‘Hajara da kishiyar Uwa’

Barkanmu da sabuwar shekara Manyan gobe. Yaya hutu? Tare da fatan ana lafiya. A  yau na kawo muku labarin ‘Hajara da kishiyar Uwa.’ Labarin ya kunshi yadda duk wani mugu ba ya cin nasara a rayuwa. A sha karatu lafiya.Taku: Amina Abdullahi. Akwai wani mutum yana da mata biyu. Matarsa ta fari tana da ’ya […]

‘Hajara da kishiyar Uwa’
‘Hajara da kishiyar Uwa’

Barkanmu da sabuwar shekara Manyan gobe. Yaya hutu? Tare da fatan ana lafiya. A  yau na kawo muku labarin ‘Hajara da kishiyar Uwa.’ Labarin ya kunshi yadda duk wani mugu ba ya cin nasara a rayuwa. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi.

Akwai wani mutum yana da mata biyu. Matarsa ta fari tana da ’ya daya mai suna Hajara. dayar kuma na da ’ya’ya uku. Ran nan sai mahaifiyar Hajara ta kama rashin lafiya. Ganin yadda ta wahala ya sa ta bai wa kishiyarta amanar Hajara daga nan ta rasu.
Tun rasuwar mahaifiyar Hajara, ta rasa gata da kula. Ran nan kawar Hajara za ta yi aure ga shi ba ta da kayan sawa. Sai ta roki kishir mahaifiyarta da ta ba ta aron kaya.
Kishiyar ta ce za ta ba ta amma da sharadi. Sharadin shi ne kada ta yarda kayan su yi dauda. Hajara ta yarda.
Da ta isa wurin biki ana cikin cin abinci sai miya ta zuba a kayan. Da ta dawo gida sai kishiyar uwarta ta yi mata duka ta ce ta je ta wanke a rafi. Sai ta hadu da kura ta ce me ya same ta, ta gaya mata sai ta wanke ta busar sannan ta ba ta.
Mahaifin Hajara na son ta sosai hakan ya sa kishiyar ta tsane ta. Ran nan sai Hajara na barci sai kishiyar uwar ta jefe ta a rijiya.
Washegari aka shiga nemanta ba a ganta ba. Wani tsoho ya ceci Hajara ya kai ta gidansa. Da ta farfado, sai ta fadi yadda abubuwa suka faru. Sai ta koma gida mahaifinta da ya samu labari ya yi wa kishiyar uwar duka kafin ya sake ta.