Haihuwa ta kankama a sansanin ’yan gudun hijirar Katsina
Yawan hare-haren ’yan bindiga a wasu kananan hukumomin Jihar Katsina ya tilasta bude sansanonin ’yan gudun hijira uku a sassan jihar da suka hada da Batsari da Faskari da Dandume. Yanzu haka ana samun hayayyafar jarirai a sansanonin, yayin da wadansu matan da dama ke dauke da juna biyu, haihuwa yau ko gobe. Ko yaya […]
Yawan hare-haren ’yan bindiga a wasu kananan hukumomin Jihar Katsina ya tilasta bude sansanonin ’yan gudun hijira uku a sassan jihar da suka hada da Batsari da Faskari da Dandume.
Yanzu haka ana samun hayayyafar jarirai a sansanonin, yayin da wadansu matan da dama ke dauke da juna biyu, haihuwa yau ko gobe. Ko yaya mata da yara suka samu kansu a irin wadannan sansanoni?
- ‘Yan bindiga: Gwamnatinmu ta gaza —Gwamnan Katsina
- Sojoji sun kama ‘yan bindiga 21, sun ceto mutum shida a Katsina
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina
“A lokacin da aka kawo hari kauyenmu muka bazama cikin daji, gudu nake ina rusa kuka ni da wadansu mata, ga shi ’yan bindigar sun nufo kanmu a guje. Na ci gaba da gudu ina faduwa ba tare da waiwayawa baya ba, ina cikin wannan yanayi sai nakuda ta taso min. Bayan na dauki wani lokaci ina fama, sai na haihu.
“Matan da muke tare suka lullube jaririyar da tsumma, sannan aka kai mu gidan dan uwana a cikin garin Faskari, aka wanke jaririyar sannan aka sanya mata tufafi, ni kuwa kafata babu takalmi ballantana hijabi; a haka na shigo garin.”
Wannan shi ne labarin Basira Sani, daga kauyen Hurumin Kogo a Karamar Hukumar Faskari, wadda take gudun hijira a makarantar firamare ta Faskari, bayan harin da ’yan bindiga suka kai kauyukansu.
Basari ta ce, “Dana wanda yake taimaka mini ya rasu sakamakon raunin da ya samu a kafarsa lokacin da ’yan bindigar suka kai mana hari. Ina cikin kunci, sannan na rasa ’ya’yana matasa biyu a cikin hare-haren da aka kai mana.”
Mata 40 sun haihu, 70 sun kusa a Faskari
Mutane da yawa suna zaune tare da ’yan uwansu, wadansu kuma sun kama haya a garuruwan da suke da tsaro.
Baya ga Basira, an samu mata 40 wadanda suka haihu a sansanin ’yan gudun hijira na Faskari, wadanda suka tsallake hare-haren ’yan bindigar.
Wadansu daga cikin iyaye mata da Allah Ya kaddara musu, sun hallaka a lokacin harin.
A yanzu haka akwai mata 70 masu dauke da juna biyu a sansanin ’yan gudun hijira na Faskari.
Sannan wadansu hudu sun haihu a sansanonin Dandume da Batsari.
Ungozomomin ne ke karbar haihuwar
Bincike ya tabbatar da cewa a kowane sansani akwai wajen shan magani da aka tanada.
Hakazalika mafiya yawan haihuwar da aka yi a sansanonin, ungozomomin gargajiya ne ke karbar haihuwar, sai ’yan kadan daga cikin malaman jinya da suke halartar wuraren.
Kadan daga cikin masu jegon suke samun damar zuwa asibitin da ke kusa.
Rashin allurar rigakafi
Wani abin lura kuma shi ne, mafiya yawa daga jariran da aka haifa a sansanin da wasu daga cikin yaran da suke zaune a wajen, ba a yi musu allurar rigakafi ba.
Ali Lawal, daya daga cikin masu kula da sansanin gudun hijira da ke Faskari, ya ce tun 19 ga Mayu da mutane suka sauka a sansanin, gwamnati ke ba su kulawar da ta dace.
“Matan da suka haihu muna taimakonsu da rigunan jarirai da sauran ababen bukata. Gwamnati tana matukar kokari wajen tallafa musu da abin da za ta iya,” inji shi.
Ya ce, “A kowace rana muna dafa buhun shinkafa biyar da buhun wake daya da rana, sannan da dare muna dafa buhun masara ko dawa biyar. Sannan a lokacin karin kumallo muna amfani da buhu biyu na gero wajen yin koko.”
Kula da ‘yan gudun hijira
A rahoton da Aminiya ta samu ranar Asabar din makon jiya, akwai mutum 6, 914 a sansanonin ’yan gudun hijira uku da ke sassan Jihar Katsina, wadanda suka hada da 3,260 a Faskari da 3,611 a Dandume da kuma 43 a Batsari.
Kwamishinan Wasanni da Ci Gaban Jama’a na Jihar, Alhaji Sani Danmali, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kula da ’Yan Gudun Hijirar, ya ce gwamnati tana iya kokarinta wajen kula da sansanonin da ke jihar wajen samar da kayayyakin bukatun yau da kullum kamar abinci da hakar lafiya.
Ya ce yawan mutanen da suke zaune a sansanonin ’yan gudun hijrar sun ragu daga 13, 804 zuwa 6, 914, sun koma garuruwansu, sakamakon samun zaman lafiya da aka yi.
Ya ce gwamnati ta yi kwamitin mutum 12 wanda zai kula da rarraba kayayyakin rage radadi a sansanonin da ke jihar.
Alhaji Sani, ya ce duk da wadansu sun koma gidajensu gwamnati za ta binciko su ta taimaka musu da ababen more rayuwa.
Ya ce “Wadannan kayayyaki da za a raba, sun zo ne daga Gwamnatin Tarayya da kuma ta jiha sai kuma daidaikun mutane da suke taimaka.
“Kwamitocin da muka yi sun hada da duk hakimi da dagacin da aka samu wannan matsala a yankinsa da dan majalisar jiha da kuma jimi’i daga karamar hukuma.”
Baiwar aure a sansanin gudun hijira
Ramma, daya ce daga cikin ’yan gudun hijirar da suka koma gida watan jiya, ta ce komawar da ta yi wata baiwa ce ta musamman, sakamakon aure da ta sake yi a lokacin da take sansanin.
Ramma, wacce ta fito daga wani kauye a Batsari sun hadu da sabon mijinta mai suna Kabi, kuma an daura musu aure ranar 7 ga Yuni a fadar Hakimin Batsari.
Ango da amaryar suna cike da farin ciki. Sannan an shirya musu kwarya-kwaryar walima a sansanin da ke Batsari.