Hajiya Amina Zakari:Hakuri maganin zaman duniya

Hajiya Amina Bala Zakari kwararriyar mai hada magunguna ce wadda ta yi aiki a asibitoci daban-daban na kasar nan. Kuma  ta yi aikin bayar da shawara a kan harkokin lafiya da zamantakewa.Ta rike mukamai daban-daban a Gwamnatin Tarayya.A yanzu  kuma ita ce Kwamishinar Zabe ta kasa. Sunana Amina Bala Zakari,ni ’yar asalin Jihar jigawa ce, […]

Hajiya Amina Zakari:Hakuri maganin zaman duniya

Hajiya Amina Bala Zakari kwararriyar mai hada magunguna ce wadda ta yi aiki a asibitoci daban-daban na kasar nan. Kuma  ta yi aikin bayar da shawara a kan harkokin lafiya da zamantakewa.Ta rike mukamai daban-daban a Gwamnatin Tarayya.A yanzu  kuma ita ce Kwamishinar Zabe ta kasa.

Sunana Amina Bala Zakari,ni ’yar asalin Jihar jigawa ce, mahaifina shi ne marigayi Sarkin Kazaure Alhaji Usaini Adamu. An haife ni a Ingila a shekarar 1960 kafin a samu ’yancin kai. Na fara makarantar firamare a Jihar Kaduna daga nan na wuce makarantar firamare ta kwana ta Shekara wadda take a jihar Kano inda na karasa karatun firamare.Daga nan sai na tafi makarantar sakandare ta keens Collage,Yaba da ke jihar Legas.Daga nan sai na tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na yi karatun digiri a fannin hada magunguna,na gama a shekarar 1980.

Bayan na gama na fara aiki a asibitin Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano a bangaren bayar da magani .Na yi irin wannan aiki a Sakkwato da Kaduna saboda yanayin aikin maigadana akwai tafiye-tafiye. Daga baya ma sai muka fita kasar waje, a nan na samu tangarda babu aiki. Amma da na dawo sai na samu aiki a Asusun Rarar Man fetur(PTF).Na kasance mai ba da shawara wajen sarrafa hidimomin sayan magunguna da yadda ake rarraba su da yadda ya kamata a yi amfani da su. Bayan wannan kuma sai siyasa ta shigo aikin ya kare .Sai na koma aikin bayar da shawara ta fannin lafiya da yanayin zamantakewa, idan na yi kamar wata uku sai a biya ni kudina, in dawo gida in zauna.Ina haka ne ma har Allah Ya yi wa maigidana rasuwa.Na fara kula da yara.
A shekarar 2004 sai aka dauke ni aiki a Gwamnatin Tarayya a matsayin kamar kwamishina ta Lafiya lokacin Malam Nasiru El- Rufa’i. Sai dai ba a kiranmu da Kwamishina sai dai a ce Sakatare.Daga nan kuma sai aka tura ni Ma’aikatar kula da gajiyayyu da wasanni, haka kuma na rike Ma’aikatar Noma. Haka na yi wannan aiki har zuwa shekarar 2007 wato karshen wannan gwamnati.Bayan na gama wannan aiki, sai na koma aikina na bayar da shawara ana kirana in yi, bayan na gama a ba ni kudina in tafi. Na yi aiki da wata ma’aikata da ake kira Songhai Medical Centre da Songhai Insurance.Daga nan sai na samu aiki a hukumar zabe ta kasa wato INEC inda aka ba ni Kwamishinar zabe. Mun yi wannan aiki na tsawon shekara biyar, mun yi zaben 2011, kuma mun yi na wannan shekarar 2015, kuma cikin ikon Allah a wannan shekarar aikin zai kare shi ma.
Abin da nake jin dadinsa a aiki
Ni ina son aiki matuka don haka ina jin dadinsa. Kowane aiki aka ba ni zan yi bakin kokarina in ga na yi yadda ake bukata,ko ban iya ba zan je in koyi yadda ake yi. Ina son aiki don haka koda yaushe a cikin aiki nake.Kuma a matsayina na mace idan na tsunduma cikin aiki sai na gama ba na ganin wani rauni wai ni mace ce.
Abin da ba zan mata da shi ba
Akwai wani lokaci ina aiki a ma’aikatar lafiya ta Abuja, sai likitoci suka hade baki suka tsunduma cikin yajin aiki, na tsawon sati uku. Bayan an biya musu duk bukatunsu sai suka ki janyewa. Suka ki gaba suka ki baya. Sai wasu suke zargin ko saboda ni ba likita ba ce kuma ina shugabantar ma’aikatar lafiya su kuma sun fi so a bai wa likita dan uwansu wannan mukami. Amma ni ban dauka haka ba ne. Domin kuwa har su ma masu hada magunguna sun shiga wannan yajin aikin, amma muka rasa manufar yajin aikin. Haka aka yi ta yi har dai daga baya Gwamnan Edo na yanzu Adams Oshomole ya zo ya warware rigimar ,ya ba mu gaskiya. Daga nan ne sai Malam Nasiru El-Rufai ya ce in bar wannan ma’aikata in koma ma’aikatar gajiyayyu da wasanni. Na ji dadin aiki a gurin domin babu matsi kuma mun taimaki mutane har da marayu da sauransu, kuma mun yi gyare-gyare da dama a gurin.
Burina ina karama
Mun tashi a gidanmu mun ga ana ilimi, har iyayenmu mata daga fada, abin alfahari, suna neman ilimi kuma suna aiki, kannen iyayenmu da yayyensu duk suna neman ilimi. Domin akwai yayar mahaifiyata wajen shekararta 82 amma tana Turanci har yanzu tana rubuce-rubuce a dakinta, mutane suna mamaki.Abokan aikina idan sun je sai ta yi ta buga musu Turanci tana karanta musu abubuwa. Saboda haka mun tashi a cikin ilimi, na san dole ne in yi ilimi, kuma dole in yi amfani da shi. Saboda na ga ana amfani da shi a gidanmu.
Kuma mahaifinmu ya kasance jigo a gurin inganta ilimin mata. Domin lokacin Gwamna Audu Bako shi ne Babban Sakatare na ma’aikatar ilimi. Su ne suke bayar da mota a je kauyukan Kano a debo ’yan mata, wasu ma da kwanukan tallansu a saka su a makaranta.Wasu yanzu alkalai ne da likitoci da sauransu.Saboda haka ni na tsinci kaina a karatu.
Wani lokacin muna sakandare aji hudu wadansu masu bayar da shawara a kan abin da mutum yake so ya zama bayan ya gama karatu sun zo makarantarmu, daga nan sai na ga ina ra’ayin karatun fannin hada magunguna. Masu bayar da tallafin karatu suka ce lallai sai in yi karatun likita, ko su hana ni tallafin karatun, kuma lokacin Babana ne shugabansu. Sai na ce idan sun hana ni zan je gida in yi ta kuka iyayena su biya min domin ni fannin hada magunguna nake so in karanta .
Abin da na koya a wurin iyaye
Na koyi girmama dan Adam komai kankantarsa. Kuma babu nuna bambanci na addini ko kabila ko siyasa duk daya muke, haka iyayenmu suka koya mana.Alhamdulillahi ko a wajen aiki za a yi mana wannan shedar. Kuma mun koyi neman ilimi da ilimantarwa. Don haka ko a titi muka ga ba ka yi dai-dai ba, za mu tsayar da kai mu fadakar da kai. Amma mutanen zamani ba sa son haka, sai dai muna iyakar kokarimu.
Mutanen da nake koyi da su
Ina koyi da marigayi Salihijo Ahmad wanda ya shugabance mu a lokaci aikin PTF. Akwai Malam Nasiru El-Rufa’i da kuma Farfesa Jega duk mutane ne masu hazaka. Idan an ba su aiki babu wasa.Akwai kuma baiwar Allah Obi Ezekwesili ita ma mace ce mai kamar maza kuma tana da son taimakon Najeriya. Akwai yayata Hajiya Rabi Ishak ita ma abar koyi ce mai kyau a wurin mata.

 

Hada aiki da kula da gida
Ban samu wata matsala ba,domin a lokacin rayuwa babu rudani, muna samun dattijawa masu kula da ’ya’yanmu sosai,kuma akwai ’yan’uwa. Ba kamar yanzu ba da ake barin yara a hannun ’yan mata . Kuma iyayenmu suna taimaka mana domin mazajenmu suna da fahimta sosai.Saboda haka gaskiya yara ba su hana ni aiki ba.Kuma bayan sun girma sun fahimci yanayin aikina.
Yadda nake hutawa
Ina da huta kuwa? Gaskiya ni mai yawan baki ce, gidana koda yaushe za ki ji ana cewa “Salamu alaikum”.Saboda haka ba zan ce ina hutawa ba.Amma wata kila sau daya a wata idan na ji shiru zan kwanta in karanta jarida, to shi ne hutuna.Sai kuma da safe zan yi kokari in tashi da sassafe, ina shan shayi ina kallon talabijin awa daya zuwa biyu, sai kuma in tafi ofis, ko ina da bakin nakan yi kokari in samu wannan dan lokacin.Amma in ba haka ba gaskiya ba ni da wani hutu sai dai godiyar Allah.
Iyali
Maigidana sunansa Bala Zakari Kazaure ya yi aiki shekara 31 a banki,ya rasu a shekarar 2000. ’Ya’yana biyar ,maza hudu mace guda daya.Namiji daya ya yi aure yana da ’ya’ya biyu. Guda uku suna aiki ,daya yana bautar kasa. dan autana kuwa yana makarantar sakandare.
Nasarori
Nasara ta farko, alhamdulillahi na samu na ilimantar da ’ya’yana duk da mahaifinsu ya rasu.
Nasara ta biyu kuma duk inda na je aiki ina tabbatarwa na koya wa wasu ta yadda idan na tafi za su yi begen aiki da ni. Akwai mutane da yawa wadanda tun aikina na da, har yanzu muna tare,muna zumunci.
Nasarar zabe kuwa da muka yi ba tawa ba ce ni kadai.Ta kowa da kowa ce.Mun taimaka mun rufa wa shugabanmu baya mun yi zabe yadda ya kamata.Mun gode Allah an ji dadin zabe,kuma an karbi canje –canjen da muka kawo, kuma an yi cikin nasara da taimakon alumma kuma da taimakon Allah.
kalubale
Rayuwa ai kullum a cikin kalubale take,idan babu kalubale babu rayuwa.Duk wanda rayuwarsa take tafiya tar-tar babu kalubale ya binciki kansa.Duk wannan kalubale jarrabawa ce daga Allah sai dai kullum fatan Allah ya sa mu ci jarrabawar.Hakuri shi ne maganin duk wani kalubale,kuma shi ne maganin zaman duniya.
Darasin da na koya a rayuwa
Darasin da na koya shi ne duk wanda ka hadu da shi kada ka raina shi.Kuma kada ka ji haushin kowa,kuma kada ka wulakanta kowa.Sannan ka rika duban alherin mutum da dabi’unsa kyawawa, kada ka rika duban rashin kirkinsa ko munanan dabi’unsa.
Shawara ga mata
Duk inda kuka samu kanku kada ku dauka mata ne ku, za a tsangwame ku.Ku dage ku yi aikinku tsakaninku da Allah. Da kuma karfin hali da kwazo. Idan ba kwazo, shi ne maza suke raina mu.Amma idan kika nuna musu karfin zuciya to babu wanda zai raina ki.Alhamdulillahi matan Najeriya muna daga cikin matan da ake girmamawa a duniya ta fannin ilimi da jajircewa a wajen aiki.