Hajiya A’ishatu Mbaka: Na shiga siyasa don in kwato ’yancin mata

Hajiya A’ishatu Audu Mbaka ita ce Shugabar Jam’iyyar Labour a Jihar Nasarawa. A tattaunawar da ta yi da wakilinmu a Lafiya ta bayyana dalilin da ya sa ta shiga siyasa gadan-gadan, sannan ta ba mata shawarwarin da za su taimaki rayuwarsu. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Tarihin RayuwataSunana Hajiya A’ishatu Audu Mbaka. An haife ni […]

Hajiya A’ishatu Mbaka: Na shiga siyasa don in kwato ’yancin mata

Hajiya A’ishatu Audu Mbaka ita ce Shugabar Jam’iyyar Labour a Jihar Nasarawa. A tattaunawar da ta yi da wakilinmu a Lafiya ta bayyana dalilin da ya sa ta shiga siyasa gadan-gadan, sannan ta ba mata shawarwarin da za su taimaki rayuwarsu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Tarihin Rayuwata
Sunana Hajiya A’ishatu Audu Mbaka. An haife ni a garin Jos da ke Jihar Filato  a shekarar 1959. Na yi makarantar firamare a Kaduna, inda na yi makarantar sankandare a Zankuwa (Jihar Kaduna). Daga nan na sake dawo wa garin Kaduna, inda na ci gaba da karatuna a makarantar malamai (Teachers College Kaduna). Daga nan na yi makarantar koyon aikin jinya (nurse) a nan Kaduna. Bayan na  kammala ne na fara aiki a matsayin malamar lafiya, har zuwa lokacin da  na yi aure a shekarar 1984, inda bayan wani lokaci ni da maigidana muka koma Legas.  Daga baya maigidana ya ce in bar aiki. A shekarar 1992 ne Allah Ya yi masa rasuwa. Maigidana soja ne inda ya kai matsayin manjo, ana kiran sa Manjo  A.J. Mbaka wanda ya yi hadarin jirgin saman a lokacin mulkin Janar Badamasi Babangida. Bayan mutuwarsa ne na dawo gida nan Jihar Nasarawa ke nan, don mahaifina asalinsa dan jihar nan ne, daga wani kauye da ake kira Bayan-Dutse yake.
Siyasa
Akwai wata rana da nake tafiya zuwa Abuja, sai muka shiga wata mota da wani sanannen dan siyasa mai suna Alasson Gimba. Da za mu sauka sai ya kasance kudin motarsa bai cika ba, sai na cika masa kudin. Daga nan ya tambaye ni wane aiki nake yi. Sai na ce masa da ina aikin unguwarzoma ne kafin rasuwar maigidana. Sai ya sake tambaya ta ko ina harkar siyasa? sai na ce kwarai ina harkar siyasa, kuma ni ’yar jam’iyyar PDP ce. Sai ya ce in zo in shiga Jam’iyyar Labour mu tafi tare. Abu kamar wasa bayan na yi shawara sai na amince, daga nan na koma jam’iyyar Labour don gano cewa jam’iyyar ta jama’a ce, kuma mai daraja da babu wata hayaniya a cikinta. Na shiga  harkar siyasa gadan-gadan saboda ya dace mata irina su rika shiga siyasa ana damawa da su. Don a lokacin na lura babu mata sosai a siyasa. Shi ya sa na shiga in nuna cewa mata ma ba a bar su a baya ba. Kuma don in kwato wa mata ’yancinsu na shiga harkar.
Burina ina karama
Burina in zama malamar makaranta a lokacin da nake karama, amma mahaifina bai amince ba, hakan ya sa na canja ra’ayina. Abin da ya faru shi ne mahaifina ya taba gaya mini cewa, a lokacin da mahaifiyata take dauke da juna biyu, tana nakuda ya taba ziyartarta a wani asibiti, inda wata nas ta mare shi, don kawai yana so ya ga matarsa da ke nakuda. Shi ya sa ya ce, to idan Allah Ya yarda ’yarsa sai ta zama mai aikin asibiti. Dalilin da ya sa na canja ra’ayina ke nan, inda na koyi aikin jinya maimakon malamar makaranta. Kodayake kamar yadda na bayyana maka a baya burina a lokacin shi ne in zama malamar makaranta.
Halayen da na koya a wurin iyayena
A gaskiya da muke tasowa iyayena sun koya mini yadda zan kasance mai dogara da kaina, sannan sun hore ni in kasance mai fadar gaskiya a koyaushe ko za a hallaka ni. Sun gaya mini cewa idan fa ban kasance mai neman na kaina ba, to ba zan samu nasara a duk inda na samu kaina ba. Duk abin da ka ga ya kamata ka yi don ka taimaka wa rayuwarka iyayena sun ce in yi shi da kyau. Kuma sun ce  kada in yarda in cuci wani ko wata a rayuwata. karya da sace-sace duk wadannan munanan dabi’u ne, don haka suka ce in guje su. Wani abu kuma da suka koya mini da ba zan taba mantawa da shi ba, shi ne, idan an aike ka wani wuri, to kada kaki zuwa. Ka je ka kuma dawo ba tare da bata lokaci ba.  Kadan daga cikin abubuwa da dama da iyayena suka koya mini  ke nan, inda har yau ina cin moriyarsu.
kalubale
Ni dai babban abin da zan iya bayyanawa a matsayin kalubalen da na fuskanta a rayuwata shi ne, lokacin da maigidana ya rasu. Ni da ’ya’yana mun sha wahala saboda a lokacin kamar yadda ka sani, idan ba ka da kowa ba mai ba ka, baya ga haka  ’yan uwan miji kowa zai zo ya ce ai dukiyar dan uwansa ce, saboda haka yana da gadonta. A gaskiya hakan ya kasance kalubale don mun dan samu matsaloli sakamakon haka ba zan manta ba. Na biyu kuma shi ne maganar renon yara. Tun da maigidana ya rasu ya zame mini dole in yi renon ’ya’yana ni kadai, wanda ka san hakan babu sauki. Kodayake Hedikwatar Tsaro ta kasar nan ta amince a lokacin cewa za ta biya kudin makarantar ’ya’yanmu da gida da dai sauransu. Amma sai ya kasance ba su cika wannan alkawari ba. Amma da ikon Allah kuma kasancewa Allah Ya yi ni mai kwazo wajen neman abin kaina ne, don haka ’ya’yana babu wanda ya sha wata wahala musamman wajen karatunsu.

Nasarori
A gaskiya ba wai yabon kai ba, amma na cimma nasarori da dama a rayuwata musamman a harkar siyasa. Ka ga a lokacin da na shigo jam’iyyar Labour babu mata sosai cikinta. Na shigo na kuma zama mace ta farko da ta zama Shugabar jam’iyyar a Jihar Nasarawa, kuma sanadiyata mata da dama sun san mahimmancin siyasa, sun kuma shiga jam’iyyar sakamakon wayar musu da kai da nake yi, sannan ina taimaka musu ta hanyoyin da dama. Haka kuma a jam’iyyar ta kasa duk abin da za a yi za a gayyace ni, don sun sani cewa gudunmawar da nake bayarwa, musamman wajen hada kan mata, in kuma jawo ra’ayinsu baki daya zuwa jam’iyyarmu. A ’yan kwanakin nan nema aka gayyace ni zuwa Ilorin, inda wani da ya fito takara karkashin jam’iyyarmu ta Labour bayan mun gama abin da ya kai mu, ya bukace in yi jawabi ga wasu mata don su zabe shi, inda ni kuma na tattauna da su, sannan na jawo ra’ayinsu suka kuma yi alkawarin kada masa kuri’unsu a lokacin zaben.
Halayen da nake so in gani a wajen mata
Ina so mace mai nuna gaskiya da rikon amana a koyaushe. Misali idan za ki tafi wajen siyasa ne ki gaya wa maigidanki gaskiya cewa ga wurin da za ki je. Kada ki yarda mijinki ya same ki da wani irin hali da bai dace ba. Kuma ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira na musamman zuwa ga mata  ’yan uwana da su rika fitowa takarar kujerun siyasa a kasar nan, don a rika yi da su. Kullum idan na ga abin da ke faruwa, inda za ka ga  mata kalilan ne kawai ke fitowa takarar siyasa a kasar nan sai in ji abin yana bata mini rai. Domin mu mata Allah Ya ba mu basira da baiwa, musamman ta shugabanci, amma abin takaici sai mu rika yin watsi da ita. A karshe kuma a fito a zabi duk wani da ya fito takara a jam’iyyar Labour don ita ce kawai za ta iya kwato kasar nan daga halin da ta tsinci kanta yau.