Hajiya Halima Ahmadu Jabiru: Ina so a tuna ni a matsayin mai taimakon jama’a

Hajiya Halima Ahmadu Jabiru ‘yar Jihar Nasarawa ce, ta yi digirinta a bangaren kasuwanci, ta yi aikin banki, daga baya kuma ta tsunduma cikin harkar siyasa, ta bayyana irin gwagwarmayar da ta yi, tana kuma so a tuna ta a matsayin wacce ta taimaki jama’a kodayaushe. Tarihin rayuwataAsalamu alaikum. Sunana Halima Ahmadu Jabiru. Babarbariyar Jihar […]

Hajiya Halima Ahmadu Jabiru: Ina so a tuna ni a matsayin mai taimakon jama’a

Hajiya Halima Ahmadu JabiruHajiya Halima Ahmadu Jabiru ‘yar Jihar Nasarawa ce, ta yi digirinta a bangaren kasuwanci, ta yi aikin banki, daga baya kuma ta tsunduma cikin harkar siyasa, ta bayyana irin gwagwarmayar da ta yi, tana kuma so a tuna ta a matsayin wacce ta taimaki jama’a kodayaushe.

Tarihin rayuwata
Asalamu alaikum. Sunana Halima Ahmadu Jabiru. Babarbariyar Jihar Nasarawa. An haife ni a shekarar 1967 a garin Lokoja, a Jihar Kogi. Na fara makarantar firamare a Holy Trinity School da ke Lokoja. Daga baya na ci gaba da karatu a Ilorin, Jihar Kwara bayan aiki ya mayar da mahaifina can. Daga nan kuma sai  makarantar sakandare ta Lafiyaji Technical College Ilorin. Bayan nan sai kueen Elizabeth College Ilorin. Daga nan aka sake yi wa mahaifina canjin wurin aiki inda na kammala a makarantar sakandaren ’yan mata da ke Garaku a Jihar Nasarawa. Daga nan sai Jami’ar Jihar Filato da ke garin Jos, inda na yi difloma a bangaren lissafi (Accountancy). Daga nan na ci gaba da karatu zuwa jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi nan kuma na karanta bangaren kasuwanci. A nan ne na samu digiri dina na farko. Daga nan aka yi mini aure da Injiniya A. J Ahmadu a shekarar 1986 wanda kuma Allah Ya yi masa rasuwa, Allah Ya sa ya huta. Mun haifi ‘ya’ya biyu; Maryam da Hasiya.
Gwagwarmayar siyasa
Na shiga fagen siyasa ne bayan na yi aiki da bankin Lion Bank plc. Wanda yanzu aka mayar da shi bankin Diamond Bank. Na kuma yi aiki da maigidana a kamfanoninsa a matsayin babbar mai lissafi (account officer) tsawon shekara 12. Daga nan ne sai na yi sha’awar shiga siyasa saboda ganin cewa ina so in ba da gudumawata wajen ci gaban Jihar Nasarawa da ma kasa baki daya. Na shiga harkar siyasa ne tun lokacin da aka kirkiro jam’iyyar PDP. Na kuma kasance daga cikin fitattun ‘yan jami’yyar PDP a wannan jiha. Na yi takarar majalisar dokoki a mazabar Lafiya ta tsakiya a shekarar 2003. Amma Allah bai ba ni nasara ba, hakan bai sa na sare ba na ci gaba da gwargwamaya a siyasa. A shekarar 2007 na sake tsayawa takarar majalisar dokokin jiha ban kuma yi nasara ba, dalilin kuwa shi ne saboda matsaloli da mu mata muke samun kanmu ciki a harkokinmu na yau da kullum ciki hard a siyasa. Kafin zaben 2011 ne tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Aliyu Akwe Doma ya nada ni a matsayin mataimakiyarsa ta musamman a bangaren ayyukan musamman (special duties) har zuwa 2011. Daga nan sai na sake fitowa takarar majalisar dokoki, bisa irin dalilin da na bayyana maka a baya, sai aka ce an kayar da ni da kuri’a daya kacal. Na kuma yarda da Allah na hakura, amma har yanzu mu ne jiga-jigan jam’iyyar PDP.
Burina ina karama
Tun ina makarantar nake harkar siyasa saboda a jinina take. Na rike mukamai tun ina firamare, na kuma rike matsayi daban-daban a sakandare. Na shiga kungiyoyi daban-daban na dalibai a wannan lokacin. Burina tun ina karama siyasa, ka ga zan iya cewa na cim ma burina ke nan.
Halayen da na koya wurin iyayena
Alhamdu llillah, iyayena sun kasance abin koyi a gare ni. Mutane ne masu horar da ‘ya’yansu yadda ya dace. Mutane ne masu nuna gaskiya da girmamawa. Sun yi mana kyakkyawar tarbiyya. A gidanmu dole kowa ya girmama na gaba da shi, ya zama mai tsoron Allah a koyaushe. Dole ne ya kasance mai kwazo don ya dogara da kansa, ba wanda zuciyarsa ta mutu ba. Shi ya sa yau muka zama masu tsoron Allah. Babu wani abu da za ka gani tattare da mu da za a yi tir ko kuma asha ba. Mukan kira mahaifiyarmu ‘soja’, saboda ba ta wargi da batun tarbiyyarmu, tun bayan da mahaifinmu ya rasu, idan za mu fita sai mun ba da kwakkwaran dalili kafin ta ba mu izinin fita.
Lura da iyali
Na gode wa Allah domin duk yinka idan ba Allah Ya taimake ka wajen tarbiyyantar da ‘ya’yanka ba, to sai ka ga ka samu matsala. ‘Ya’ya dai kamar yadda ka sani amana ne da Allah Ya ba mu. A lahira dole ne mu ba da bayani yadda muka kula da su. Da ciyarwarsu da tarbiyyarsu da kuma addininsu da hakkinsu da neman iliminsu duk Allah Ya aza mana. To daidai gwargwado abin da za ka iya yi, za ka yi kuma Allah zai taimaka maka ka samu nasara. Na samu nasara ‘ya’yana sun kasance masu tarbiyya. Dukansu sun yi karatu, sun kammala. Sun yi hidimar kasa. daya daga cikinsu ma tana da aure. Ta auri Sarkin Tula a jihar Gombe. Na gode wa Allah da Ya taimaka mini na kula da su

  1.  
    Ba a rasa kalubale a rayuwa ba komai nasarar da mutum ya cim ma. Tun muna kanana mahaifinmu kodayake ya yi iya kokarinsa wajen taimaka mana musamman a bangaren karatu. To mahaifiyarmu ce ta yi ta wahala don ganin cewa kowa ya yi karatu. To ka ga wannan ya kasance kalubale.

Wurin da nake sha’awa zuwa lokacin hutu
A lokacin hutu ina sha’awar tafiye-tafiye sosai. Haka ya sa na yi tafiye-tafiye sosai a rayuwata. Tun ma muna yara, iyayenmu da yake ba masu zama wuri daya ba ne, sun yi yawace-yawace da mu sosai. Haka ma yanzu ina yawace-yawace musamman daga lokacin da na fara harkar siyasa. Amma na fi son zuwa Saudiyya don na yi ibada a duk lokacin da na samu hutu, a can nakan samu kwanciyar hankali sosai. Ina sha’awar zuwa Afrika ta Kudu, duk yawace-yawace kasashen waje kamar su Faransa da Jamus da Holland da Dubai da sauransu, amma har yanzu ban je can ba.
Abin da nake so a tunani da shi
A gaskiya idan da wani abu da zan so a tuna da ni da shi ne- mai taimakon mutane a koyaushe. Idan na ga wani cikin mawuyacin hali kuma na taimaka masa sai in kasance cikin farin ciki da annashuwa. In kasance wacce Allah Zai yi amfani da ita don inganta rayuwan jama’a.
Tallafi daga maigida  
Alhamdu lillah. Allah Ya gafarta masa. Shi dai wannan bawan Allah tsakanina da shi sai addu’a, ya taimaka mini sosai. Shekararsa 3 da mutuwa. Duk wadannan nasarori da na cim ma, zan iya cewa sanadiyyarsa ne. Ka ga a gidansa na kammala karatuna, na kuma yi aiki a kamfanoninsa da dama a kasar nan.  Ba kawone miji ba ne musamman ma a Arewa zai yarda matarsa ta rika fitowa tana gwargwarmayar siyasa ba. Maigidana ya ba ni wannan damar. Ya ba ni dukkan goyon baya da ya kamata a ce miji ya bayar. Zan iya tunawa wani lokaci ma da idan zan fita kamfen muna tare. Wani lokaci ma da kansa yake tuka mota. Addu’ata dai a koyaushe Allah Ya biya shi da aljanna.
Kayan koli  
To, ni dai ba mace ce mai son yin kwalliya fiye da misali ba. Ni uwa ce Musulma kuma mai son zama misali ga ‘ya’yana musamman masu tasowa. Amma na fi son fita irin ta ‘ya’mace mai mutunci a idon mutane. Iyayena sun ba ni kyakkyawar tarbiyya. Saboda haka nakan yi kwalliya daidai gwargwado. Batun a yi shafe-shafe a kwaba fuska bai dace ga mace ba musamman Musulma.
Shawara ga mata     
Shawara ga mata musamman ma iyaye shi ne, Allah Ya ba mu ‘ya’ya, don haka mu dage mu yi damara mu kuma yi iya kokarinmu mu ga cewa mun ba su tarbiyya tagari. Mu kuma tabbatar sun samu ilimi na zamani da na addini don su ne za su taimaki rayuwarsu a duniya da kuma lahira. Duk wadannan matsayi da ka ga mun samu kanmu ciki mun samu tushensa ne daga iyayenmu. Mata a daina yin watsi da ‘ya’ya. A ba su kyakkyawar tarbiyya don a ci moriyarsu nan gaba. Su kuma ‘ya’ya mata masu tasowa su zama masu biyayya ga iyayensu da na gaba da su don su samu nasara a rayuwarsu. Idan ba haka suka yi ba fa to daga ba ya za su yi da-na-sani a rayuwarsu. Su kuma ‘ya’ya maza masu tasowa su zama masu biyayya ga iyayensu. Su guji shaye-shaye don hakan ba zai haifar musu da da mai ido ba. Su kuma zauna lafiya da junansu don samun nasara a rayuwa.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya