Hajiya Hadiza T. Abdulwahab: Mata na da muhimmiyar rawa a fagen siyasa
Hajiya Hadiza T. Abdulwahab ita ce Kwamishinar Mata ta Jihar Jigawa. Tsohuwar malamar makaranta ce, ta kuma yi fice a kan aikin gona. Ta rike matsayin darakta da kuma Babbar Sakatare a Ma’aikatar Hukumar Mata ta Jihar Jigawa, daga nan sai ta tsunduma harkar siyasa Tarihina Assalamu alaikum, sunana Hajiya Hadiza Abdulwahab, an haife ni […]
Hajiya Hadiza T. Abdulwahab ita ce Kwamishinar Mata ta Jihar Jigawa. Tsohuwar malamar makaranta ce, ta kuma yi fice a kan aikin gona. Ta rike matsayin darakta da kuma Babbar Sakatare a Ma’aikatar Hukumar Mata ta Jihar Jigawa, daga nan sai ta tsunduma harkar siyasa
Tarihina
Assalamu alaikum, sunana Hajiya Hadiza Abdulwahab, an haife ni a ranar 15 ga watan Fabrairu, 1963 a garin Malam Madori da ke cikin yankin Masarautar Hadejiya, a Jihar Jigawa. A yanzu ni ce Kwamishanar Mata ta Jihar Jigawa. Na yi shekara 32 ina aikin gwamnati. Na fara aikin gwamnati a mataki na uku a matsayin malamar makaranta a garin Rano da ke tsohuwar Jihar Kano tun kafin a kirkiro Jihar Jigawa. Na yi makarantar firamare a garin Malam Madori kafin na je Makarantar Horon Malamai da ke Dutse, daga nan na je Makarantar Koyon Aikin Gona da ke garin Rano, wanda daga baya na fara aiki da Hukumar Koyon Aikin Gona ta Jihar Kano (KNARDA). Bayan nan sai na yi HND a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a fannin aikin Gona a cikin shekarar 1989. Bayan na kammala wannan karatun sai aka tura ni karamar Hukumar danbatta a matsayin jami’ar aikin gona mai da kula da shiyyar danbatta.
Ina danbatta aka kirkiro Jihar Jigawa, daga nan sai na sake koma wa Jami’ar Bayero ta Kano na yi babbar difloma. Bayan nan kuma na sake koma wa jami’ar na yi digiri na biyu a kan kwas din Debelopmental Studies. Bayan na kammala sai na dawo aiki Jihar Jigawa, wanda aka ba ni mukamin darakta a ma’aikatar aikin gona amma bangaren mata. Daga nan na fara aiki a matsayin babbar darakta a Hukumar Mata ta Jihar Jigawa, daga bisani kuma na rike mukamin babbar darakta a ma’aikatar mata, wato a lokacin da Gwamnatin Saminu Turaki ta mayar da hukumar mata garin Gumel. A shekarar 2008 aka nada ni babbar sakatare a ofishin kwamashinar mata da walwalar mata ta Jihar Jigawa, inda a shekarar 2011 aka nada ni Kwamishinar Mata, wanda har zuwa yanzu ina kan wannan mukamin.
Burina
Babban burina in gama da rayuwar duniya lafiya, sannan in ga mutanen karkara suna rayuwa cikin jin dadi da walwala, musamman a ce sun samu ilimi, suna kuma yin sana’ar da za su dogara da kansu. Ina da burin in rika taimaka wa mata don su dogara da kansu.
Abin da ya fi damuna
Ina matukar damuwa game da rashin kulawar da ake nuna wa ’ya‘ya mata musamman wadanda iyayensu suke dora masu talla. A duk lokacin da na ga yarinya tana yawan talla hankalina kan tashi. Idan har da da akwai abin da zan yi a daina dora wa yara talla da na yi don a kawo karshen matsalar, kasancewar yin talla na lalata rayuwar yara. Masu tallar suna yin shige da fice a tasoshin mota da wajen da ake yin aikin gine-gine, sau da yawa birkiloli ne suka fi lalata ’ya’ya mata masu talla.
Gwagwarmaya
Na kaskantar da kaina don na koyi siyasa a wurin uwardakina Hajiya Ladi Aliyu. Har gobe ina alfahari da ita, domin ita ce ta ba ni horo a kan siyasa har kuma nake cin amfaninta, jama’ata ma suke cin amfaninta. Tabbas na yi nasara a kan abin da na koya daga wajenta, amma wasu suna yi wa mata mummunar fassarar cewa mu ‘yan a bi Yarima a sha kida ne, abin ba haka yake ba, mu fahimta addini ya ba mu kariya; ya ba kowa matsayinsa daga bangaren maza har mata, saboda haka har yanzu akwai bukatar a kara wa mata dama kasancewar suna da mahimmiyar rawar da za su taka a fagen siyasa.
A taimakawa marayu
Akwai bukatar a taimaka wa marayu domin suna bukatar taimako, kasancewar na fi kowa sanin zafin maraici, saboda ni ma marainiya ce, ban san mahaifiyata ba domin ta rasu tun ina karama. Don haka ya zama dole na tausaya wa marayu. A duk wurin da na ga maraya sai na ji tausayinsa ya kama ni.
Nasara
A gaskiya na samu nasara a rayuwa tun da na yi fice a aikin gwamnati kasancewar na shekara 32 ina aikin gwamnatin. A gaskiya a wadannan shekarun na cim ma nasarori da dama.
Taimaka wa mata
Na taimaka wa mata sosai ta hanyar shirye-shiryen ‘Tallafa wa Mata’ da kuma ‘Shirin Haihuwa Lafiya da taimaka wa nakasassu’, shirye-shiryen da gwamnatin Sule Lamido ta kirkiro. Ta mayar da hankalinta wurin taimaka wa mata musamman ta bangaren kiwon lafiya.
Gwamnati ta bullo da wadannan shirye-shiryen ne da nufin magance matsalar yawaitar mace-macen mata da kananan yara. A sakamakon wadannan shirye-shiryen a karkashin Ma’aikatar Mata an samu raguwar mace-macen mata masu ciki da kananan yara. Hakan ya sanya shirye-shiryen suka samu karbuwa a wurin jama’a.
Ina alfahari da wannan gwamnatin domin ta taimaka wa mata da dabarun aikin gona da kiwo da yin man gyada duk don a inganta rayuwar mata. Yanzu haka na sama wa mata murhun da ake yin girki masu amfani da itace kwaya daya a kokarin gwamnatin wajen hana sare dazuzzuka da kare dumamar yanayi.
kalubale
Ban fuskanci wani babban kalubale ba, domin mijina ya fahimce ni, ya ba ni babbar gudunmuwa kamar yadda ya ba ‘ya’yansa da ma duk sauran matansa. Mijina yana da burin ya ga na samu daukaka a wurin aikina, kuma na zama mai biyayya gare shi, ina yi masa abin da yake so. Don haka ina ba matan auren da suke aikin gwamnati ko siyasa su rika yi wa mazajensu biyayya.
Abin da na fi so
Na fi son a samu zaman lafiya a gidana da kauyena da rayuwata da jihata da kuma kasata, domin zaman lafiya shi ne tushen rayuwa, shi ke haifar da walwala da kuma jin dadi da kwanciyar hankali.
Shawara ga mata
Ya kamata mata su rika bin mazajensu domin aljannarsu tana karkashin duga-dugin mijinsu. Yin hakan zai inganta musu rayuwarsu, kuma za su rika tallafa wa mijinsu, ya kamata mata su kasance masu tsabta a gidajensu. Su kasance masu yin girki mai kyau. Su iya kwalliya, su kuma mazaje wato magidanta su ji tsoron Allah su kuma zama masu adalci, domin sai mazaje sun kasance masu adalci da tsoron Allah; aure zai zama mai inganci a tsakanin ma’aurata.