Hadurran jirgin saman da suka faru a shekarar 2014
Shekarar 2014, shekara ce da za a dade ba a manta ba a tarihi saboda abubuwa da dama da suka faru, musamman ma ta fuskar hadurran da kuma bacewar jiragen sama, inda hatta a kwanakin karshen shekarar aka kara samun hadarin wani jirgin kasar Indonesiya bayan ya tashi daga birnin Surabaya na kasar zuwa kasar […]
Shekarar 2014, shekara ce da za a dade ba a manta ba a tarihi saboda abubuwa da dama da suka faru, musamman ma ta fuskar hadurran da kuma bacewar jiragen sama, inda hatta a kwanakin karshen shekarar aka kara samun hadarin wani jirgin kasar Indonesiya bayan ya tashi daga birnin Surabaya na kasar zuwa kasar Singapore.
Kodayake, wannan ba shi ne karon farko ba da hakan ya faru a shekarar, idan ba a manta ba a cikin watan Maris ma jirgin saman kasar Malesiya mai lamba MH370 ya yi batan-dabo da fasinjoji 239. Kuma kimanin wata 10 ke nan ana nemansa, amma ba amo, ba labari.
Bugu da kari, akwai hadarin jirgin saman kasar Algeriya mai inkiyar 5017, wanda ya fadi a kusa da garin Gossi na kasar Mali, a cikin watan Yunin barar. Jirgin ya tashi ne daga Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso zuwa birnin Algiers na kasar Algeriya. Kuma babu mutum guda da ya tsira daga hadarin cikin fasinjojin jirgin 110 da ma’aikatansa su shida.
Har ila yau, akwai wani jirgin mallakin Malesiyan, mai inkiyar MH17, wanda ake zargin ’yan tawayen kasar Ukraine sun kakkabo a cikin watan Satumba, bayan ya nausa yankin Gabashin kasar, inda akalla fasinjoji 298 suka rasa rayukansu.
Sai kuma hadarin jirgin saman karshe, wanda ya faru ranar Lahadin da ta gabata, jirgin mai lamba kZ8501, mallakin kasar Indonesiya yana dauke ne da fasinjoji 162. Kodayake zuwa shekaranjiya Laraba, rundunar ruwan kasar ta ce an gano gawawwaki 40 tare da wasu daga cikin tarkacen jirgin a cikin teku.