Haduwata da masu garkuwa da mutane – Jibril Direba

Jibril Muhammad Direba ne da ya kubuta daga hannun masu satar mutane suna yin garkuwa da su a hanyar Zariya zuwa Kaduna a makon jiya. A zantawarsa da Aminiya ya ce sai da ya yi gudun sa’a uku a cikin daji kafin ya tsere musu bayan sun nemi ya biya su Naira miliyan biyu:   […]

Haduwata da masu garkuwa da mutane – Jibril Direba

Jibril Muhammad Direba ne da ya kubuta daga hannun masu satar mutane suna yin garkuwa da su a hanyar Zariya zuwa Kaduna a makon jiya. A zantawarsa da Aminiya ya ce sai da ya yi gudun sa’a uku a cikin daji kafin ya tsere musu bayan sun nemi ya biya su Naira miliyan biyu:

 

An ce masu garkuwa da mutane sun sace ka, yaya lamarin ya kasance?

kwarai an yi haka, na dauki fasinja zuwa Kano na kai su tashan Gyadi-Gyadi, ýina hanyar dawowa a ranar Alhamis da misalin karfe 11 na dare ina biye da wani mai mota kirar J5 sai wadansu mutane sanye da kakin sojoji suka fito kan hanya.  Sai na tsaya saboda ganinsu cikin kayan soji. Kuma ganin mai motar da ke gabana ya tsaya sai ni ma suka ce in gyara tsayuwar motata da kyau, sai daya daga cikinsu ya tsaya a bakin kofar direba ya ce kada in fito ta nan sai dai in fita ta bangaren kofar fasinja.  Sai na fita ta inda ya ce na bar mabudan mota a jikinta. Da ni da fasinjana suka ce mu kwanta a kasa bayan mun kwanta, suka lalube mu. A cikin fasinjojina akwai wadanda suka karbe wa Naira dubu 50, ni kuma Naira dubu shida ne a jikina. 

Motoci kuma na ta zuwa suna tsare su. Wadansu kuma suna kubuta idan ba ka tsaya ba sai su bude wuta. Bayan sun kammala sai na ce da su ai ni ne na farko da na fara ba da wayata da Naira dubu shida, amma sai suka zage ni tare da cewa ai ba wannan ne ya dame su ba. Sai na yi shiru muna kwance a kasa bayan sun dawo gefenmu sai suka ce ina diraban motar Sharon? A tsammanina za su ce ne in shiga mota in tafi, sai na mike na ce gani nan. Sai suka ce in bi su daji mu garkuwa za su yi da mu. A cikin motata an dauki mutum biyu kuma suka kwashe mutum biyu daga cikin motar da ke bayana, daga nan muka shiga daji. Muna ta tafiya tun karfe 11 har zuwa karfe 3:30 na dare kafin muka kai masaukinsu.

Me ka gani a masaukinsu?

Babu kwanukan abinci da tukunyar dafa abinci a wurin. Kuma duk maza ne babu mata, kuma irin abincin da suke ci shi ne dankali na gani. 

A cikinku da aka kama akwai mata?

A’a babu mace ko daya cikinmu dukanmu maza ne biyar.

Yaya aka yi ka kubuta daga hannunsu?

Ni dama tun da suka kama mu na yi niyyar in gudu amma saboda na lura su bakwai ne kuma dukkansu da bindiga ýsai na hakura. Kuma dukansu Fulani ne. 

Yaya aka yi ka gane Fulani ne?

Saboda ina tare da Fulani kuma Fulatanci suke yi duk da cewa ba na jin abin da suke fadi, amma na san dai harshen Fulatanci. 

To, yaya aka yi ka kubuta?

Bayan sun kai mu karkashin wata babbar itaciya mai dauke da abubuwan zama sai suka tura mu ciki. daya daga cikinsu ya dauki kwanon dankali sai ya shiga ciki, sauran biyu kuma sai suka jingina da bishiya daga nan sai barci ya kwashe su. Ni kuma da yake na kudiri aniyar gudu ban yarda barci ya dauke ni ba, duk kuwa da wahalar da muke yi. Sauran na can gefe suna ta danne-dannen wayoyin da suka kwace a hannun mutane, ina ganin wayoyin sun kai kusan 50. Akwai wayar da suka kasa kashewa, sai daya daga ciki ya tambaye ni ko na iya kashewa ko su buge ni. Da na lura hankalinsu ya tafi wajen waya sai daya daga cikin wadanda aka kama mu tare ya ce yana jin fitsari sai suka ce ya tafi ya yi. Ni kuma sai na miki na bi shi kamar zan je in yi fitsarin hankalinsu baya tare da ni. Kafin su ankara, na yi masu nisa. Suka biyo ni amma saboda akwai duhu ba su gan ni ba, sai dai kawai hasken tocilarsu da nake gani daga nesa. Ka ji yadda aka yi ke nan na kubuta. 

Wani hali ka bar sauran mutanen da aka kama ku tare?

Gaskiya ban san halin da suke ciki ba tunda na gudo.

Ina ka bulla bayan ka gudu?

Da na tashi bulla sai na gan ni kawai a wani kauye, na tambayi mutanen da na gani a inda nake, suka fada min sunan kauyen amma gaskiya ban rike ba. Sun dai ce da ni yankin Zariya nake. 

A kauyen ba su tambaye ka inda ka fito ba?

Sun tambaye ni kuma na yi musu bayanin yadda na kubuta daga nan suka ba ni koko na sha. Ina garin misalin karfe shida na safe ne.

Ka yi gudun kusan awa uku ke nan a daji?

Eh, to, na dai fara gudu ne misalin karfe uku da wani abu. 

Lokacin da suke bin ka sun yi harbi?

A’a ba su yi harbi ba, sai dai suna ta bi na ne rike da bindigoginsu. Akwai wani babban kududdufi a wajen, na shiga ciki ina ta gudu har na samu na haura.

Baka ji tsoron naman daji ba a lokacin da ka shiga ciki?

A’a ban ji ba, gudu kawai nake yi. Mutanen da suke kauyen ne daya ya dauke ni a babur zuwa tashar motar da ke Zaria. Daga nan na samu mota zuwa Marabar Jos inda shugabanmu ya tarbe ni suka kawo ni tashar Kawo.

A lokacin da kake hannunsu yaya kake tunanin rayuwarka?

Ni ban dauka a raye nake ba.

Sun buge ku?

A’a ba su buge mu babu wanda ya buge mu a cikinsu.

Yaya za ka kwatanta wurin da suka tsare ku?

Akwai bukka amma akwai dan rata a tsakaninmu da su. 

Me ka manta ba ka fada ba?

A lokacin da suka karbi wayoyinmu. Sai suka tambaye ni ko motar da nake tukawa tawa ce? Na ce a’a akwai mai ita. Sai suka tambaye ni mutumin ina ne? Na ce musu ni mutumin Jihar Nasarawa ne daga garin Lafiya. Sai suka ce za su ba ni wayata in kira gida a tura musu Naira miliyan biyu. ýIdan na gaggauta ina son barin wurinsu, to, a tura musu Naira miliyan biyu su sake ni. In kuma ban shirya ba, su ba su ba da ruwa ko abinci. Yunwa za ta sa in gaggauta a turo musu da Naira miliyan biyu. 

Ashe dankalin da suke dafawa ba don ku da suka ajiye ba?

A’a ba don mu ba ne.