Hajiya Aishatu Yakubu: Ilimantar da ’ya’ya mata na da kyau
Hajiya Aishatu Yakubu, tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati ce wacce ta share shekaru 35 tana aiki kafin ta yi ritaya, yanzu kuma ita ceShugabar Mata ta Jam’iyyar PDP ta jihar Gombe. Tarihin rayuwata Sunana Hajiya Aishatu Yakubu, ni ’yar asalin kabilar Tula ce a karamar hukumar Kaltungo a jihar Gombe kuma a Tula aka haife ni a […]
Hajiya Aishatu Yakubu, tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati ce wacce ta
share shekaru 35 tana aiki kafin ta yi ritaya, yanzu kuma ita ce
Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP ta jihar Gombe.
Tarihin rayuwata
Sunana Hajiya Aishatu Yakubu, ni ’yar asalin kabilar Tula ce a karamar hukumar Kaltungo a jihar Gombe kuma a Tula aka haife ni a ranar 9 ga watan Nuwamba 1958, amma na girma ne a unguwar Herwagana. A fadar jihar na yi makarantar firamare ta ‘Central’ da ke Gombe. Da na gama sai na samu tafiya Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnati da ke garin Bauchi,inda na shekara biyar. Ina gamawa sai na fara aiki a ma’aikatar Shari’a .Daga baya na tafi kwas na manyan ma’aikata a ‘Staff Training Centre’da ke Azare .
Aiki
Na fara aiki ne a Ma’aikatar Shari’a ta jihar Bauchi bayan wani lokaci sai na nemi canjin wajen aiki na koma sashen daukan Ma’aikata da Horar da su, daga nan kuma aka tura ni ma’aikatu daban-daban a matsayin Jami’a mai lura da Harkokin Ma’aikata. Daga nan kuma na koma gidan Gwamnatin jihar Bauchi a bangaren shirye-shirye.Na yi shekara goma ina wajen na kuma yi aiki da Gwamnoni daban- daban kama daga na farar hula da suka hada da Alhaji Dahiru Muhammad Deba da Abu Ali da Christ Abutu Garba da Gruf Kyaftin Adisa Raji da kuma Kanal Yana Kalau, kuma dukkansu sun ba ni shaidar yabo.
Bayan an bai wa Gombe jiha sai muka dawo Gombe inda aka tura ni Baitulmalin Gwamnati .Daga baya aka mai da ni Ma’aikatar Aikin Gona, na kuma yi aiki a ma’aikatu da dama a matsayin Jami’a mai lura da Harkokin Ma’aikata kafin na yi ritaya a shekarar 2011.
kalubalen da na fuskanta
A gaskiya na fuskanci kalubale sosai saboda ka san maza ba sa so a ce yau mace na gaba da su balle ma kuma Jami’a mai lura da Harkokin Ma’aikata, wanda mu muke daga mutum ko mu gurfanar da shi a aiki sai dai Allah ya sani ban taba take wani ba, shi ne ma ya sa ka ga na ci gaba har na samu mukamin Shugabar Mata ta PDP bayan na ajiye aiki. Ka ga aikin Jami’a mai lura da Harkokin Ma’aikata din nan ba karamin aiki ba ne ,domin za ka yi ta gwagwarmaya da mutane kala- kala wanda idan ba ka yi hakuri ba sai ka bata aikinka ko ka bata wa wani. Ka ga ko tsayawa na yi a bakin hanya ina jiran abin hawa kafin ka ce meye za ka ga mutane da yawa sun tsaya suna tambaya ta cewa Hajiya ina za ki je, mu je in kai ki mana ba wani abu ya kawo haka ba kuma illa kyautatawa jama’a a lokacin da nake aiki.
Nasara
Aikin da na yi a matsayin Jami’a mai lura da Harkokin Ma’aikata a wurare daban- daban shi ne nasarar samun kujerar Shugabar Matan jam’iyyar PDP da Gwamna ya ba ni.
Lambar yabo
Na samu lambobin yabo masu yawa daga Gwamnonin soji da na farar hula da na yi aiki da su sannan kuma har na yi shekara talatin da biyar ina aiki ban taba samun takardar koke kan na yi laifi ba kuma ba wanda ya taba nuna min yatsa a aiki har na yi ritaya.
Siyasa
Alhamdulillahi bayan na yi ritaya ne sai na ga cewa kullum ina tare da mata shi ne sai na yi tunanin kafa kungiyar da ta kunshi mata muna harkokin yau da kullum. Daga nan sai muka ga ya kamata mu hada da siyasa ganin cewa siyasa abu ne mai kyau bayan kuma ga shi na iya jawo hankulan matan yankin Gombe ta kudu, kuma ina fada a ji,shi ya sa a wannan shekara ta 2011 da dankwambo ya fito takarar siyasa aka saka ni a cikin kwamitin yakin kamfen dinsa, hakan ne ma ya sa da ya zama Gwamna aka dauko ni a ka ba ni Shugabar Matan Jam’iyyar PDP ta jihar Gombe.
Abin da na fi so a tuna ni da shi
Ina son a rika tuna ni a matsayin uwa mai gaskiya mai kuma son ganin an yi gaskiya don ko da ba na duniya zan so a rika cewa matar nan komai nata tana yin sa ne bisa gaskiya.
Tufafin da ya fi burge ni
Kowacce mace in dai tana da mutunci za ta so ta tsare tsiraicinta balle ma kuma a ce ke ‘yar Arewa ce, ka ga ni ban taba fita ba tare da na sanya hijabi ko gyale a jikina ba, bayan na sanya sutura ta mutunci wadda za ta rufe mini ko ina a jikina ko a gida ba na iya zama ban sa suturar kirki ba saboda na saba.
kungiyoyi da kasashe
Ni ce na kafa wata kungiya ta mata ‘yan siyasa na Gombe ta kudu wacce kuma na sa kowacce shiyya ta jihar aka kafa irin ta sannan kuma ina cikin wasu kungiyoyi irin su kungiyar Kwallare ta mata zalla ina kuma kungiyar Ci gaban Matan Yankin Tula da sauransu. Ban taba zuwa kowacce kasa ba a duniya illa kasar Saudiyya.
Yawan iyali
Alhamdulillahi ina da ‘ya’ya shida maza hudu, mata biyu babban yana
aiki a Ma’aikatar Shari’a ta jihar Bauchi daya kuma tana aiki a gidan talabijin na jihar Gombe daya ta yi aure daya kuma yana koyarwa a makarantar sakandare, biyu daga cikinsu suna sakandare ba su gama ba.
Shawara ga iyaye
Karatun ‘ya mace yana da kyau ina mai bai wa iyaye shawara da su ilimantar da ’ya’yansu mata domin bai wa ’ya mace ilimi kamar bai wa al’umma ne gaba daya.
Domin ilimin ’ya mace yana amfanar kowa da kowa saboda ’ya mace ta fi kulawa da iyaye da ’yan uwa .
Ka ga kamar mu a gidanmu mu tara Babanmu ya haifa amma ni kadai ce na yi karatu har zuwa sakandare domin sau da yawa yana cewa da ya san ilimin mace na da amfani da ya sa sauran yayuna da suka yi aure, wanda yana cewa karatun da na yi ne ya sa ni kadai na fi kulawa da shi kafin ya rasu.
Don haka ina mai kiran iyaye da su tsaya su tabbatar da cewar sun ga ’ya’yansu sun sami ilimi na addini da na boko wanda zai taimaka musu wajen tarbiyantar da ’ya’yansu da kuma wajen zaman gidan aure .