Hadurran mota sun ci rayukan mutane 23 cikin kwana 2 a Oyo

Mutane 23 sun rasa rayuka a wasu hadurran mota da aka yi sau 2 a cikin kwanaki 2 a kan manyan hanyoyin mota na Ibadan zuwa Legas da Oyo zuwa Ibadan.Hadari na farko ya auku ne a ranar Lahadi da safe a tsakanin wata babbar motar tirela da karamar motar bas kirar Peugeot J5 da […]

Hadurran mota sun ci rayukan mutane 23 cikin kwana 2 a Oyo
Hadurran mota sun ci rayukan mutane 23 cikin kwana 2 a Oyo

Mutane 23 sun rasa rayuka a wasu hadurran mota da aka yi sau 2 a cikin kwanaki 2 a kan manyan hanyoyin mota na Ibadan zuwa Legas da Oyo zuwa Ibadan.
Hadari na farko ya auku ne a ranar Lahadi da safe a tsakanin wata babbar motar tirela da karamar motar bas kirar Peugeot J5 da suke kan hanyar zuwa Legas daga Arewacin kasa, a inda suka rika yin rige-rigen tsere wa juna da gudun ganganci; wanda ya kai ga gugar juna da faduwa da suka yi a daidai kauyen Sepo a kusa da Ibadan, a inda aka tabbatar da mutuwar mutane 17 a nan take.
Wakilinmu ya samu labarin cewa, motar tirelar tana dauke da fasinjoji fiye da 80 da kaya masu yawa a cikinta da suka taso daga Jihar Katsina zuwa Legas.
Hadari na biyu kuwa ya auku ne a ranar Litinin da ta gabata, a lokacin da wata motar bas mai dauke da fasinjoji 18 wacce taya ta fashe ta yi kuli-kulin kubura a kan hanyar Oyo zuwa Ibadan, a inda mutane 6 duka daliban makarantar Polytechnic ta Ibadan suka rasa rayukansu.
Hudu daga cikinsu sun mutu ne a nan take a yayin da sauran biyu suka cika a wani asibiti da ke garin Oyo.
Kwamandan Rundunar kiyaye hadurra (FRSC) na Jihar Oyo, Mista Yusuf Salami, shi ne ya jagoranci jami’ansa zuwa wajen hadari na farko da suka kwashe gawarwakin mamatan zuwa asibitoci daban-daban a Ibadan. Jim kadan bayan samun wannan labari da al’ummar Musulmi ’yan Arewa da ke Ibadan suka garzaya zuwa fadar Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, wanda a nan take ya bayar da rubutacciyar takarda zuwa ga asibitocin da aka nemi su bayar da gawarwakin mutanen; domin a yi masu sutura da binne su a makabartun Musulmi, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Wakilinmu ya samu labarin cewa daga cikin mutane 79 da suka samu raunuka da aka kai su asibitoci, domin yi masu magani, an kara samun wasu daga cikinsu da suka rasa rayuka.