Hajiya Fatima Widi: Yawaitar mace-macen aure na ci mini-tuwo-a-kwarya

Hajiya Fatima Widi ‘yar jarida ce a Jihar Jigawa. ‘Yar gidan attajiri dan asalin masarautar Hadeja, Jihar Jigawa, Alhaji Widi Jalo wanda ya shahara a Legas, wanda mawaki Shata ya yi wa waka mai taken ‘Widi dan Tijjani’. Ta yi gwagwarmayar rayuwa inda ta koyi sana’ar dinki da girke-girke da sauransu. Babu abin da ya […]

Hajiya Fatima Widi: Yawaitar mace-macen aure na ci mini-tuwo-a-kwarya

Hajiya Fatima Widi ‘yar jarida ce a Jihar Jigawa. ‘Yar gidan attajiri dan asalin masarautar Hadeja, Jihar Jigawa, Alhaji Widi Jalo wanda ya shahara a Legas, wanda mawaki Shata ya yi wa waka mai taken ‘Widi dan Tijjani’. Ta yi gwagwarmayar rayuwa inda ta koyi sana’ar dinki da girke-girke da sauransu. Babu abin da ya fi ci mata tuwo-a-kwarya kamar yawaitar mace-macen aure.

 

Hajiya Fatima WidiTarihina
Assalamu alaikum, sunana Fatima amma ana kirana da Hajojo. An haife ni a garin Legas. Mahaifinmu ya yi fice a harkokin kasuwanci da siyasa. Har yanzu kuma bai daina kasuwanci da siyasa ba, kuma har yanzu yana Legas, a cewarsa ya fi gane zaman can din duk da cewar tsufa ta kama shi.
Asalinmu mutanen ‘Yanleman ne da ke yankin karamar Hukumar Kaugama a cikin masarautar Hadejia da ke Jihar Jigawa. Na yi firamare a Legas, daga nan na yi Kwalejin ‘Yan mata (GTC) a Dala, Jihar Kano, bayan na kammala sai na yi Difloma da Kaduna Poly inda na karanta aikin jarida. Na yi makarantar koyon dinki da girke-girke. Daga nan sai makarantar aikin likita. Daga nan na shiga harkokin kungiyoyi masu zaman kansu (NGO).
Burina
Burina a rayuwata shi ne na ba da gudunmawata wajen raya da bunkasa Jihar Jigawa har ta yi fice; ta kuma ci gaba al’umma su samu abin yi. A rika cewa Jihar Jigawa ce kan gaba, sannan na ga Arewa ta zama kasa daya, kana ina da burin a rika taimaka wa mata har su dogara da kansu. Ina da burin ganin irin sakin da ake yi wa mata ya ragu sosai a Arewa. Hausawa su suka fi kowa sakin matansu, sukan yi saki barkatai.  Yawan sakin auren da ake yi na ba ni takaici, domin idan an sake su ba a kuma daukar nauyinsu ko ‘ya’yan da aka haifa. Haka su ma matan da mazajensu suka mutu su ma ‘yan uwan mazajensu ba sa daukar nauyin ‘ya’yan da aka samu a tsakani. Daga karshe sai ka ga tituna sun cika da mabarata.
Abin da ya fi damuna
Ba na son karya da munafurci. Rashin gaskiya shi ne babban halin da nake kyama a rayuwata. Wadannan halaye su ne suka yi kamari a zukatan mutane, kuma su ne suka lalata zaman duniya a halin yanzu.
Aure
Na taba yin aure har na haifi ‘ya’ya uku kafin Allah Ya kawo rabuwata da mijina. Yanzu haka ba ni da aure kuma har gobe ina da burin na sake yin aure, amma idan na samu miji nagari mai halin kwarai. Wadansu matan ba burinsu auren ba, a’a, suna zuwa wurin mata ne don dukiya ko nasabarsu, wato su yi auren jari. Wasu kuma saboda fasikanci, wasu kuma don wani dalili amma ba wai don Allah ba.
Halayen da na fi so a wurin namiji
Na fi son wanda ya mallaki hankalinsa, ba yaro  karami ba domin yaro bai san darajar aure ba, musamman ma da yawancin matasa suke auren manyan mata don dukiyarsu ba don soyayya tsakani da Allah ba. Amma idan mutum ya manyanta, yana da ilimin addini wanda idan na kauce hanya zai yi mini nasiha cikin taushin harshe bisa kuma sigar da ta dace. Ya ce Allah Ya ce annabi ya ce, ba wanda zai hau dokin zuciya ba, ya rika fushi babu gaira babu dalili. Miji na gari shi ne wan da ba ya so ya ga wani abu ya bata wa matarsa rai. Ya zama mai kishin matarsa da kaunarta da kuma kare mata mutuncinta.

Matsalata
Hajiya Fatima WidiBabu wata matsala da ta fi ci mini tuwo a kwarya kamar yawaitar mace-macen aure. Musamman ma yadda maza suke sakin matansu a kan laifin da bai taka kara ya karya ba. Yawan saki na jefa ‘ya’ya cikin ukuba da ni’yasu a cikin rayuwa, yana jefa yara cikin maraicin dole musamman idan aka samu uba marar sanya idanu a kan harkokin rayuwar ‘ya’yansa.
Sau da yawa kishiyoyi na azabtar da ‘ya’yansu da mahaifiyarsu ba ta gidan musamman idan suna da nasu ‘ya’yan. Na taba fuskantar irin wannan matsalar a lokacin da mahaifiyata ta bar gidanmu ina karama, babu irin  tsangwamar da ban gani ba a wajen matan mahaifina amma da na yi hakuri ga irin sakayyar da Allah Ya yi mini a halin yanzu.
Tarbiyya
Akwai bukatar a yi wa ma’aurata gyaran tarbiyya a kodayaushe domin hakan zai magance matsalar yawaitar mace-macen aure a cikin wannan zamani musamman cikin al’ummar Hausa/Fulani kuma akwai bukatar iyaye su rika yi wa ‘ya’yansu addu’a da nasiha don ganin sun rike aure da mahimmanci.
Tausayi
A kullum ina tausaya wa matan karkara domin sun fi kowa wahala a rayuwa saboda a nan ne miji zai yi wa matarsa ciki sannan ya yi watsi da ita, ya daina damuwa da lafiyarta kuma bai da mu da kai ta asibiti ba; bai damu da sabulun wankanta ba ko man shafawarta ba, an mayar da matan kauyuka burtuntuna, mazaje ba sa kula da lafiyarsu ballantana su saya musu tufafi.
Tafiye-tafiye
Ina da burin in zaga kasashen Afrika don na ga yadda suke, don in tabbatar da maganar da ake fada cewar mu Najeriya mu ne uwar Afirka shin da gaske ne, amma ni kam ina da ja a kan hakan. Ina so na ziyarci Kenya da Kongo don na ga yadda dabbobinsu suke, na kuma ga yanayin al’adunsu.
Shawarata
Ina kira ga mazaje su ji tsoron Allah a cikin harkokinsu na rayuwa, su rika sanya Allah a cikin zuciyarsu, su daina sakin aure barkatai, su kuma mata su yi karatun-ta-natsu wajen daina yi wa mazaje rashin kunya domin sau da dama karancin tarbiyya ne ke jawo mazaje suke sakin mata, kuma akwai bukatar malaman addini su tashi tsaye sosai wajen fadakar da ma’aurata mahimmancin zaman aure tare da irin illolin da shi kansa saki yake haifarwa a lokacin da auren ya mutu. Da fatan wadanda aka yi domin su za su hankalta.

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54