Hajiya Amina Muhammad Baba: Sannu ba ta hana zuwa…

Hajiya Amina Muhammad, shahararriyar ’yar kasuwa ce da ke zaune a garin Filato. Harkokin kasuwancinta ya bunkasa inda a halin yanzu kasa daidai ce wacce ba ta kai ziyara ba saboda harkar kasuwanci. Aminiya ta samun zantawa da ita inda ta bayyana fadi-tashin da ta sha kafin ta kawo yanzu, ma’ana kalubalen da ta fuskanta […]

Hajiya Amina Muhammad Baba: Sannu ba ta hana zuwa…
Hajiya Amina Muhammad Baba: Sannu ba ta hana zuwa…

Hajiya Amina Muhammad, shahararriyar ’yar kasuwa ce da ke zaune a garin Filato. Harkokin kasuwancinta ya bunkasa inda a halin yanzu kasa daidai ce wacce ba ta kai ziyara ba saboda harkar kasuwanci. Aminiya ta samun zantawa da ita inda ta bayyana fadi-tashin da ta sha kafin ta kawo yanzu, ma’ana kalubalen da ta fuskanta da kuma irin nasarorin da ta samu da kuma shawarwarin da ta bai wa mata. A biyo mu sannu a hankali don a sha kara

Tarinhi:

Sunana Hajiya Amina Muhammadu Baba. An haife ni ne a garin Filato. Na yi karamar makaranta da babbar makaranta a Al-iman a garin Jos, kuma na yi karatun Jami’a a Abubakar Tafawa balewa (ATBU) da ke Bauchi. Bayan na yi auren ne sai muka dawo Abuja. Na fara aiki a banki, amma kin san yanda halin rayuwa take maigida na ya fara kukan cewa aikin ya sa ba na ba shi kulawar da ta dace da dai sauran su. Ta dalilin wannan ne ya sa na bar aikin banki. Bayan na bar aikin bankin ne sai na fara tunanin abin da zan yi a matsayin sana’a. Sai na ce a zuciyata me ya sa ba zan samu sana’ar da zan rika yi ba ko da kuwa a gida ne. Daga nan sai na fara sayen kayayyakin kwalliya irin na mata. Wani lokacin sai in zuba a cikin motata ina kaiwa ma’aika ma’aikata ina sayarwa. har ya zuwa lokacin da maigidana ya ga cewa wahalar ta yi yawa, sai yac e da ni me ya sa ba zan mu samu dan shago ba don na rika yin kasuwancin a ciki? Sai kuwa na ga lallai ai hakan ya fi. Da na samu shago sai na ga yakamata a ce na hada da wani abu. To a unguwar Jabi da ke Abuja sai na bude wurin yin gyaran gashin irin na matan Musulmi. Na dauki ma’aikata a wannan fanni kuma duk musulmai. Alal hakika dai na kafa wannan wurin ne saboda matan mu Hausawa amma sai na ga ba su ciki zuwa don a yi musu gyaran gashi ba, sai na daina. Da na sake budewa ne sai na mayar da abikin na kowa da kowa, ma’ana na Musulmi da na Kirista da ma wanda ba ta da addini. Da tafiya ta yi nisa ne sai na sake bude wani shago a Garki II da ke Abuja. A nan dai tafiya ta yi tafiya, har muka gina namu gidan a Trade more Estate a Abuja. Sai na ga su ma suna da bukatar irin wadannan abubuwan sai na bude wani wuri na kara daukar ma’aikata kimanin goma sha shida wadanda nake biya duk karshen wata sannan ni ke biyan kudin hayan da suke biya a wuraren da suke zaune. To kin ji kadan daga cikin tarihina.

Me ya ba ki sha’awar tsunduma cikin irin wannan sana’a?
Farko abin da na yi tunani a kai shi ne kamar mu mata mun dauka in banda aikin ofis babu wata sana’a da za mu iya yi. Don haka ne na yanke shawarar nuna wa mata cewa ba wai sai aikin ofis kadai mace za ta iya yi ba, ko a cikin gidanta na aure za ta iya yinm sana’ar da za ta rufawa kanta da na iyalinta asiri amma ganin yadda mata muka bar wa mazajenmu duk wata dawainiya, a ce mace ta zauna ba ta sana’ar komai sai zaman banza bai dace ba. Mu sani fa rayuwa ta canza, abin ya zama cudeni- in- cudeka ne. Gara a ce mace tana wata sana’a da haka ne za ku iya rufa wa junanku asiri, koda wani abu ya faru zan iya rike kaina da ‘ya‘ya na ba tare da mun tagayyara ba.

Ko za ki iya gaya mana dalilin da ya sa wasu matan ba sa son yin sana’a?
Ya dangantaka. Wani lokoci mazan ne ke hana matan

nasu yin wata sana’a. Don haka ina kira ga ire-iren wadanan mazajen da su daina yin haka, su yi la’akari da abubuwa da dama. Yin sana’ar mace ba karamin taimako zai iya yi ga iyalai ba. Saboda halin rayuwa komai na iya faruwa. Ta bangaren mu mata, wasu don son jiki ba sa iya yin komai, sai dai su ci su kwanta kawai. Wasu matan ma mazajen kan ba su jari don su yi sana’a amma sai su cinye. Sana’a ba ta tafiya a kan haka, sana’a kamar yaro take renonta ake yi, har ta kai wani matsayin da za ki ji dadi. Amma abin bakin ciki shi ne wasu matan kan cinye jarin da aka ba su kuma su koma su zuba wa maigida ido.

Mene ne burinki a rayuwa?
Burina a rayuwa nan gaba shi ne na ga na bude wurin da zan rika tara mata don koya musu abubuwa da dama, musamman wanda ya shafi yin girke-girke da gyaran jiki da dai sauransu kyauta. Don na ga yawanci mun fi samun matsala ta wannan bangaren. Yanzu haka ina yin haka sannu a hankali. Na fara ne da ma’aikata biyu amma yanzu sun ka goma sha hudu. Daga cikin 14 akalla rabi da ciki suna zaune da mu ne a matsayin dindindin inda muka kama masu gidajen haya a wurare daban-daban. Idan sun kware, su ma za su koyar da wasu, da haka abin zai bunkasa.

Me ya fi bata miki rai?
A gaskiya abin da yafi ci min tuwo a kwarya shi ne karya. Ba na son rashin gaskiya. Idan na gane mutum haka yake to wallahi ba za mu taba jituwa ba.

Da yake na ga kina da son taimakon jama’a wadanne irin gudummawa kike ba ma’aikatanki?
A yi gaskiya. Kuma, nan gaba kadan ina son in bude gidan marayu na Musulunci, don na rika taimakawa marasa gata, in Allah ya yarda.

Wane shawara gareki kan yanda mata zasu iya bada nasu gudummawa wajen gyara al’umma?
Lallai mata su ne tushen komai, abin yana fara wa da tarbiyar ya’ya tun suna kanana, idan sun samu kyakkyawar tarbiyya za su tashi da ita. Don haka ina shawartar mata mu bar zaman yin gulma. A kira tashi ana tsaftace gida da kuma kula da yara. Mata su cigaba da tunanin yadda za su taimaki kansu da kuma taimakawa iyali da al’umma baki daya.