Hajiya Furera Abdullahi: A samar da doka mai tsanani ga masu fyade

Hajiya Furera Abdullahi Baffa Hadejia ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar Jigawa. Ta rike mukamin Shugabar Makarantar Sakandiren Arabiyya ta karamar Hukumar Birniwa da Garki, sannan ta zama Jami’a da ke lura da ilimin mata a karamar Hukumar Hadejia. Ta bayyana takaicinta game da yawaitar yi wa mata kanana fyade. Ta […]

Hajiya Furera Abdullahi: A samar da doka mai tsanani ga masu fyade
Hajiya Furera Abdullahi: A samar da doka mai tsanani ga masu fyade

Hajiya Furera Abdullahi Baffa Hadejia ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar Jigawa. Ta rike mukamin Shugabar Makarantar Sakandiren Arabiyya ta karamar Hukumar Birniwa da Garki, sannan ta zama Jami’a da ke lura da ilimin mata a karamar Hukumar Hadejia. Ta bayyana takaicinta game da yawaitar yi wa mata kanana fyade. Ta bukaci Gwamnatin tarayya da sauran mahukunta su samar da wata doka da za a rika hukunta duk wadda aka samu da laifin yi wa yarinya fyade.

Tarihina   
Assalamu alaikum, sunana Hajiya Furera Abdullahi Baffa, an haife ni a garin Hadejia, wato cikin masarautar Hadejia a 30 ga Afrilu 4, 1963. Na fara makarantar firamare a Hadejia, daga nan mahaifina ya koma Zariya, wato a lokacin yana aiki ne a ma’aikatun gwamnatin tarayya, nan ma ban gama ba aka mayar da da ni makarantar ’yan Mishan da ke Kaduna, wato a can Kakuri ke nan. Daga bisani ya mayar da ni makarantar firamare da ke Shekara, makarantar kwana ce, to a nan na gama. Daga nan na wuce Makarantar ’Yanmata ta Dala da ke Kano. Na kammala sakandire a shekarar 1977.
Daga nan ne na wuce Jami’ar Bayero da ke Kano, inda na yi digiri a kan Tarihi (History). Na yi hidimar kasa a Makarantar ’Yan Mata (WTC), inda na fara aikin koyarwa. Bayan na kammala sai aka dauke ni aiki a makarantar, inda na koyar daga 1982 zuwa 1987. Daga nan aka mayar da ni Makarantar ’Yan Mata ta Birniwa, a lokacin jama’a ba sa son a kai su aiki kauye, amma saboda ni garin mijina ne, sai na je na rike makarantar a matsayin shugabar makarantar. Bayan wasu shekaru aka mayar da ni ofishin shiyyar ilimi da ke Hadejia a matsayin jami’a mai kula da ilimin mata ta yankin masarautar Hadejia. Bayan an kirkiro Jihar Jigawa aka mayar da ni Makarantar Mata ta Garki a matsayin shugabar makarantar, daga nan ne aka mayar da ni Daraktar Kula da Tsarin Iyali a karkashin shirin ‘Better Life Programme’ a lokacin marigayiya Maryam Babangida ke nan.
Burina
Babban burina shi ne, Allah Ya sa mu cika da imani, kasancewa duk abin da nake bukata in zama na zama, kuma duk abin da nake bukatar in yi, ina yi a rayuwata. Fatana shi ne, Allah ya sa mu cika da imani, sannan ina so in gama aikina lafiya, kamar yadda na fara ban taba samun matsala ba, wato tun daga lokacin da na fara aikin gwamnati har zuwa yanzu, ina fatan in bar aikina lafiya.
Iyali
Ina da aure da ’ya’ya, yanzu ina tare da mijina da ’ya’yana da kuma ’yan uwa da abokan arziki, rayuwarmu tana tafiya kamar yadda ake so.
Ado da Kwalliya
Ni mace ce mai son kwalliya, kamar yadda duk mace mai hankali take da bukatar yin kwalliya don burge mijinta haka nima nake son kwalliya.  Kwalliya ita ce darajar mace, kuma kayan adona ba sa wuce atamfa, domin ita ce suturar da ta dace da kowanne irin yanayi na rayuwa, babu ruwanta da zafi ko sanyi, tana yi wa kowane yanayi daidai, tana kuma yi wa kowace mace kyawu, fara ce ko baka ce. Nakan hada atamfar da za sanya da hijabi, ba na iya amfani da gyale a yanzu, amma a da na fi amfani da shi, yanzu kan na fi yin adona da hijabi.
Alfahari
Na ji dadi matuka a wuraren da na yi aiki, domin duk garin da na zauna ma’aikatan da ke karkashina kan sanya wa ’ya’yansu mata sunana, wadda yanzu haka wasu da dama daga cikinsu da aka sanyawa sunana an yi musu aure, na ji dadin hakan, domin yanzu haka duk garuruwan da na zauna akwai mai sunana a garin, ba komai ya kawo haka ba sai zaman lafiya da na yi da mutane a wajen aiki.
Abinci
 Ba ni da abincin da ya wuce shinkafa dafa-duka ko shinkafa da miya, duk abincin da na ci in ba shinkafa da miya ba ce, to ba na koshi, wani lokacin ma sai in ji kamar ban ci komai ba, amma saboda larura ta ciwon suga da nake fama da ita, ya sa tilas yanzu har wake nake ci da wasu nau’ikan abinci da ba na ci a baya.
Takaicina
Nakan ji takaici da tausayi idan na ga mata a kauye ko a yankunan karkara suna sissika ko casa, wasu ma su ne suke yin noma ko su yi itacen wutar da za su yi wa mazajensu girki, ko su dauko musu ruwan sha da alwala, wannan lamarin yana ba ni takaici matuka, idan na ga mata ’yan uwana a cikin wahala. Ya kamata mazaje su ji tsoron Allah su rika sauke nauyin da yake kansu, su sani matansu da ’ya’yansu amana ne a kansu, za a kuma tambaye su a kan yadda suka rike matansu da yadda suka tarbiyyantar da ’ya’yansu, don haka ya kamata su bar matansu su nemi ilimin addini da na zamani, kasancewar na gane karancin ilimi ne yake sa mazaje danne wa mata damarsu, ba ina nufin a bar mata su yi gogayya da maza ba, ina nufin mazaje su ba mata damar samun ilimi, domin su ma su san yadda za su bauta wa mahaliccinsu, domin sai da ilimi ne komai yake tafiya daidai.

Damuwa
Ina shiga halin damuwa idan na gani ko na karanta a jarida cewar an yi wa mata kanana fyade, hakan yakan sanya ni takaici, a gaskiya akwai bukatar gwamnati ta samar da doka mai tsanani, wadda za ta hukunta duk masu aikata fyade, a samar da dokar da za ta yi wa duk wadda ya aikata laifin fyade hukunci mai tsanani da diyya mai yawa.
kalubale
Na fuskanci kalubale daban-daban a rayuwa a lokacin da nake koyarwa a makaranta, musamman a lokacin ina shugabar makaranta a Birniwa, na fuskanci kalubalen ne daga iyayen yara da malamai da leburori har da su kansu daliban, inda wasu yaran ba sa zuwa makaranta sai sun kammala aikin gida ko tallar kayan abinci.
Halayen da ba na so
Ba na son karya, domin karya tana sa mutun ya aikata komai a rayuwa, kuma ba na son yaudara, domin yaudara tana daya daga cikin nau’in munafunci.
Halayen da nake so
Ina son mai son zaman lafiya, domin babu abin da ya fi zaman lafiya komai a rayuwa. Ina bukatar a ce ina da ’yancina, ba na san takura.
Shawara ga mata
Ina ba mata shawara da su tashi tsaye wajen neman ilimi, kada su bari lalaci ya hana su neman ilimi, na addini da na zamani. Sannan su rika yin kanana sana’o’i don kashe wadansu kananan matsalolin gabansu, ba wai sai sun tambayi mijinsu ba.