Hafsan dan sanda ya yi bayan gida a jikinsa a bakin aiki

Sufeton dan sanda sanye da kaki ya yi fitsari da bayan gida a jikinsa bayan da ya yi mankas da giya a bakin aikinsa

Hafsan dan sanda ya yi bayan gida a jikinsa a bakin aiki

Jami’in Dan Sanda

Wani hafsan dan sanda sanye da kaki ya yi fitsari da bayan gida a jikinsa bayan da ya yi mankas da giya a yayin da yake bakin aikinsa.

Bayan ganin bidiyon bugaggen Sufeton dan sandan a cikin kaki da ya karade kafofin sada zumuna, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kwara, Paul Odama, ya sa a tsare shi.

Bidiyon da wani dan sanda ya dauka, ya nuna wasu ’yan sanda biyu sanye da kaki sun riko bugaggen dan sandan cikin maye, da kazantar a jikinsa.

An jiyo wadanda suka riko bugaggen dan sandan suna tambayar dayan, wanda da alama na gaba da su ne, cewa, “Oga, ko dai mu afi da shi mu sauke shi?”

Amma mai daukar bidiyon ya ya ce, “A’a, ai har yanzu a bakin aikinsa yake.”

Ya ciga da cewa, “Ku dubi yadda wani Sufeon dan sanda ya yi bayan gida a jikinsa, amma yana cewa albashinsa ya yi kadan.

“Ina so duniya ta gan abin da ka aikata, sannan a jira matakin da mahukunta za su dauka a kan wannan al’amari.”

A binciki kwakwalwarsa —Kwamishinan ’yan sanda

A martaninsa bayan ganin bidiyon, kwamishinan ’yan sandan Jihar Kwara, Paul Odama, a bayyana takaicinsa bisa abin kunyan.

Daga nan ya sa a gano dan sandan a tsare shi, da cewa abin ya wuci na buguwa kawai, akwai bukatar duba lafiyar jami’in.

Kwamishinan ya ce an gano an kuma tsare hasfan dan sandan yana aiki ne a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Share a Karamar Hukumar Irepodun ta jihar, kuma ana duba lafiyar kwakwalwarsa.

“An gano abin ya fi karfin buguwa, har da kwakwalwarsa, amma za a yi amfani da sakamakon gwajin da aka yi masa wajen daukar matakin da ya dace,” in ji shi.

Sanarwar da kakakin rundunar, SP Ajayi OKasanmi ya fitar ta kara da cewa, kwamshinan ya umarci jagororin ’yan sanda na yankin da su ci gaba da lura da jami’in har sai an gama duba lafiyarsa.