Hajiya Hadiza Bulama: Kuskure ne mata su zauna babu sana’a
Hajiya Hadiza Yerima Bulama ta rike mukamin shugabar makarantar Gobernment Girls Secondary School da ke Maiduguri, ta kuma rike mukamin Mataimakiyar Darakta a Hukumar Samar da Ayyukan yi ta kasa, sannan ta zama Darakta a sashin mata na hukumar. Bayan ta yi ritaya sai ta kafa cibiyar da ke ba mata horo don su dogara […]
Hajiya Hadiza Yerima Bulama ta rike mukamin shugabar makarantar Gobernment Girls Secondary School da ke Maiduguri, ta kuma rike mukamin Mataimakiyar Darakta a Hukumar Samar da Ayyukan yi ta kasa, sannan ta zama Darakta a sashin mata na hukumar. Bayan ta yi ritaya sai ta kafa cibiyar da ke ba mata horo don su dogara da kansu. Ta ce babban kuskure ne mata su zauna ba tare da suna yin sana’a ba.
Assalamu alaikum, sunana Hajiya Hadiza Yerima Bulama, ni ’yar Jihar Yobe ce, amma na fara karatun firamare a Kaduna, daga baya na kammala a Maiduguri a shekarar 1972, wato bayan an mayar da mahaifana aiki can. Na kammala makarantar sakandare mai suna Yerwa Gobernment Secondary School da ke Maiduguri a shekarar 1977. Na kammala digiri a kwas din kimiyyar sanin halayyar dan Adam a Jami’ar Bayero ta Kano a shekarar 1982.
Bayan na yi hidimar kasa a Jihar Bendel, na kuma dawo Maiduguri a shekarar 1984 sai aka daura mini aure da Injiniya Yerima Bulama. Mun hadu ne a lokacin da nake aiki a Ma’aikatar Gidaje ta Jihar Barno. Daga baya aka dawo da ni Ma’aikatar Ilimi, inda na zama mataimakiyar shugabar makarantar Gobernment Girls Secondary School da ke Maiduguri.
Daga nan na fara aiki da Hukumar Samar da Ayyukan yi ta kasa a shekarar 1989, na rike mukamai masu yawa a hukumar har zuwa matsayin Mataimakiyar Darakta, sannan na zama darakta a sashin mata na hukumar. Bayan na yi ritaya ne na bude ofishinta mai suna Muhadisun Consultant. Ofishi ne da ake nazari da bincike kan harkokin kanana da kuma matsakaitan kasuwanci musamman ga mata. Daga nan na bude wata cibiya mai taimakon almajirai a Abuja. Cibiyar tana koya wa almajirai sana’ar hannu kamar yin sabulun wanki da maganin kashe kwari da yin takalma da gyaran waya da sauransu, don su dogara da kansu. Ina da ’ya’ya 7 da kuma jika daya.
Abubuwan da ba zan manta da su ina karama ba
Akwai abubuwa da yawa da ba zan manta da su ba. Ba zan manta da yadda ake ‘kamu’ lokacin biki ba, a lokacin za mu yi dafe-dafe, za mu sayi biredi da sauransu, mukan je wurin kamu bayan mun yi shiga ta alfarma, a wurin za mu yi wasanni, sannan mu yi raha da hira.
Wani abin da ba zan manta ba shi ne, koyaushe lokacin muna kanana mahaifiyarmu takan yi mana nasiha mu guji yin abota da gurbatattun abokai a ko’ina muka samu kanmu, mu kasance masu ladabi da biyayya, sannan mu kasance masu haba-haba da mutane.
Farin cikin zama uwa
Na kasance cikin farin ciki bayan haihuwata ta farko, mahaifiyata tana tare da ni, kuma ta taimaka mini sosai, a lokacin ban yi komai ba, ban san yadda ake yi wa jariri wanka ba, haka na rika ganin yadda mahaifiyata take yi har na koya.
Burina ina karama
A lokacin da nake karama na so in karanta kimiyyar sanin halayyar dan Adam (Sociology), yadda ake kiran sunan kwas din ne yake burge ni, nake kuma so in san wani abu a kansa. Kodayake daga baya na kare a bangaren gudanarwa, dukkan wadannan bangarorin sun shafi abin da ya jibanci jama’a ne.
Aure yanzu da kuma a da
Abubuwa sun canza yanzu, na yi aure a shekarar 1984, a lokacin abin da za ka saya Naira 20 yanzu sai ka saye shi Naira dubu 2, don haka a yanzu an fi shan wahala a kan baya, a da kudi kadan mijinka zai ba ka ya kai ka wata, amma yanzu dole ma’aurata sai sun taimaka wa juna ta bangaren daukar nauyin iyali. Musulunci ya ce miji ke da hakkin daukar nauyin iyalinsa, amma yanzu mata suna dawainiya wajen daukar nauyin gida. A yanzu ma’aurata sai sun taimaka, wannan ya kawo gudunmuwa ta nan, wancan ya kawo gudunmuwa ta can. Kudin makarantar ’ya’ya da na haya duk sun yi tsada.
Yadda na hadu da mijina
Kamar yadda na fada a baya, na hadu da mijina a lokacin da nake hidimar kasa a Ma’aikatar Gidaje ta Jihar Barno, shi kuma mijina a lokacin yana aiki da Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Barno, a lokacin sai ya kawo wa abokansa ziyara a ofis din da nake aiki, na dauki abokansa kamar ’yan uwana, ya fada musu yana sona, suka tambaye ni ko ina sonsa na ce ‘eh’, suka tambaye shi da gaske yake ko wasa, ya ce da gaske yake yi. Bayan an tashi aiki suka ce mini yau ba za su samar damar kai ni gida ba, domin akwai wani wuri da za su je, amma mijina zai kai ne gida, ashe wani shiri ne suka yi, sun yi hakan ne don ya samu damar tattaunawa da ni, haka ya kai ni gida, a lokacin ya rika ja na da hira har ya kai ni gida. Soyayya mai karfi ta kullu tsakaninmu har muka yi aure. Abokan mijina wadanda suka hada shi da ni a lokacin su ne Injiniya Ali Gambo wanda ya rike mukamin shugaban ma’aikatan Jihar Barno da kuma Alhaji Gambo Maigoni wanda a yanzu babban sakatare ne a Jihar Yobe.
Babbar kyautar da mijina ya taba yi mini
Mijina yana sona, ina yi masa addu’ar Allah Ya kara daukaka shi, ba zan iya kirga yawan kyaututtukan da ya yi mini ba, akwai lokacin da nake so in sayi gida a Maiduguri, a lokacin ana sayar wa ma’aikata gida, ina son gida, amma ba ni da kudi; kudin rabin gida nake da shi, na zauna ina tunanin inda zan samu kudin da zan cika in sayi gida, babu abin da ba na so face aron kudi, ya gan ni cikin damuwa, bayan ya tambaye ni na fada masa damuwata, ya ce babu damuwa, ya saya mini gidan, wannan kyauta ba zan taba mantawa da ita ba.
Abin koyi
Mutum na farko da nake koyi da shi a duniya shi ne, manzon Allah (SWT), saboda ya bar mana abubuwan koyi na kwarai a duniya, sannan ina koyi da marigayiya Hajiya Maryam Babangida, ta taimake ni sosai. Ina koyi da Hajiya Hadiza Lebers da Hajiya Hamra Imam da Injiniya Babagana Zanna da Dokta Mairo Amshi da sauransu.
Yadda nake tafiyar da harkokina a yanzu
Ina da cibiyoyin da ke tallafa wa mata ne, na dora daga wurin da marigayiya Maryam Babangida ta fara ne, cibiyoyin suna horar da mata da kuma matasa kan yadda za su dogara da kansu ne, kuma na fi ba da lokacina ga cibiyoyin nawa. Nakan horar da masu ilimi da marasa ilimi. Ba na so a ce yau ga wata mace da ba ta yin komai. Kafin ka yi horar da mutum sai ka duba abin da zai amfanar da shi, misali ba za ka koya wa matar da take kauye sana’ar kawata wurin taro ba, saboda mutanenta ba su damu da yin tarurruka a dakin taro ba.
Wuraren da na fi son zuwa
Na fi so in je kauyenmu saboda a nan ’yan uwa da abokan arziki suke, amma wani lokaci nakan je kasashe kamarsu Amurka da Netherland da Afirka ta Kudu da Kenya da sauran kasashen Afirka. Na je Saudiyya.
Tufafi
Nakan sanya tufafin da zai tsare mini mutunci, na fi sanyan Laffaya, kasancewar na fito daga kasar Barno. Duk bikin da zan je za ka gan ni sanye da ita, idan ban sanya ta ba ji nake kamar ban sa komai ba.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Ina so a tuna ni a matsayin wacce ta rike gaskiya, ta kasance mai hakuri da juriya da kuma taimakon jama’a ta ko yaya ne, wato ta bangaren kudi da karfi da kuma ilimi. Ni mutum ce mai son taimaka wa jama’a, ina addu’ar Allah Ya ba mu zaman lafiya a wannan kasar.
Shawara ga mata
Babban kuskure ne mace ta zauna ba ta sana’a, komai na rayuwa ya tabarbare, ba za a gan ka da mutunci sai kana da wani abu a hannunka, ba wai na ce mata su tara kudi ta kowace hanya ba, a’a, ina nufin su samu wani abu da za su dogara da kansu, wanda hakan zai sanya a daina yi musu kallon kaskanci.