Hajiya Hadiza: Karantarwa na faranta min zuciya
Hajiya Hadiza Abdullahi babbar malama ce da ke koyarwa a Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin Sojan Najeriya da ke Kaduna( NDA). Amma kafin haka,ta koyar a wadansu Jami’o’in kasar nan. TarihinaSunana Hajiya Hadiza Abdullahi, an haife ni a shekarar 1952 a cikin watan Afirilu a garin Jos da ke jihar Filato. Na yi makarantar firamare […]
Hajiya Hadiza Abdullahi babbar malama ce da ke koyarwa a Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin Sojan Najeriya da ke Kaduna( NDA). Amma kafin haka,ta koyar a wadansu Jami’o’in kasar nan.
Tarihina
Sunana Hajiya Hadiza Abdullahi, an haife ni a shekarar 1952 a cikin watan Afirilu a garin Jos da ke jihar Filato. Na yi makarantar firamare ta ‘Saint Lukes’ a Jos, daga nan na wuce makarantar sakandare ta ‘kueen Elizabeth’ da ke Ilorin a jihar Kwara inda na samu takardar ‘WAEC’.
Daga nan sai na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda na yi karatundigiri na farko a fannin aikin gwamnati. Digiri na biyu kuma na yi shi ne a kasar Amurka a “Harbard Unibersity Cambridge Messachusetts” a fannin sanin harkokin jama’a da tsare-tsare. Takaitaccen tarihina ke nan.
Aiki
Na fara aiki ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Daga nan kuma sai na tafi Jami’ar Jos da ke Jihar Filato. Sai kuma aikin da na yi a gidan talibijin na tarayya wato NTA Jos a matsayin shugabar sashen shirye-shirye. Daga nan na sami aiki da Cibiyar Sojoji inda ake makamai (DIC) a matsayin Daraktan Gudanarwa.Amma a yanzu ina koyarwa ne a Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin Soja da ke Kaduna (NDA).
Abin da yake faranta mini rai
Ina jin dadin koyarwa domin a kullum ina jin dadin koyar da dalibaina, musamman ta fannin kara masu ilimi domin a yanzu zan iya cewa ni da dalibaina muna kara wa juna ilimi ne a kullum. Ina kuma jin dadin ilimantar da jama’a ta hanyoyi da kuma fannonin da suka shafi rayuwarsu.
Domin yin hakan, zai amfani rayuwarsu nan gaba har su kasance ’yan kasa na gari. Wannan abin shi ne yake matukar faranta mini rai ko zuciyata a duk lokacin da nake gaban dalibaina. Kamar yadda ka sani ne cewa bukatar kowace uwa shi ne ta ga ’ya’yanta sun zama mutanen kirki,haka kuma bukatar kowace malama shi ne ta ga dalibanta sun zama mutanen kirki bayan sun girma.
Abin da ba zan manta da shi ba
Akwai abubuwa da yawa da suka faru da ni a rayuwata da ba zan manta da su ba, musamman kalubalen da na fuskanta a bangaren aiki da zamantakewa da mutane da kuma kalubalen da na fuskanta a lokacin ina karatu. Amma sai dai abin farin ciki shi ne wadannan kalubale daga baya sun zame mini alheri a rayuwata.
hi ya sa ba zan iya lissafa maka cewa abu kaza ko kaza ne ba zan manta da shi ba. Sai dai kawai in yi godiya ga Allah.
Burina ina karama
A lokacin da nake karama burina in zama ma’aikaciyar asibiti (Nurse). kwarai-kwarai abin da na so in zama ke nan Nas. Sai dai a zamanin muna makaranta akan ba mu shawara wajen zabar abin da muke son zama idan mun girma. Saboda kwazona sai aka shawarce ni da cewa bai dace in shiga fannin Nas ba. Wannan ne ya sa na wuce Jami’a domin ci gaba da karatuna.
Kuma maganar da nake yi da kai a yanzu ban yi da na sanin yin aikin da nake yi ba a yanzu, wato koyarwa.
Abin da na koya daga iyayena
Na koyi dabi’u masu yawa kyawawa, kamar ladabi da biyayya a wajen su na koya. Na koyi rikon amana da yadda ni ma zan kula da nawa iyalin. Har ila yau, na koyi yadda zan zauna da jama’a lafiya ba tare da nuna kyama ko bambanci ba. Sun nuna mini cewa kowa nawa ne. Sun karantar da ni addini da duk wani abu da ’ya’ya za su koya daga iyayensu na kwarai. Tsakanina da su sai dai fatan Allah ya saka masu da aljanna.
Ya ya kike hutawa bayan aiki
Nakan hutane a dan karamin lambuna, sannan ina da sha’awar girke-girke. Bayan haka kuma ina yawan karance-karance na littattafai domin kara wa kaina sani saboda yanayin aikina.
Ina kuma da sha’awar tafiye-tafiye, idan ina cikin annashuwa nakan motsa jikina. Ta wadannan hanyoyin nake hutawa .
Hada aiki da kula da yara a gida
Gaskiya abin babu sauki, musamman lokacin da muka yi aure. Amma da yake Allah ya taimake mu da iyayen kwarai, sai abin ya zo mini da sauki. A lokacin su ke taimaka mana da rikon ’ya’yanmu idan za mu je aiki. Baya ga haka, a zamanin akwai matan kirki da ake dauka aiki domin kula da ’ya’ya da aiyukan gida ana biyansu a wata.’Ya’yanmu kan kira su ‘Iya’ mu kuma mu kira su ‘Baba’ za ka ga saboda mutuncinsu sai ka dauke su kamar ‘yan uwanka. Amma yanzu abin ba haka yake ba.
Ya ya kika hadu da maigidanki (Dariya) a gidanmu.
Wanne abu kike son a tuna ki da shi
Zan so a tuna da ni a matsayin malamar da burinta shi ne karantar da dalibanta su zama abin alfahari ga iyayensu da jama’arsu domin su kasance ‘yan kasa na gari. Wannan abin ke matukar faranta mini rai ko zuciya a duk lokacin da nake gaban dalibaina.
Ya’yanki nawa
’Ya’yana hudu, maza uku mace daya. Su Allah ya ba ni. Ina kuma godiya.
Shawara ga mata
Su yi kokarin yin karatun boko da na addini domin samun kyakkyawar rayuwa. Su rike addini domin su zamanto iyaye na kwarai. Ilimin mata yana da mahimmanci musamman ‘yan matanmu da ke Arewacin kasar nan. Ina kira ga iyaye da su tabbatar da ’ya’yansu mata sun yi karatu.