Hajiya Amina Ibrahim BB Faruk: Abubuwa uku suka taimake ni zaman duniya

Hajiya Amina Ibrahim BB Faruk, lauya ce, a yanzu kuma mataimakiyar darakta a hukumar tsare-tsare ta kasa. Ta ce da za ta iya da ta sanya kowa ya yi karatu, ta kuma ce abubuwa uku da ta koya a rayuwa ne suka taimake ta zaman duniya. TarihinaAssalamu alaikum, sunana Hajiya Amina Ibrahim BB Faruk, an […]

Hajiya Amina Ibrahim BB Faruk: Abubuwa uku suka taimake ni zaman duniya

Hajiya Amina Ibrahim BB Faruk da ‘ya’yanta da kuma jikanta (na farko daga dama) Hajiya Amina Ibrahim BB Faruk, lauya ce, a yanzu kuma mataimakiyar darakta a hukumar tsare-tsare ta kasa. Ta ce da za ta iya da ta sanya kowa ya yi karatu, ta kuma ce abubuwa uku da ta koya a rayuwa ne suka taimake ta zaman duniya.

Tarihina
Assalamu alaikum, sunana Hajiya Amina Ibrahim BB Faruk, an haife ni a shekarar 1962. Na fara makarantar firamare a Saint Luis Primary School, daga nan na je Shahuci da Shekara, bayan na gama ne na wuce zuwa Saint Luis Secondary School duka a Kano. Daga nan sai na yi Jami’ar Bayero ta Kano, inda na yi karatun lauya, a bangaren Shari’ar Musulunci (Shari’a Law).  Tun kafin na kammala karatun jami’a aka yi mini aure, yanzu shekara talatin da wani abu ke nan, domin an yi mini aure tun ina shekara 17. Bayan na kammala jami’a a lokacin da nake hidimar kasa a Kano na haifi dana na biyu. Daga nan sai muka koma Legas, a nan kuma na shiga makarantar kwarewa a kan aikin lauya (Law School). Bayan na kammala wannan makaranta sai na fara aiki a matsayin lauya. Ana-nan-ana-nan har na yi haihuwa ta uku da ta hudu. Daga nan na fara aiki da NICON Insurance. Bayan shekara sha uku a Legas ne sai muka dawo Abuja aka ci gaba da gwagwarmaya, wanda a yanzu nake aiki a Ma’aikatar Tsare-tsare ta kasa, inda nake matsayin mataimakiyar Darakta a bangaren gudanarwa. Kafin wannan lokacin na yi aiki a Ingila, a ma’aikatar kare hakkin dan Adam, kasancewar ni lauya ce mai kare hakkin dan Adam. A lokacin da nake Ingila kuma na yi digiri na biyu a karatun Lauya, inda na kware wurin kare hakkin mata da sasanta rikice-rikice da sauransu. Bayan na dawo ne sai na fara aiki da hukumar kare hakkin dan Adam, amma ban dade ba na fara aiki da ma’aikatar tsare-tsare ta kasa a Abuja.
kalubale kan aikin lauya
Na yi sa’a domin lokacin da muka taso iyayenmu da sauran kuriciyarsu, don haka komai zan yi sai na tuntube su, kasancewar ba ni da babban aboki sai mahaifina, hakan ya sanya duk wani abu tare muke yi. Shi yake ce mini yi kaza, ko kada ki yi kaza. Don haka da na fada masa ina so na zama lauya, sai ya ba ni goyon baya, ya ce da ma na yi kama da su. Mahaifina da kuma Bashir dalhatu da Mai Shari’a dahiru Mustapha ne suka karfafa mini gwiwa har na zama lauya. Kodayake kafin lokacin na so na karanta Turanci da Arabic ne, amma wata rana mun je gidan Bashir dalhatu da yake matarsa yarmu ce, sai ya tambaye ni me nake so na karanta sai na ce masa Turanci, sai ya ce bari ya fada mini wani abu, zan iya samun digiri biyu idan na zama lauya, ma’ana zan iya turanci kuma na zama lauya. Wani ilimi da na gano bayan na kammala karatun lauya a bangare shari’ar musulunci shi ne, babu wata shari’a a duniya da ta ba mata ‘yancinsu kamar shari’ar musulunci.    
Taimaka wa mata ta bangaren aikin lauya
Da a ce na dade a bangaren aikin lauya da bangaren mata zan fi mayar da hankali, wannan aiki irin na NGO ne, don haka zai yi wuya wanda yake aikin gwamnati kamar ni ya yi shi. Amma sau da yawa mata kan zo wurina su rika tambayata mene ne hakkinsu a wurin kaza da kaza, ni kuma nakan fada musu. Wasu kuma kan sanar da ni sun samu kansu a matsala kaza, don haka me ya kamata su yi, ni kuma sai na yi musu bayani.
Abin da ba zan manta da shi ba lokacin da nake karama
Na taso cikin farin ciki ne, mahaifinmu mutum ne mai jama’a, kuma da ma na fada muku shi ne babban abokina, don haka mukan zauna da shi a yi ta hira, shi ya koya mana tafa-tafa da cankuloto-kuloto da sauransu, kasancewar ba ya bari mu fita waje, kofar gidanmu akwai kyandir inda yara kan taru su yi ya gada da sauran wake-wake, amma ba zai barmu mu fita ba, haka za mu rika jin wake-wakensu. Sannan kuma idan ya fita aiki to mun san yawancin lokutan da yake dawowa, daga lokacin ya yi sai mu yi layi, domin bai taba dawowa gida ba tare da wani abu da zai ba mu ba.
Nasarata a rayuwa
Babu wata nasara a wurina face idan na kalli yadda rayuwata ta rika gudana, iyayena sun yi mini gata, sun jajirce wajen ganin na yi karatu, sun kuma yi mini kyakkyawar tarbiyya, mahaifiyarmu ba ta yi karatun boko ba, amma ta jajirce sai da muka yi, wani lokaci za ta tsaya a kanmu sai mun yi jinga, koda ba za ta iya karantawa ba dai sai mun nuna mata. Bayan wannan aka yi mini aure da wuri, shi ya sa duk da na yi karatu ban yarda wai kada a yi auren wuri ba, domin auren wuri gata ne. Na yi aure kuma na ci gaba da karatuna. Allah Ya azurtani da ‘ya’ya hudu, maza biyu, mata biyu, wannan ma nasara ce. ‘Yar autata shekararta 21. Ina da jikoki biyu.

Abin da nake so a tuna ni da shi
Manzon Allah (SAW) ya ce mutumin da ya fi kowa a duniya shi ne wanda jama’a suke amfana da shi, don haka burina bayan na mutu na bar wani abu da jama’a za su rika amfana da shi, ba wai kuma don a fada ba, a’a, na yi don Allah kuma jama’a su amfana da shi. Idan ka raini ‘ya’yanka suka zama mutane ai za su amfani jama’a, to alhamdu lillahi, na raini ‘ya’yana, sun yi karatu wasu sun yi aure, ba su yi yawace-yawacen banza ba, babu mai shaye-shaye ko yin abubuwan zamani da ke damun mutane. Kun ga su ma za su amfani jama’a, ta hanyar tarbiyyantar da nasu ‘ya’yan, da haka sai ka ga al’umma ta zama tagari.  Mahaifina ya fada mini abubuwa uku a rayuwa. Ya ce duk abin da nake so in zama a duniya zan iya zama idan na kiyaye su, na farko, kada na saba wa Allah, na biyu kada na cuci wani, na uku kuma kada na cuci kaina. Wadannan abubuwa uku kullum suna raina, komai zan yi sai ya zamana ina tunawa da su, sun kuma taimake ni a zaman duniya.
Shawara ga mata
Shawarata ga mata musamman masu aure ita ce- su ne za su samar da ginshikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidansu. Don haka ina shawartar mata su guji roko, wato ba-ni-ba-ni, kada su zauna a gidan miji ba tare da aikin komai ba, ma’ana su rika sana’a ko da a cikin gidanta ne. Na biyu su guji bincike domin kazantar da idonka bai gani ba tsafta ce a tare da kai. Matan yanzu kan yawaita binciken miji, walau wayarsa, ko kuma su rika bibiyar ina yake zuwa, duk wadannan ba su dace ba. Na uku ya kamata ko da mace ba ta magana to ta rika tattaunawa da mijinta hakan zai kawo fahimtar juna, ta fahimci miji abokinta ne, ba wai ta zo gidansa ta yi bauta ba ne.
Shawara ga masu karatu
Da zan iya da na tilasta wa kowa ya yi karatu, na addini ne ko na zamani. Kowane addini ya jaddada a yi karatu, ga Musulunci kuwa abu na farko da aka umarci Manzon Allah (SAW) shi ne ya yi karatu, don haka da karatu ba shi da muhimmanci da Allah Bai umarci manzonSa da yi ba. A fahimta ko shara mutum zai yi idan ya yi karatun sharar to za ku ga sharar ta yi kyawu, kuma ba za a hada ta da wanda bai karance ta ba.
kasashen da ta ziyarta
Na ziyarci kasashe da dama ciki har Koriya da Singapore da Brazil da Amurka da Birtaniya da Austireliya da Dubai da sauransu, wadansu kasashen aiki ne ya kai ni, wani lokaci kuma ni da yara muka je hutu, wani lokaci kuma ni da ‘ya’yan mu bi mahaifinsu wurin aiki, da dai sauransu, amma babu kasar da na fi son zuwa kamar Saudiyya (Makka) idan ina can hankalina yakan kwanta.   
Abinci
Na fi son kunun kanwa, ga bangaren abin ci kuma babu wani abu da zan ce na fi so, domin ni ba ma’abociyar ciye-ciye ba ce.
Tufafi
Na fi son kayanmu na gargajiya, da zan iya da na hana mata sanya tufafin da ba namu ba.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya