Hadin Kan kasa: Matsayin kungiyar ACF Dangane Da Al’amuran Biyafara (2)

Alhaji (Dokta) Ibrahim Ahmadu Coomassie (GCON), shi ne Sardaunan Katsina, Garkuwan Hausa kuma Shugaban kungiyar Tuntuba ta Arewa. A ranar Asabar, 20 ga watan Fabrairu ne aka yi bikin mika masa digirin girmamawa a Jami’ar Najeriya Nsukka, inda ya gabatar da jawabi mai nusarwa da fadakarwa. Muhimmancin jawabin ne ya sanya muka kawo muku shi […]

Hadin Kan kasa: Matsayin kungiyar ACF Dangane Da Al’amuran Biyafara (2)
Hadin Kan kasa: Matsayin kungiyar ACF Dangane Da Al’amuran Biyafara (2)

Alhaji (Dokta) Ibrahim Ahmadu Coomassie (GCON), shi ne Sardaunan Katsina, Garkuwan Hausa kuma Shugaban kungiyar Tuntuba ta Arewa. A ranar Asabar, 20 ga watan Fabrairu ne aka yi bikin mika masa digirin girmamawa a Jami’ar Najeriya Nsukka, inda ya gabatar da jawabi mai nusarwa da fadakarwa. Muhimmancin jawabin ne ya sanya muka kawo muku shi nan, ga kashi na biyu kuma na karshe kamar haka:

Abu ne mai muhimmanci a gare mu a kasar nan, a duk lokacin da ake son daukar wani mataki, to a rika yin la’akari da abin da hakan zai iya haifarwa ga al’ummarmu ta gobe. Mu rika jinjina muhimmancin al’amarin ko akasinsa. Kada mu mance, Najeriya kasa ce da ke dauke da jihohi 36 da kananan hukumomi 774 kuma duk kwabon da ke shiga lalitar kasar nan, ana raba shi ne tsakanin sassan gwamnati uku, kamar yadda tsarin rabon arzikin kasa ya tanadar a karkashin kundin tsarin mulki. Kada fa mu dauke kai daga wannan bayanin: Kason da ake ba wata jiha daya a yankin Neja-Delta, shi ake ba jihohi kusan shida na Arewa. Kuma ga wata gaskiya nan tsirararta, mu duba kasafin kudin bana, a karkashin Gwamnatin Tarayya, wadda dan Arewa ke wa shugabanci, amma manyan ayyukan da za a gabatar a bana, a yankunan Kudu maso kudu da Kudu maso yamma sun ninka na ayyukan da za a gudanar a dukkan yankuna uku na Arewa gaba daya. Amma duk da wannan kashin dankalin da ake wa Arewa, sai wani ya tubure gefe guda yana kukan cewa ana yi masa wariya!
Idan muka waiwaya baya, tun da aka shigo mulkin dimokuradiyya daga 1999 ake antaya wa jihohin Kudu makudan kudi daga asusun Gwamnatin Tarayya. Shin anya abin nan ya dace da hankali a ce wani bangare na kasar nan zai yi ikirarin ana yi masa wariya, idan aka yi la’akari da wannan tsarin? Idan har na duba jihata ko karamar hukumata ban ga wani aikin ci gaba ba, shin ba sai in fara tuntubar masu mulkin yankin nawa ba a jiha ko karamar hukuma?
Mu dai a nan kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), tun da dadewa muka ankara da cewa, har sai an samu shugabanni nakwarai da za su jagoranci kasar nan, sannan za a samu zaman mutunci tsakanin sassan kasa, a samu ci gaba a kasa tare da zaman lafiya. Wani mataki da muka dora wa kanmu shi ne, sada zumunci tsakanin kabilun Najeriya. Tuni mun kai caffa ga kungiyar Shugabannin Yarabawa ta Afenifere da ta Ibo, wato Ohanaeze Ndigbo da kungiyar Al’ummar Kudu Maso Kudu da kuma shugabannin kabilun Itsekiri da Urhobo da kuma kungiyoyin ’yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje. Ba za mu gajiya ba har sai sun kulla kyakkyawar alakar zumunci a kowane sashi na al’ummar kasar nan.
Ina ganin ya zama dole in kara bayani, cewa duk da irin kokarin da muke na hadin kai da neman zaman lafiya, ba fa yana ishara ba ne da cewa komai ya daidaita a kasar nan. Babu shakka Najeriya tana matukar kishirwa da neman taimako. Babu raba daya biyu, kasar nan tana fuskantar barazana, musamman yadda al’amura suka tabarbare, ’yan kasa sun rasa karsashi. Ya zama wajibi mu yi aiki tukuru, mu fitar da kasar nan daga duhun zaluncin da ta samu kanta. Ya zama dole mu sake dasa ingantattar tarbiyya ga al’ummarmu, ta fuskar aikin gwamnati, wanda babu wanda zai yarda ya bari abin ya ida lalacewa. Ya zama dole a dawo da martabar aiki da tafiyar da al’amuran gwamnati, yadda ma’aikata za su jajirce su yi aiki tukuru, domin daukaka martabar kasar nan da al’ummarta.
Idan muka sanya wadannan kudurori a gabanmu, ganin cewa mun samu nagartaccen shugaba a zaben bara, wato Muhammadu Buhari, muna sa ran a samun ci gaba a kasar nan. An bayyana cewa, ingancin shugaba ya rataya ne da kudurorin da ya gindaya wa kansa. Wannan kuwa ya zama hakkun ga Shuagba Buhari, wanda na yi katarin sanin halayensa tun muna yara, domin kuwa ajinmu daya da shi tun daga makarantar firamare. Buharin da na sani, yana da halayen da’a da jajircewa wajen bibiyar abin da ya sanya gaba, har sai ya samu nasara. Muna fata tare da addu’a, da taimakon Allah da tallafin al’ummar kasa, Buhari ya gyara kasar nan, batun cin hanci da rashawa da satar dukiyar kasa da rashin da’a su zama tarihi. Idan ana son samun nasara a wannan kuduri, dole ne sai an yi wa kundin tsarin mulkinmu kwaskwarima, musamman ma dai sashin dokar da ya ba wasu zababbun shugabanni wata kariya, cewa ba za a gurfanar da su gaban kuliya ba, madamar suna kan madafun iko. Lallai ne wannan kariya ba ta kamata ta hada har da manyan laifuka ba.
Shuagaban kasa Buhari dai ba mai saddabaru ba ne, domin shi da kansa ya tabbatar da haka da bakinsa, amma gami da hadin kan al’ummar Najeriya, musamman matasa, wadanda ke a shirye su rungumi canje-canje masu kyau da kawo ci gaba, lallai ne muna da yakinin ganin babban canji mai inganci, na sake gina kasar nan, Najeriya.
Daga karshe, a madadin Mai Sarauta, Obi na Onitsha da kuma abokan karramawata, muna godiya ga Jami’ar Najeriya, Nsukka, saboda karrama mu da ta yi a yau. Na dauki alwashin kasancewa jakadan wannan jami’a a kowane lokaci.
Ya Shugaban Jami’a, sauran ’yan kasa nagari, ina yi muku godiya matuka saboda hakurinku. Bari in yi maku bankwana da wadannan muhimman kalamai a matsayin sako: Kada mu sake mu kashe Najeriya. Mu yi kokarin kashe duk wani abu da ke kashewa ko yake kokarin kashe Najeriya!
Mun kammala