Hadin tsawon gashi a lokacin damina

Yana kara wa gashi maiko, ya sanya shi tsayi da laushi ya kuma hana shi karyewa.

Hadin tsawon gashi a lokacin damina

Lokacin damina yanayi ne da yake haifar da zubar gashi, wanda idan ba a kula ba yana sanya shi karyewa.

Akwai hanyoyi da dama wadanda mata za su bi domin samar da gashin kai mai tsawo.

Mata da dama suna son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya. Gashi na daya daga cikin ababen da ke kara wa mace kyau, don haka ya kamata mu kula da gashinmu sosai.

Wannan hadin da na kawo muku yana kara wa gashi maiko, wajen hana shi karyewa da sanya shi tsayi da laushi.

Wannan hadin akan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, bai kamata a rika hada wannan gyaran gashin da wani daban ba in ba haka ba, kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba.

Abubuwan da za a buqata
•       Man Amla.
•       Zuma.
•       Ruwan dumi.

Hadi
•       A zuba cokalin amla biyu a roba.
•       Sannan a zuba rabin cokalin zuma a cikin amla.
•       A sanya cokalin ruwan dumi kamar 2-3.
•       A juya hadin har sai sun cakudu da juna.
•       A taje gashi kafin a shafa wannan hadin a fatar kai.
•        A jira na tsawon mintuna 30.
•        A wanke kai da man wanke gashi (shampoo).

•  Man kwakwa: Yana sanya gashi laushi da tsayi da kuma santsi. Yana da kyau a rika shafawa a fatar gashin kai a duk lokacin da za a yi kitso ko kuma a rika gaurayawa a cikin man kitson.

•  Man zaitun: Yana da mahimmanci sosai a jiki baki daya. Sannan kuma yana sanya gashi santsi da baki. Yana kuma magance furfura da kuma sanya gashi tsayi da baki da sheki da kuma kyau.