Hadin kan Musulmi da Kirista zai wanzar da zaman lafiya – Ustaz Musa
Wani malamin Addinin Musulunci, wanda ke da zama a Unguwar Itamakpako Ijebu –ode, Ustaz Musa Muhammed Sani Aladori ya bayyana hanyar da yake ganin ta dace al’ummar kasar nan su bi, domin wanzuwar zaman lafiya, wato a cewarsa, Musulmi da Kirista su hada kansu, su rungumi juna tamkar uwa daya, uba daya, su bi tafarkin […]
Wani malamin Addinin Musulunci, wanda ke da zama a Unguwar Itamakpako Ijebu –ode, Ustaz Musa Muhammed Sani Aladori ya bayyana hanyar da yake ganin ta dace al’ummar kasar nan su bi, domin wanzuwar zaman lafiya, wato a cewarsa, Musulmi da Kirista su hada kansu, su rungumi juna tamkar uwa daya, uba daya, su bi tafarkin gaskiya, su rabu da son zuciya.
“Kuma su mance da irin bambance-bambance da ke tsakaninsu na siyasa da addini da kabilanci ko na yankuna, su rungumi akidar kaunar juna a tsakaninsu,” inji su.
Ustaz Musa Muhammed ya yi bayanin hakan ne a wata zantawarsa da wakilin Aminiya, a karshen makon da ya gabata, inda ya ce: ‘’Ina ganin Duniyar baki dayanta babu abinda yake janyowa alummanta fitintinu da tashe -tashen hankula, ban da son rai na zalunci da mafi yawan mutane suke yi wa juna. Don ya kamata mu dawo akan hanyar gaskiya, mu hada kai mu zama tsinya madaurinki daya, mu manta da duk wani abu mai suna bambanci a tsakaninmu. Domin takan kai mu samu wanzuwar zaman lafiya akasarmu .
Kuma ina kira garemu gaba daya, Musulmi da Kirista da mu mayar da al’amarinmu ga Allah, mu hadu mu zama tamkar Uwa daya Uba daya tare da kaunar juna domin da alkur’ani da Bible duk suna koyar da hadin kan Alumma akan tafarkin Addinin Allah da zaman lafiya tsakaninsu da juna.
Akan batun dage zaben kasa kuwa, cewa ya yi, ‘’Allah shi ya san abin da ya fi zama alheri ga bayinsa.