Hadin Kan kasa: Matsayin kungiyar ACF Dangane Da Al’amuran Biyafara

Alhaji (Dokta) Ibrahim Ahmadu Coomassie (GCON), shi ne Sardaunan Katsina, Garkuwan Hausa kuma Shugaban kungiyar Tuntuba ta Arewa. A ranar Asabar, 20 ga watan Fabrairu ne aka yi bikin mika masa digirin girmamawa a Jami’ar Najeriya Nsukka, inda ya gabatar da jawabi mai nusarwa da fadakarwa. Muhimmancin jawabin ne ya sanya muka kawo muku shi […]

Hadin Kan kasa: Matsayin kungiyar ACF Dangane Da Al’amuran Biyafara
Hadin Kan kasa: Matsayin kungiyar ACF Dangane Da Al’amuran Biyafara

Alhaji (Dokta) Ibrahim Ahmadu Coomassie (GCON), shi ne Sardaunan Katsina, Garkuwan Hausa kuma Shugaban kungiyar Tuntuba ta Arewa. A ranar Asabar, 20 ga watan Fabrairu ne aka yi bikin mika masa digirin girmamawa a Jami’ar Najeriya Nsukka, inda ya gabatar da jawabi mai nusarwa da fadakarwa. Muhimmancin jawabin ne ya sanya muka kawo muku shi nan, kamar haka:

Ba karamar girmamawa ba ce gare ni da fitacciyar Jami’ar Najeriya Nsukka ta karrama ni da digirin girmamawa. Jami’ar Najeriya Nsukka, ita ce jami’a ta biyu da aka fara kafawa a Najeriya a cikin shekarar 1955. Tun daga wancan lokaci jami’ar ta nuna alamar cewa za ta tsere wa tsara, domin kuwa ta share hanyar ayyukan ginawa da raya kasa, tare da bullo da hikimomin bunkasa al’amura daidai da ci gaban duniya baki daya. Irin wannan bunkasassa kuma shahararriyar jami’a, a ce ta tsamo ni kuma ta karrama ni, babu shakka wannan daya ce daga cikin ranaku mafi farin ciki a rayuwata.
Baya ga shi Mataimakin Shugaban Jami’a, wadannan muhimman mutane da suka hada da Shugaba da mukarrabansa na gudanarwar jami’ar da sauran duk wanda ya sanya hannu har aka kai ga cin ma amincewa da wannan karamawa tawa, ina miko maku babbar godiya ta musamman.
Dukanmu nan da muka amfana daga wannan mabubbugar ilimi, ya zama wajibi mu gode wa Allah da kuma dukkan wadanda suka taimaka wajen gina wannan jami’a zuwa wannan matsayi nata, ba tare da gajiyawa ba. Kada mu taba mancewa, cewa wannan jami’a ta samu ne daga namijin kokarin iyayen kasa masu kishi, ta hikimar muhimmin mutum, Dokta Nnamdi Azikiwe, Gwamna-Janar na karshe kuma Shugaban kasar Najeriya na farko. Hakilo da gwagwarmayar da suka yi jiya, ta haifar mana da ci gaba a yau, don haka ya zama dole mu ma mu shiga tunani, mu san hanyoyin da za mu ba da namu tallafin, domin ’ya’yanmu da jikokinmu su yi alfahari da mu, ko ma amfana da addu’o’insu.
Ina ganin ya dace in fadada jawabin nan nawa, dangane da yadda na ga ana kiraye-kiraye don a raba kasar nan, tare da kokarin kafa kasar Biyafara. Ya shugaban jami’a, a matsayina na Shugaban kungiyar Tuntuba ta Arewa, bai kyautu in yi jawabin nan ba tare da na bayyana matsayinmu ba, yadda muka cije kuma muka tsaya kai da fata cewa lallai ba mu goyon bayan raba kasar nan. Muna goyon bayan dorewar Najeriya, a matsayin kasa daya, al’umma daya cikin hadin kai da ci gaba.
Muna ji ana yada maganganu cewa: ‘Mene ne amfanin ci gaba da zaman kasar nan a hade, alhali zaman taren bai da tasiri?’ Ko kuma ka ji ana cewa: ‘Arewa ce kadai ta dage sai an ci gaba da zama a Najeriya saboda ba ta da wata dukiyar kasa, alhali a Kudu akwai arzikin mai.’ Wasu kuma suna cewa: ‘Idan har Sudan da Yugoslabiya za su rabu, me zai hana Najeriya ta dare?’ Babbar manufar wadannan maganganu dangane da raba Najeriya ita ce, wasu kungiyar mutane ko kabilu sun mamaye kuma sun danne wasu. Abin da ya fi ciwo da ban haushi dangane da wannan shi ne, ba wai kiran a raba kasar ba ne kadai, amma yadda wasu ke kokari da yunkurin ganin sun tsunduma kasar nan cikin yakin basasa. Ana ta tunzura matasa, ana hilatarsu domin su dauki makamai. Ana yi musu karkatattar hudubar rura wutar kiyayyar wasu bangare na kasa ko na wasu kabilu. Akwai wata rana da idanuwana suka ci karo da wani mugun zance, mai cewa: “Arewa ita ce matsalar Najeriya, dalili ke nan Najeriya ba ta ci gaba. Mu raba Najeriya, mu cire Arewa daga cikinta, za mu ga Najeriya ta bunkasa.”
Abin lura a nan shi ne, matsalar Najeriya ba ta girman kasa ba ce, ba kuma ta yunkurin da ake cewa na wasu sun danne wasu ba ne. Matsalar Najeriya dai ita ce, kamar yadda shahararren marubucin nan, Chinua Achebe ya bayyana: “Matsalar Najeriya dai ita ce, gazawar shugabanci.” Irin wannan bayanin dai ne shi ma wani dan kishin Najeriya, marigayi Chif Sunday Awoniyi ya ce:
“Mu (Shugabannin Najeriya), mun kasance masu tsananin hadama kuma ga mu da bakar rowa. Mun cika hadama da rige-rigen tara dukiya, ga shi kuma ba mu iya kyauta da nuna jinkai ga marasa galihu ba. Ga mu da kasala da kyuyar aiwatar da ayyukan da suka wajaba a kanmu. Mun kuma siffatu da aiwatar da aikin baban giwa. Tunaninmu game da aikin ofis ya canza daga hidimar al’umma zuwa ga hidimta wa kawunanmu, inda muke wawura da babakeren dukiyar kasa domin biyan muradin kawunanmu.”
Ba tare da raba daya biyu ba, idan aka yi la’akari da wadannan bayanai na gaskiya da suka gabata, babu shakka al’umma za su dawo daga rakiyar kurarin raba kasar nan. Ya kamata mu lura da wannan, a can baya, mun wahalar da kanmu, mun yi yakin basasa, inda muka rasa mutane sama da miliyan daya. Ina ganin hatta makiyinmu, ba zai kaunaci mu sake komawa cikin wannan yanayi na yakin basasa ba. Darussan da ke cikin tarihi sun ishe mu mu hankalta, mu yi la’akari da yadda muke rasa rayuka a sanadiyyar hargitsi, a duk lokacin da aka fara wannan yunkuri na raba kan kasa. Haka kuma, akwai misalai da dama daga wasu kasashe da al’ummu, yadda suka kasance a sanadiyyar yakin basasa ko na kabilanci. Mu duba kasashen Pakistan da Bagladash da tsohuwar Yugoslabiya, da kuma abin da ya faru na baya-bayan nan a Sudan. Idan mun lura, tun bayan da Sudan ta Kudu ta balle daga Sudan take cikin sabbin rikice-rikice masu nasaba da kabilanci da bangaranci.
Ya Shugaban Jami’a da mahalarta taro maza da mata, tun daga ranar 29 ga Mayun 2015 da aka rantsar da sabuwar gwamnati, tone-tone da bankade-bankaden yadda aka wawashe dukiyar kasar nan suka yi ta fitowa. Wannan al’amari kuwa abu ne mai matukar firgitarwa, yadda jami’an gwamnati da shugabannin da aka zaba domin rike amanar al’umma suka maida dukiyar gwamnati tamkar tasu. A kasar nan, kusan ba inda za ka ga ana aikin gwamnati don hidimta wa jama’a, babu tsaro sai dan abin da ba a rasa ba. Al’umma sun wayi gari suna gani cewa Gwamnati ta watsar da mafi yawan ayyukan da suka wajaba a kanta, na kare rayuka da dukiyoyin al’umma; domin kuwa dukiyar da aka ware domin wadannan ayyuka an wawashe su, an zurara su cikin aljifan ’yan siyasa da makusantansu. Wadannan al’amura, babu shakka su ne cikakkun shaidun da ke kara tabbatar mana da cewa, lallai matsalar Najeriya ta ta’allaka ne ga lalacewar shugabanci.

Za mu kammala makon gobe