Hajiya Habiba Hassan Jibrin: Burina a magance matsalar almajirai
Hajiya Habiba Jibrin ta yi gwagwarmayar rayuwa a bangaren koyarwa da aikin jarida da kuma siyasa. Ita ce mai ba Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido shawara a kan harkokin mata matsa. Ta yi fafutuka a kungiyoyi da dama wadanda suka shafi taimaka wa mata. Ta ce burinta a daina ganin almajirai a titunan Arewa. Tarihin […]
Hajiya Habiba Jibrin ta yi gwagwarmayar rayuwa a bangaren koyarwa da aikin jarida da kuma siyasa. Ita ce mai ba Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido shawara a kan harkokin mata matsa. Ta yi fafutuka a kungiyoyi da dama wadanda suka shafi taimaka wa mata. Ta ce burinta a daina ganin almajirai a titunan Arewa.
Tarihin rayuwata
Sunana Habiba Hassan Jibrin, an haife ni a garin Birnin Kudu da ke cikin jihar Jigawa a Unguwar kofar Fada cikin shekarar 1972. Na yi makarantar firamare ta Unguwar Zango a Birnin Kudu. Kakana ne ya sa ni a makarantar ni da ’yan gidanmu a lokacin ma ina karama sosai, kasancewar makarantar tana karkashin kulawarsa, a lokacin shi ne Magajin Garin Birnin Kudu. Bayan na kammala firamare sai na samu ikon tafiya makarantar Horon Malamai ta Mata (WTC) da ke kano a 1982, inda na kammala a 1988. Daga nan sai na yi fafutikar tafiya makarantar koyon aikin likita, amma ban samu dama ba, saboda a wancan lokacin babu wayewar kai, domin ana yi wa mata masu koyan aikin likita wata irin fasara kuma kasancewar na fito daga gidan sarauta, saboda martabar gidanmu da darajar mahaifana ban samu ikon yin karatun likita ba, amma duk da haka na fara karatu a makarantar koyan aikin jinya da ungozoma (school of nursing) inda a nan ma ban fi wata biyu da faraway ba mahaifana suka yi min aure tare da Alhaji Yusif Hassan Maifata da ke Kano, wanda tuni ya jima da rasuwa. An yi mini aure ina da shekara 16.
Bayan mijina ya rasu ne sai na yi sha’awar fara aikin jarida, amma kafin nan sai da na fara koyarwa kasancewar ina da ilimin aikin koyarwa.
Na fara aikin jarida ne a gidan rediyon jihar Jigawa a matsayin mai karanta labarai wadda mai girma tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma Gwamnan jihar na farko a lokacin siyasa Alhaji Ali Sa’adu Birnin Kudu shi ne ya ce mini ana neman ma’aikata a fannin rediyo, daga nan ya sa na rubuta takardar neman aiki, kuma ya tsaya mini har aka dauke ni, kasancewar ina da sha’awar aikin sai na fitar da shi kunya domin kuwa ban samu wata matsala ba tun da na fara aiki, wadda duk dacewar ina harkokin siyasa har yanzu ban ajiye aikin ba, na dai jingi ne amma har gobe ni ’yar jarida ce, kuma ina alfahari da aikin. Na fara aikin jarida a shekarar 1993.
Abin da na fi tunawa lokacin ina karama
Tun ina karama nake sha’awar wasanni da guje-guje da kuma tsalle-tsalle don ko a makarantarmu ni nake cinye gasar sanya zare a cikin allura. Haka lokacin tseren kwai a cokali da gudun buhu ni ke zuwa ta daya a wasan guje-guje irin wannan tun muna tsohuwar jihar Kano a daukacin gasar da ake gwabzawa a tsakanin makarantun jihar Kano. Nakan tuna kyaututtukan da na samu daga gwamnoni daban-daban na wancan zamanin, a lokacin ma sojoji ne suke mulkin kasar nan.
Allah da ikonsa na fara rike mukami tun ina karama domin ina aji uku aka nada ni Shugabar dalibai. Na shiga cikin kungiyoyi tun ina makaranta har zuwa yanzu. A sakandare ma na shugabanci wata kungiya. Na rike shugabar kungiyar ci gaban garin Birnin Kudu, wadda har yanzu kungiyar tana nan kuma ni ma mamba a cikin kungiyar har gobe.
Na shiga kungiyoyin masu yawa a baya kafin tsohon Gwamna Saminu ya ba ni mukamin siyasa a kan harkokin mata, wadda ita ma wannan gwamnatin yanzu haka ta nada ni a matsayin mai ba gwamna Lamido shawara a kan harkokin matasa mata wadda duk da haka bai sa na bar aikin jarida ba, idan na gama sai na koma harkokin siyasa.
Gwagwarmaya
Na yi gwagwarmayar rayuwa, na taba zama shugabar kungiyar ci gaban mata wadda jigonta yake Amurka a matsayin shugabarta a jihar Jigawa, daga nan na yi shugabar mata ta jihar Jigawa a lokacin mulkin IBB, wato a lokacin matarsa marigayiya Maryam tana da wata kungiya da ake cewa ‘better life for african women’ ni ce sakatariyar kungiyar ta jihar Jigawa.
Burina
Burina na ga talaka cikin walwala da farin ciki, hakan ne ya sa na shiga harkar kungiya domin a ganina tun da ni ba mai kudi ba ce kuma ba ni da karfin da zan iya daukar nauyin al’umma sai na shiga harkar kungiyoyi don na samu damar taimaka wa marasa karfi. Na ga talaka cikin farin ciki na sanya ni jin dadi. Ina da burin na ga yara mata sun samu ilimin zamani da na addini. Ina da kuma burin nag a matan da suke aikin gwamnati sun tsunduma cikin harkokin siyasa, su kasance rike da mukamai daban-daban, domin sai ana damawa da su ne za su samu ’yancinsu har su rika taimaka wa mata musamman ma na karkara.
Wasu na yi wa mata ’yan siyasa kallon masu zaman kansu, abin bah aka ba ne a jiharmu domin gwamnati tana taimaka wa mata wajen ganin sun shiga harkokin siyasa cikin karimci da mutunci, ba kamar yadda ake yi wa mata a wadansu jihohi ba. Ina fata mutane za su daina yi wa matan da suka shiga harkar siyasa mummunar fassara. Wannan ta sanya zuwan Lamido da kuma irin yadda aka dauki mata da muhimmanci sai mata da yawa har da karkara suka shiga siyasa, wadansu sun fara aikin gwamnati.
kalubale
Na shiga matsalolin rayuwa da dama domin da ma ai duk lokacin da ake gwagwarmaya to sai an yi a hankali. Na sha jin wadansu munanan kalamai a kaina, wadansu ma sai su kira ko su aiko mini da sakonni su rika zagina. Duk da abin yana bata mini rai sai na kira su na yi musu nasiha, idan na fahimci ba masu fahimta ba ne sai na ba su hakuri. Duk da haka bai san a canza ra’ayi a kan siyasa ba, domin burin masu hassada ka bar abin da kake yin a alheri.
Abin da ya fi bata mini rai
babu abin da ya fi bata mini rai kamar na rika ganin almajirai ko marasa gata suna yawo a kan tituna. Za ka gansu babu wanka babu wanki cikin datti mai tayar da zuciya, hakan na matukar bata mini rai. Kuma suna ba ni tausayi. Da ni mai karfi ce da na yi wani abu a kai.
farin cikina
A kullum ina alfahari da aikin jarida domin shi ne ya zama sila na duk wani abu da na zama a duniya. Ina farin ciki na fito daga gidan tarbiyya, gida na alfarma, wato gidan sarauta. Wannan ya sanya ina girmama mutane, nake ganin kowa da kima. Duk wanda ya san ni ya san ban a raina mutane. Allah (SWT) Ya halicci dan Adam, inda Y ace Ya halicci dan Adam ya kuma sanya shi cikin mafifitan daraja. Ka ga ni wace ce da zan wulakanta dan Adam.
Fatana ga marasa karfi
Abin da ya sa nake so na taimaka wa marasa karfi shi ne domin na ga sun fita daga cikin kangi da talauci, su zama mutane kamar kowa maimakon wadanda ake yi wa kallon wulakanci.