta Ridwanullah Jamiu, ya ja hankalin limamai da su kasance masu nagarta wajen ganin an samu hadin kan kasa.

Daga nan sai ya bayyana cewa masallaci wuri ne na hadin kai da hidima da kuma al’amuran zamantakewa da tattalin arziki da tunani da tunani na jama’a.

Wani mamba a kwamitin shirya taron, Imam Ismail Yusuf, ya shaida wa manema labarai cewa, “Sama da limamai 300 galibinsu daga al’ummar Yarbawa ne suka taru domin a nuna musu irin rawar da suke takawa da kuma yanayin zamani domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na shugabancin addini”.

Shugabar taron, Hajiya Rahmatallahi Akansin ta ce dalilin taron shi ne kara ilimi ga shugabannin addinin Musulunci da aka dora wa alhakin gyara matsalolin da ke faruwa a cikin al’umma.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi