Hajara Umar Sanda: Farko a fafutukar fadada ilimin sadarwa

Dokta Hajara Umar Sanda ce mace ta farko da ta yi digiri na uku a fannin sadarwa a BUK

Hajara Umar Sanda: Farko a fafutukar fadada ilimin sadarwa

Dokta Hajara Umar Sanda

Dokta Hajara Umar Sanda ce mace ta farko da ta yi digiri na uku a fannin Nazarin Yada Labarai a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).

Bayan haka kuma, ita ce mace ta farko da ta zama Mataimakiyar Farfesa ce (wato Associate Professor a Turance) a Tsangayar Yada Labarai ta Jami’ar.

Sannan akwai yiwuwar ta zama mace ta farko da za a kira Farfesar Yada Labarai a Jami’ar ta Bayero.

Hajara Umar Sande ta yi bincike da dama a harkar yada labarai da hulda da jama’a.

Littattafai da makaloli

Baya ga littattafan da ta rubuta guda biyu, Tauraruwar tamu takuma rubuta makaloli da dama, ko dai ita kadai ko kuma ta hanyar hadin gwiwa, wadanda aka wallafa a mujallun ilimi a ciki da wajen Najeriya.

Bayan wadannan kuma, ta rubuta babi a wasu littattafan na ilimi wadanda aka wallafa a sassa daban-daban na duniya.

A wani bangare na yunkurinta na fadada ilimin yada labarai, Dokta Hajara umar Sanda ta kuma halarci tarurrukan ilimi da dama inda ta gabatar da makala ko ta yi tsokaci.

Sannan ta duba makalar karshe ta dalibai masu digiri na farko da dama da wasu kuma na masu digiri na biyu.
Sannan ta yi aikin duba makalar dalibai a wasu jami’o’in a matsayin external examiner.

Ayyukan al’umma

Tauraruwar tamu ta rike mukamai da dama a Jami’ar Bayero, na jam’i da na sashe, wadanda suka hada da Mataimakiyar Shugaban Sashen Kula da Jin Dadin Dalibai, da Shugabar Kwamitin Hukumar Jami’a Mai Sauraron Korafin Dalibai da Shugabar Sashen Yada Labarai, da sauransu.

Dokta Hajara Umar Sanda mamba ce a kungiyoyin masana da dama, wadanda suka hada da Kungiyar Jami’an Hulda da Jama’a ta Kasa (NIPR), da Majalisar Malaman Sadarwa ta Afirka (ACCE), da Kungiyar Masu Bincike a Kan Kafofin Sadarwa ta Duniya da dai sauransu.

Daga cikin mukaman da ta rike don taimakon al’umma kuma akwai Mai Ajiyar Kudi ta gidauniyar Ihsan Scholarship Foundation, da Jami’ar Hulda da Jama’a ta Kungiyar Daliban Fulbright ta Najeriya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos