Hajiya A’isha Ahmed Kaita: Burina in canja rayuwar al’umma
Hajiya A’isha Ahmed Kaita ita ce Shugabar Matan Arewa maso Gabas a tsohuwar jam’iyyar CPC. An haife ta a 13 ga Mayu 1965. Ta yi karatun firamare a Katsina da kuma sakandaren ‘yan mata (GGSS) a Gwandu, sannan ta yi digirin zama lauya. A wanan hirar ta fada wa Zinariya irin kalubalen da ta fuskanta […]
Hajiya A’isha Ahmed Kaita ita ce Shugabar Matan Arewa maso Gabas a tsohuwar jam’iyyar CPC. An haife ta a 13 ga Mayu 1965. Ta yi karatun firamare a Katsina da kuma sakandaren ‘yan mata (GGSS) a Gwandu, sannan ta yi digirin zama lauya. A wanan hirar ta fada wa Zinariya irin kalubalen da ta fuskanta a siyasance:
Tarihina
Sunana Hajiya A’isha Ahmed Kaita, an haife ni 13 ga Mayu, 1965, kuma mahaifiyata Shuwa Arab ce daga Maiduguri, a Jihar Barno. Mahaifina kuma bakatsine ne. Na yi makarantar Gobarau Primary School a Katsina, daga nan muka koma Maiduguri, inda na shiga makarantar Holy Trinity. Bayan na kammala sai na yi sakandaren ‘yan mata (GGSS) a Gwandu. Daga nan kuma sai na yi digirin zama lauya.
Ina jami’a aka yi mini aure, na haifi dana Khalid. A lokacin da nake hidimar kasa, na haifi ‘ya ta Yasira wadda Allah Ya yi mata rasuwa. Amma yanzu dana ya fara aiki bayan ya yi karatun zama injiniya a jami’a. Da aurena ya mutu, sai na fara aiki da hukumar shige da fice (Immigration), inda kuma na yi aiki da hukumar na tsawon shekara 11. Da Janar Muhammadu Buhari ya shiga siyasa sai na bi shi, saboda tun ina karama, nake lura da dabi’unsa wadanda suka hada da rikon amana da son talakawa da kamanta gaskiya da kyawawan al’adunsa da kuma irin kaunar da yake wa kasarsa. Ganinsa da wadanan halayan, sai ya sanya bayan ya shiga siyasa, sai na bar aiki na shiga siyasa don in mara masa baya. Saboda ina da kaunar kasata sosai kuma ina son ganin canji. A lokacin da nake karama, littattafai da kudin makaranta duk kyauta ne. Amma yanzu an wayi gari idan kana son danka ya samu ilimi sai ka kai shi makarantar kudi. Babu ta yi yawa a kasar nan.
Abin da ba zan manta da shi ba lokacin da nake karama
Idan kana tuna lokacin da kake karami har zuwa girmanka da kuma jin dadin da ka samu, ai ba za ka so ka girma ba. Saboda ba ka da wani aiki illa zuwa makaranta. Ba zan manta ba, mahaifiyata Allah Ya ji kanta, kullum in zan tafi makaranta, sai ta ba ni madarar peak mai kwakwa, sai ta ce sai na shanye gaba daya. Ta ce idan na shanye zan yi ilimi. Har yanzu ba zan iya manta irin madarar da take ba ni ba, don na shanye gwangwanayen madara masu yawa da ba zan iya ma tuna yawansu ba. Idan ka tuna yadda ka girma cikin kauna da soyayya, sai ka ga ba ka son ka girma.
Wanda na fi shakuwa da shi tsakanin iyaye
Na fi shakuwa da mahaifiyata, ta taimaka mini sosai a rayuwa. Domin da suka rabu da mahaifina sai ta koma Maiduguri ta yi aure, na bi ta can, hakan ne kuma ya sa na saba da al’adunta, yarenta da dabi’unta. Mijinta ya taimaka mini sosai. Yakan kai ni makaranta. Da yake nakan yi shekara biyu ko uku kafin na je Katsina wajen mahaifina, sai ya zamana na shaku da ita sosai.
Abin da na koya a wajen mahaifiyata
Na koyi yadda zan zama mace ta kwarai. Kamar girki, kula da gida da turaren wuta da tsafta da yadda za ki kula da jikinki da yadda za ki yi biyayya ga da namiji, har da yadda za ki zama uwa tagari. Ba wai yabon kai ba, amma haka mu shuwa muke.
kalubalen da na taba fuskanta
Kamar a siyasar da muke yi ma dole ne mutum ya fuskanci kalubale, idan kuka duba siyasar Janar Buhari, za ku ga siyasa ce da babu kudi a cikinta. Siyasa ce ta akida da ra’ayi. Abokan adawar Janar za su iya zuwa su same ka su ba ka cin hanci na misalin miliyan biyu ko uku don ka bar su su ci zabe, suna ganin don ba ka da abin hannu. Irin abubuwa haka sukan faru. Kuma in ba ka da imani da tawakkali sai ka yi abin da bai dace ba. Sannan kuma ga talauci ya yi yawa. Mun ga irin wadannan, amma Alhamdulillahi ina daya daga cikin wadanda na zauna da Buhari tun daga 2002 har yanzu ban taba barinsa ba. Mutane da yawa sun zo kuma sun tafi. Amma mu muna nan daram.
Barazana a harkar siyasa
kwarai na fuskanci barazana a harkar siyasa. Kamar ka ga a Kano nake da zama. A lokacin zabe, akwai ’yan takarar gwamna kamar guda biyu, in kana yin daya kuma ba ka yin daya sai ka ga idan yana da matasa, sai a rika cewa za a zo a kona gidanka. Ba zan manta ba, a zaben shekarar 2011 sai da muka je gidan makwabta muka zauna na tsawon kwana 5. Amma kuma bai kamata mutum ya zamo matsoraci ba a kan barazanar da ake yi. Domin idan ka ga an samu canji, to ba a samunsa cikin ruwan sanyi, dole ne sai ka fuskanci barazana.
Abincin da na fi so
Ina sha’awar tuwo da miyar kuka. Ina kuma son salak irin namu na shuwa, wanda ake yanka ganyayyakin manya, kuma sai a matsa masa lemon tsami da tumatir da gurji.
kasashen da na ziyarta
Na je Saudiyya. Ni da mijina mun zauna a Al-kahira babban birnin kasar Masar (Egypt) na tsawon shekara biyu. Na je Canary island da mijin mahaifiyata da ke Arewacin Afrika.
Kirana ga mata
A koyaushe mace ce karfin gida, saboda a kusan mafiya yawan lokuta maigida yakan fita wurin aiki, saboda haka yana da kyau mace ta tarbiyartar da ‘ya’yanta, ta kuma kare mutuncin mijinta, saboda yadda halinki yake, haka mutane za su fassaraki kuma su kalli mijinki a hakan. Idan kika zama kamila, kika kare mutuncinki, kuma ba ki kasance mai yawan zuwa makwabta ba, dole ne a ce wannan mutumin ya isa da gidansa. Ya kamata mata mu zama a koyaushe muna cikin natsuwa kuma cikin kamun kai, mu zama masu tausayi.
Kira ga mata a bangaren siyasa
Ina son mata su san cewa, irin wannan ra’ayin da ake cewa mata masu siyasa ’yan iska ne, ko karuwai ne, ba haka ba ne. Saboda mafi yawan masu kada kuri’a ai mata ne. Idan har za mu zama mu ne mafiya yawa a wajen kada kuri’a, ya kamata mutane su daina yi mana wani irin kallo. Mata na siyasa ne don su kare mutuncinsu. Idan mata suka kame kansu da kimarsu babu wanda zai kawo musu zancen banza. Ina son mata su kwantar da hankalinsu duk da irin maganganun da ake yi a kansu don suna siyasa.
Irin tufafin da nake sha’awa
Ina son laffaya.
Launi
Ina son launin kore, saboda launin rayuwa ce, domin ko a damina ganyayyakin bishiyoyi na jin dadin rayuwa, sukan canza launi zuwa koraye.
Motsa jiki
Nakan yi zirga-zirga don motsa jiki a lokacin da nake karama. Kuma har yanzu nakan yi don samun karfin jiki.
Abin da nake son a tunani da shi
Ina so a tunani a matsayin macen da ta kawo canji a rayuwar jama’a, musamman ma talakawa. Idan Allah Ya ba mu sa’a muka kafa gwamnati zan yi kokarin kawo canji kan lafiya da ilimi. Wadannan abubuwa biyu ne zaune a zuciyata kamar gyambo. Ina son in ga ana taimaka wa mata masu ciki, saboda da yawansu suna mutuwa domin ba sa iya biyan kudin tiyata. Da yawansu na haihuwa a gida. A matsayina na mace kuma tun da na haihu na san zafin nakuda, ina son kafin na bar duniya na gina gidan marayu. Ko a addinance idan mutum ya taimaka wa maraya, ai ya yi sadakatu-jariya ne.