Hajiya Alawiyya Kulliya: Burina in kawo ci gaban al’umma

Hajiya Alawiyya Kulliya Mataimakiyar-Darakta ce a Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta kasa (NDE), ta yi digirinta na farko da na biyu  a Jami’ar Bayero da ke Kano,  ta samar wa mata aikin yi, inda ta ce burinta ta kawo ci gaban al’umma. TarihinaSunana Alawiyya Kulliya, bayan na auri Umar Ibrahim, sai ake kirana Alawiyya […]

Hajiya Alawiyya Kulliya: Burina in kawo ci gaban al’umma

Hajiya Alawiyya KulliyaHajiya Alawiyya Kulliya Mataimakiyar-Darakta ce a Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta kasa (NDE), ta yi digirinta na farko da na biyu  a Jami’ar Bayero da ke Kano,  ta samar wa mata aikin yi, inda ta ce burinta ta kawo ci gaban al’umma.

Tarihina
Sunana Alawiyya Kulliya, bayan na auri Umar Ibrahim, sai ake kirana Alawiyya Kulliya-Umar. An haife ni a Kano a 1959. Na yi karatun firamare na a Jarkasa Primary School daga 1966 zuwa 1970. Daga nan sai na je Sakandaren Shekara; makarantar kwana a Kano. A 1972 sai muka koma Dala. Da muka kai aji Hudu a Dala, sai aka ce ba za a fara karatu a makarantar ba a watan Yuni, hakan ya sanya muka yi wata Shida a aji hudu. A watan Yuli muka fara aji Biyar. Abin da ya sa muka kammala karatu a 1976 ke nan. Daga nan sai na je Jami’ar Bayero da ke Kano tun tana  Abdullahi Bayero College (ABC) a karkashin Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Da yawanmu mun shiga da niyyar karatun zama likita, amma makarantar ba ta  fara ba a lokacin, hakan ya sa na karanta Chemistry. Mun gama karatun a 1981, daga nan sai na yi digiri na biyu a Chemistry duk a Jami’ar Bayero din. Muka yi hidimar kasa a Kano a 1983. A 1984 sai na koma Ma’aikatar Ilimi, inda na koyar na tsawon shekara biyu. Na yi digiri na biyu daga 1985 zuwa 1987. Daga nan sai na koma makarantar Kano State Institute for Education na zama Shugabar bangaren koyar da Chemistry. A 1989 sai maigidana ya koma Legas. Yadda na bar Kano ke nan na koma Legas. To tun 1989 ina tare da Hukumar Samar da Ayyukan yi (NDE) a yanzu kuma Mataimakiyar Darakta a Resource Center da ke karkashin NDE.
Yadda muke taimakawa mata a NDE
Kafin na fara aiki a Hukumar NDE ni ce shugabar kungiyar samar wa mata aiki (Women Employment Association).  Mata kawai kungiyar take taimakawa. Mukan koya wa mata aikin hannu kamar koyon dinki da kere-kere da sauransu, domin su samu abin da za su rike kansu da shi. Mukan taimaka wa mata Musulmi da kuma Kirista. In dai ke mace ce mukan taimaka miki wajen koya miki aikin hannu. Kuma Alhamdu lillahi ana samun nasara.
kalubalen da na taba fuskanta a harkar aiki
Samun shugaba daga arewa na da matsala gaskiya. Amma shugaba daga kudancin Najeriya ba su da matsala. Saboda shugaba daga kudu ba zai yi tunanin wai ko ke mace ba ce ko ba mace ba. Zai ba ki damar yin aikinki yadda ya kamata kuma zai biya ki hakkinki yadda ya kamata. Kuma ba zai ce wai don ke matar aure ba ce saboda haka ba zai ba ki aiki ba. Kuma a gaskiya shugabanin da na samu daga kudunci ba su yi mini hakan ba, kuma sun ba ni hakkina daidai gwargwado. Amma shugabanni maza daga arewa daban suke. Sai su kawo wani larura ko wata matsala don tauye maka hakkinka. Hakan ya faru gare ni ba sau daya ko sau biyu ba. Hakan ya sa na zama mataimakiyar Darakta na tsawon shekara 11 kuma na yi jarrabawar da ya kamata na yi samu karin girma har sau 4, kuma duk na ci nasara a kan su don na zama darakta. Amma har yanzu akwai wata matsala ko wani abu don an ki ba ni abin da ya kamata. Abin har ya kai ga na ji komai ya ishe ni, har na ce zan bar aiki. Don abin da bacin rai. Sai Sanata Emodi ta ce ba za a yi haka ba. Kuma ta ce wanda yake miki haka ba shi ya kawo ki aiki nan ba. In ba hakan ba da na dade da barin aikin.
Abin da bazan manta da shi lokacin da nake karama ba
A shekarar 1966 lokacin yakin basasa, kuma lokacin mukan taka a kafa ne daga gida zuwa makaranta a Jarkasa. A lokacin akan haka ramuka don yara su rika buya a ciki. Akan ce mana “in kun ji jiniya, ku shiga rami”.  To har yau mukan tsokani junanmu da in kun ji jiniya, ku shiga rami.
Wanda na fi shakuwa da shi tsakanin  iyaye
Gaskiya da nake karama na fi shakuwa da mahaifiyata. Daga baya shakuwar ta karu sosai, saboda a lokacin da nake karama tsakanin 1964 zuwa 1966 da nake Jar kasa, yawanci ina zaune ne da kakata saboda iyayena sun tafi kasar Masar. Dawowarsu sai na fi shakuwa da mahaifiyata.
Yadda na hadu da maigidana
Mun hadu da maigidana a lokacin bikin kawata. Akwai kawata da muka gama makaranta tare, kamar ‘yan uwa ne da maigidana. Da aka zo yin aurenta, sai maigidana ya je a matsayin abokin mijinta. A nan muka hadu da shi.

Sirrin zaman aure
Kamar yadda nake gaya wa dana, sirrin zaman aure shi ne wanda za a iya sasanta bambancin tsakanin halayen ma’aurata, don idan za a koyi zama da mutum sai an san halinsa. Ba auren da za ka ji komai ya tafi daidai, haka kuma rayuwa ko da ba ka yi aure ba, ba lallai ba ne ka ji komai ya tafi yadda kake so. Ko mutum yana cikin mahaifiyarsa ma baya samun abin da yake so. Samun komai ya tafi daidai shi ne ranar da mutum ya gan shi a Jannatul Firdausi. Sirrin zaman aure shi ne fahimtar halayen juna tsakanin ma’aurata.
Kyauta daga maigidana
Maigidana ma’abucin kyauta ne. Amma kyautar da na fi jin dadinta ita ce, lokacin da ya ba ni kyautar mota. A Ranar muna zaune sai yake cewa wani dan abokinsa ya kawo motoci daga kasar waje, ko a kawo mini in gani? Sai na ce eh. Da aka kawo sai na ce gaskiya motar tana da kyau. Sai ya ce wa yaron zai biya kudin motar. Sai na ce ai motar da tsada ya kuma zai saya? Sai ya ce in an ba ki kina so? Sai na ce eh. Kamar da wasa sai ya ce to ya ba ni. Na ji dadi sosai.
Farin cikin zama uwa
Na haifi ‘yata ta fari lokacin da ina shekara 19, gaskiya na yi farin cikin haihuwarta. Amma lokacin da na haife ta maigidana ba ya kasar. Daga nan  na haifi namiji. Alhamdu lillahi gaskiya abin farin ciki ne ga kowace mata ta ga ta haihu.
Tufafi
Ina sha’awar sanya hijabi domin na fi sakewa a cikinsa.
Motsa jiki
Alhamdu lillahi, nakan motsa jiki, kuma nakan yi hakan ne ta hanyar amfani da treadmill. Na dauki motsa jiki da mahimmanci. Nakan motsa jiki a gidana ne.
Abinci
Ina son shinkafa. Koma yaya aka dafa in dai shinkafa ce to zan ci.
Fahimtata a kan nasara
A wajena nasara dai ita ce ka ga ka taimaka wa wani har ya ci gaba. Idan kana da kudi kamar dangote amma kuma ba ka taimaka wa mutane, to ba zan dauke ka a matsayin wanda ya samu nasara ba. Amma yau in kai almajiri ne a kan titi, kuma za ka iya taimaka wa wani, to zan dauke ka matsayin wanda ya samu nasara.
Wanda nake sha’awar haduwa da shi
Ina sha’awar haduwa da Oprah Winfery, saboda mace ce mai taimakon talakawa. A yau idan na hadu da ita, zan tambaye ta yadda take janyo mutane zuwa wajenta da kuma yadda take taimaka musu.
kasar da na fi sha’awar zuwa hutu
Ina sha’awar zuwa Saudiya. Ko da yake wannan ba hutu ba ne, amma ina sha’war zuwa Saudiya sosai. Saboda a duk ranar da na je Saudiya, nakan ji na kusanci da Ubangijina, a lokaci guda na samu natsuwa.
Burina
Burina a kullum shi ne, Allah Ya dauki raina a lokacin da mutuwa ce ta fi rayuwata alheri.
Abin da nake son ana tunani da shi
Ina son a tunani a matsayin mai taimaka wa mutane don su samu ci gaba.
Shawara ga masu karatu
Shawarar da zan ba su ita ce, ka da su cire tsammani daga rahamar Ubangiji. Kada su manta an ce in da rai da rabo, kuma Allah Ya ce “Inna ma’al usri yusra”  kowane tsanani yana tare da sauki. Kuma ko mai za su yi su san cewa, duniya ba matabbata ba ce akwai ranar kin dillanci.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno