Hajiya A’isha H. Abdulqadir: Talla jami’ar lalacewar tarbiyyar ’ya’ya ce
Hajiya A’ishatu Hari Abdulkadir, uwa ce mai hankoron ganin ta kare ’yancin mata. Daraktar kudi a Hukumar Majalisar Dokokin Jihar Gombe ce, kafin ta zama darakta ta rike mukamai da dama ciki har da jami’ar kula da kuma tsara kasafin kudi tun Gombe na cikin tsohuwar Jihar Bauchi. Ta bukaci iyaye su ba ‘ya’yansu ilimi […]
Hajiya A’ishatu Hari Abdulkadir, uwa ce mai hankoron ganin ta kare ’yancin mata. Daraktar kudi a Hukumar Majalisar Dokokin Jihar Gombe ce, kafin ta zama darakta ta rike mukamai da dama ciki har da jami’ar kula da kuma tsara kasafin kudi tun Gombe na cikin tsohuwar Jihar Bauchi. Ta bukaci iyaye su ba ‘ya’yansu ilimi na addini da na zamani, sannan ta ce dora wa ‘ya’ya talla kamar shigar da su jami’ar lalacewar tarbiyyarsu ce.
Tarihina
Sunana A’ishatu H. Abdulkadir, ni ’yar gidan sarautar Dukku ce, an haife ni ne a garin Dukku ranar 4 ga watan Afirilu, 1968, kimanin shekaru 45 ke nan. A garin Dukku na girma har aka sanya ni a makarantar firamare a Dukku Central Primary a shekarar 1974 zuwa 1980, sai na tafi sakandaren ‘yan mata ta gwamnati da ke Kuri, wato GGSS Kuri a 1980 zuwa 1982, sai na karasa a sakandaren ‘yan mata ta Bauchi (GGSS Bauchi) daga shekarar 1982 din zuwa 1984. Bayan na gama sai na tafi BACAS (Bauchi Collage of Art and Science) inda na yi karatun share fagen jami’a (IJMB) a 1984 zuwa 1986, sannan sai na tafi Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato, na yi digiri dina na farko a bangaren tattalin arziki (Economics) a 1986 zuwa 1989.
Aiki
Na fara aiki da Gwamnatin Jihar Bauchi a shekarar 1991 a sashin tattalin arziki da kula da kasafin kudi a matsayin jami’ar tsare-tsare a mataki na biyu (Planning officer II Budget and planning Bureau), bayan na shekara uku sai na samu karin girma zuwa jami’ar tsare-tsare a mataki na daya, a bisa ka’idar aikin gwamnati, a haka har lokacin da na kai mataki na goma sha hudu a matsayin mataimakiyar Darakta. Kafin nan ina mataki na goma aka dawo da ni majalisar tsara dokokin Jihar Gombe a lokacin an kirkiro Jihar Gombe a shekarar 1996 a matsayin jami’a mai kula da kasafin kudi na zauren majalisar. A wannan lokaci ina rike da matsayi biyu ne na mataimakiyar darakta da kuma mukaddashiyar daraktar riko a shekara 2009, bayan da aka yi wa Daraktan canjin wajen aiki saboda kwazo, ni kuma na kai mataki na goma sha biyar sai aka kara min girma na koma mataki na sha shida, a lokacin kuma babu gurbin daukar aiki sai aka ce in maye gurbinsa tun da da ma ni ke rike da wajen bayan an kirkiro da Hukumar Zauren Majalisa (wato House of Assembly Commission), shi ne na zama Daraktar kudi da mulki (DAF) a shekarar 2011.
kalubalen aiki
A aikin gwamnati irin na ‘ya mace gaskiya akwai kalubale saboda a kullum duk abin da mace za ta yi, za ta yi iya kokarinta ne don kada a ce ta kasa saboda wasu suna da rauni, ga kuma kula da ‘ya’ya a gida ga aikin ofis, wanda a kodayaushe kokarinta shi ne a ce ta yi sammako ta shirya yara sun tafi makaranta, sannan ta sallami maigida ita ma ta shirya ta tafi wajen aiki ba tare da ta makara ba, ka ga idan ba mace tana da kwazo ba, dole za a ga gazawarta.
Nasara
Duk da cewar akwai kalubale a aikin, akwai kuma nasara domin muddin mace tana da kwazo kuma ta san aikinta dole za ta yi nasara, sannan kuma idan mace ta zama ba ta da nuna bambancin kabila ko addini nan ma za ta ga ci gaba a rayuwarta da wajen aikin ta, ka gan ni tun ina makaranta ban taba sanin mene ne rashin nasara a karatu ba, tun da ban taba samun koma baya ba ballantana a wurin aiki, saboda ban taba wuce shekara uku ban samu karin girma a wajen aikina ba, hakan ne ya sa yanzu har na kai matsayin Darakta a aikin gwamnati.
Yadda na shaku da ‘ya’yana
Na shaku da ‘ya’yana matuka, saboda tun suna kanana nake kai su makaranta da safe fiye da yadda mahaifinsu yake kai su, da zarar na hada musu abincin safe, na yi musu wanka sai makaranta idan suka dawo kuma ina zama da su muna hira, hakan ya sa muka shaku sosai.
Burina
Bayan na yi ritaya ina da burin in huta, tun da duk ‘ya’yana mata ne kuma sun sami tarbiyyar da ta kamata kuma sun yi karatu, zan zauna ne kawai in ci gaba da ibada ina yi musu addu’ar alheri.
Inda na fi shawa’ar zuwa lokacin hutu
Idan na dauki hutuna muna tafiya da maigidana ne dajin Yankari a Jihar Bauchi, wani lokaci mukan je tare da ‘ya’yanmu idan ya zo daidai da hutunsu, su ga namun daji da tsuntsaye wani lokaci kuma mukan tafi Abuja ne, amma dai mafi yawan lokuta na fi yin hutuna ne a gida tare da ‘ya’yana, shi ya sa ma suka samu tarbiyya irin wacce uwa take son ‘ya’yanta su samu.
Yawan iyali
Alhamdu lillahi, ina da ‘ya’ya biyar, kuma dukkansu mata ne babu namiji; babbar ta kammala jami’a yanzu haka tana hidimar kasa, wacce ke bi mata tana aji biyu a jami’a; biyu suna matakin sakandare, ‘yar autansu tana firamare aji hudu.
Shawara ga iyaye
Ina ba iyaye shawarar su ba ‘ya’yansu ilimi sosai, saboda ilimi shi ne babban jari da iyaye za su ba ‘ya’ya, har ya yi musu amfani ko da bayan ba su, musammam ma ‘ya mace idan aka ba ta ilimi kamar an ba duk jama’a ne, saboda ita ke da hakkin tarbiyya a gida, yau idan aka ce maka mace ta samu ilimi, to zai yi wahala ka ga a cikin ‘ya’yanta an samu lalatacce. Ilimin kuma ya zama na addini da na zamani, bari in ba da misali da ‘ya’yan da iyayensu suka yi karatu da wadanda ba su yi karatu ba, idan aka duba tarbiyyarsu ba daidai ba ce. Sannan kuma ina kara kiran iyaye da kada su dinga dora wa ‘ya’yansu talla, saboda wajen talla babbar jami’a ce ta lalacewar yara, ko wucewa nake yi idan na ga yarinya da talla nakan nemi iyayenta in gaya musu illar talla ta wajen ba su shawarar cewa gara su nemi aikatau a gidajen mutane ko wanke-wanke ko shara su tsira da mutuncinsu a kan dora wa ‘ya’yansu talla, domin wasu iyayen idan suka dora wa ‘yarsu talla za ka ji sun ce kada ta yarda ta dawo gida da kwashe, fada wa yarinya haka kuwa ashe wani lasisi ne aka ba ta na ta je ta lalace domin idan ta ga za ta koma gida da kayan talla a dake ta, ka ga za ta iya zuwa wajen samari su yi mata juye, ka ga su kuma dole su gaya mata kalma da dole ta yi hakuri da ita, idan ba haka ba kuma ta ci duka da kwashen talla a wajen uwarta.