Hajiya A’ishatu Mu’azu: Siyasa makaranta ce
Hajiya A’ishatu Mu’azu ita ce Uwar kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) reshen Jihar Zamfara kuma ita ce Uwar kungiyar Mata ta kasa (NCWS), ’yar siyasa ce, ta rike mukamin shugabar matan jam’iyyar GDM da DPN da ANPP duk a Jihar Zamfara, har zuwa yanzu ana damawa da ita a siyasar kasar nan. Tarihin rayuwataAssalamu […]
Hajiya A’ishatu Mu’azu ita ce Uwar kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) reshen Jihar Zamfara kuma ita ce Uwar kungiyar Mata ta kasa (NCWS), ’yar siyasa ce, ta rike mukamin shugabar matan jam’iyyar GDM da DPN da ANPP duk a Jihar Zamfara, har zuwa yanzu ana damawa da ita a siyasar kasar nan.
Tarihin rayuwata
Assalamu alaikum wa rahamatullah wa barkatuh, da farko dai sunana Hajiya A’ishatu Mu’azu, wadda jama’a suka fi sani da A’i Malu, an haife ni a shekarar 1960 a unguwar Dole da ke titin Ahmadu Bello Way a garin Sakkwato birnin Shehu.
Bayan na fara wayo sai iyayena suka sanya ni a makarantar Allo don in koyi addinin Musulunci, ban yi karatun Boko ba, kasancewar a lokacin ba a ba karatun boko muhimmancin ba, musamman ma idan aka ce ke ’ya mace ce, don haka sai aka sanya ni a makarantar Malam Bakake da ke unguwar dandutsi Gabas a Sakkwato, haka na ci gaba da makarantar allo, inda bayan na fara girma iyayena suka ce za su yi mini aure, ba zan manta ba a lokacin shekarata goma sha uku.
Gwagwarmayar siyasa
Bayan an yi mini aure ina zaune da mijina, zaman amana; zama na mutunci, har muka samu haihuwa, daga nan na shiga harkar siyasa, daga farko kamar in daina, amma sai abokan gwagwarmayar siyasata suka yi mini alluran maganganu, wadanda suka sanya na zabura, sannu a hankali kuma muka yi GDM da DPN da APP har ta koma ANPP, daga nan muka yi CPC, yanzu kuma muna APC, ban taba yin jam’iyyar PDP ba. Hakan zan ci gaba da siyasa har in koma ga Mahaliccina.
Mukamai
Kamar yadda ka tambaye ni cewa ko na taba rike wani mukami a siyasa, kai ma ka san ba za a rasa nono a riga ba, to ganin yadda abubuwa suke ci gaba, kuma kasancewar babu wata matsala tsakanina da abokan tafiya, sannan mutane suna jin dadin zama da ni, musamman yadda suke ba ni shawarwari kuma in yi amfani da su, sai a wancan lokacin aka zabe ni Shugabar Matan Jam’iyyar GDM a Jihar Zamfara, daga baya na sake rike Shugabar Matan Jam’iyyar DPN ta Jihar Zamfara.
Mun ci gaba da gwagwarmayar siyasa, inda a lokacin Marigayi Janar Sani Abaca, aka zabe ni Mataimakiyar Shugabar kungiyar Mata Matasa da ke neman Janar Abaca ya zarce, wadda aka fi sani da suna YEAA.
Bayan Janar Abaca ya rasu har an kirkiro sababbin jam’iyyu ne, sai aka zabe ni Shugabar Matan Jam’iyyar APP ta Jihar Zamfara daga 1998 zuwa 1999, aka sake zaba ta daga 2000 zuwa 2002. Na zama mamba a kwamitin ZASIDEP a lokacin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Ahmad Sani Yariman Bakura, sannan na zama uwar kungiyar NCWS da FOMWAN da JNI duk reshen Jihar Zamfara.
Nasarari
Nasarorin da na samu a rayuwa ai ba su da iyaka, domin duk wanda aka ce ya rabu da iyayensa lafiya ai ya gama samun nasara a rayuwa, kuma duk da irin matsalar da siyasa take da shi har yanzu ban samu matsala da kowa ba, ka ga wannan nasara ce babba, sannan ina zaune da mijina lafiya, kuma duk abin da ake samu a rayuwa na same shi, har yanzu ana gani na da mutunci, babu wanda zai ce ga abin da A’i Malu ta yi masa na rashin mutunci, ko na sharri, sai alheri, to mun gode wa Allah SWT, kuma ga shi da lafiyarmu, ana yi da mu har yanzu.
Baya ga haka na samu nasarar samar wa matasa da dama aikin yi, musamman ma aikin damara, wannan ya kara mini jin dadi, kuma ina alfahari da shi, don abu ne wanda ka zama sanadin samun hanyar cin abincin wani, kuma zan ci gaba da yin haka sai na cim ma lokacina na mutuwa, duk in da na samu damar samar wa wani ko wata aikin yi zan yi haka.
kalubale
Dole a ci karo da kalubale a rayuwa, musamman ma ga mu ’yan siyasa, ka san a siyasa: Ba ka iyawa; ba ka gamawa; ba ka kuma yabawa. Ita haka take, babban takenta ke nan, duk kokarinka sai ka samu wasu suna ganin ba ka yi musu daidai ba, ko ba ka taba yi musu komai ba, wannan kuma ya zama ruwan dare, don an ce idan kana siyasa sai ka gama da abubuwa biyu zuwa uku, wato sai ka yi hakuri, kuma sai kaki ji, kaki gani, kuma duk wanda ya ce ya shiga siyasa, to mutum ya dora dammarar hakuri da hangen nesa, don a halin yanzu ni ban yi tsammanin zan sake shiga halin da na shiga a gidan siyasa nan gaba ba, don haka sai dai in yi godiya.
Iyali
Na yi aure, kuma har yanzu ina da aure, sai dai ka san haihuwa ta Allah ne, sai wanda Ya so Yake ba wa, kuma babu wanda zai tilasta Shi, cikin ikon Allah na haifi namiji mai suna Muhammad Bello, kuma daga baya ya karbi abinSa, sai dai addu’ar Allah Ya jikansa da gafara, amma yanzu akwai ’ya’yan kanwata uku da ta rasu ta bar mini su, daya daga cikinsu har ta yi aure ta samu ’ya’ya hudu.
Abinci
Ni Bahaushiya ce, don haka ina nan rike da al’adarmu ta Hausawa. Ba ni da wani abinci wanda ya wuce wanda na taso na gani a ci a gidanmu, wato tuwo ke nan, babu ruwana da abincinku na zamani, ban ce ba na ci ba, amma na fi son in ci tuwo.
Sutura
Babu wata sutura da nake sa wa, ko nake sha’awa fiye da suturar da mu Hausawa muke sa wa, wato zane da riga da hijabi, sai dai a sauya salon dinki, amma idan ka ce wane launi na fi so, sai in ce maka kore, ya fi kwanta mini.
Shawara ga mata
Shawarata ga mata ita ce, duk abin da za su yi, to su yi hakuri, shi ne abu na farko, idan ba su yi hakuri ba, to ba za su ci nasara ba. Na biyu, su kasance masu biyayya da kamun kai.
Sannan ina ba mata shawara su shiga siyasa, domin makaranta ce, yana da kyawu su yi ta, za su karu da darussan rayuwa masu yawa. Idan mata suka ce ba za su yi siyasa ba, to ba su taimaki kansu da karamar hukumarsu da jiharsu da kuma kasarsu ba, su kuwa mata ’yan siyasa musamman kuma masu aure, ya kamata su dauki aure da muhimmanci, ya zama dole su rike amanar aurensu, kada su ce za su rika tsalle-tsalle, ko su tsallake iyaka, ma’ana kada su yi wasa da aurensu, kada su dauki wani gefe wanda shari’a ba ta yarda da shi ba.
Ga ’yan siyasa marasa aure kuma, to su kasance masu kamun kai, don idan mace ba ta da kamun kai ba za ta yi mutunci a idon mutane ba, kuma su kauce wa duk wani abu na badala, su tuna cewa a kowane lokaci ana iya daukar ransu, su koma ga Ubangiji.
Burina
Burina ai bai wuce idan mutuwa ta riske ni in cika da kalmar Shahada ba, kuma in rabu da mijina da ’yan uwana da dangina da makwabtana lafiya.