Hajiya Halima Bin Umar: Maza ku rika tausaya wa mata

Tarihina Salamu alaikum ,da farko dai zan fara da sunana, sunana Halima Bin Umar an haife ni a unguwar Kankarofi, a lokon jalli cikin birnin Kano amma mahaifina mutumin kauyan Dabi ne da ke masarautar Ringim ta nan jihar Jigawa kuma mahaifiyata mutuniyar Sumaila ce da ke jihar Kano.  Na yi makarantar firamare ta gidan […]

Hajiya Halima Bin Umar: Maza ku rika tausaya wa mata
Hajiya Halima Bin Umar: Maza ku rika tausaya wa mata

Tarihina

Salamu alaikum ,da farko dai zan fara da sunana, sunana Halima Bin Umar an haife ni a unguwar Kankarofi, a lokon jalli cikin birnin Kano amma mahaifina mutumin kauyan Dabi ne da ke masarautar Ringim ta nan jihar Jigawa kuma mahaifiyata mutuniyar Sumaila ce da ke jihar Kano. 

Na yi makarantar firamare ta gidan Makama daga nan na shige makarantar ’yan mata ta sakandire da ke Shekara inda na kammala karatuna na sakandire a makarantar ’yan mata ta GGC Dala daga nan ne mahaifana suka yi min aure kuma ba mu dade da maigidana ba muka tafi kasar Ingila.
Bayan mun dawo gida Kano na shiga makarantar Polytechanic da ke kofar Nasarawa na yi karatun zane-zane bayan na kammala ne na fara aiki da KNARDA daga bisani na yi karatun digirina na farko a jami’ar Bayero da ke Kano inda na karanta aikin jarida har ma na taba tsayawa zabe. An zabe ni Shugabar kungiyar mata ’yan jarida ta jihar Kano a wancan zamanin.
Na bayar da gudumawa a fanonin rayuwa daban-daban,musamman wajen hana yara ’yan mata talla ,domin yawon tallan ’ya’ya mata yana taimakawa wajen lalacewarsu. Na kuma bayar da gudumawa wajen hana yawan barace-barace da jama’armu ke yi.
Yanzu ina aiki ne da wata kungiya mai suna JIM THREE Bayan na bar aikin gwamnati ina aiki ne da kungiyar wajen taimaka wa jihohi ta hanyar yadda za su horar da ma’aikatansu musamman ma’aikatan kananan hukumomi yadda za su samu kudaden shiga wadda jihar za ta iya dogaro da kanta. Yanzu haka ina irin wannan aikin ne a jihar Jigawa muna bai wa kananan hukumomin jihar horon yadda za su samar da kudadem shiga.
Burina
Babban burina a rayuwa shi ne ina son na ga maza suna tausaya wa matansu. Ina son na ga maza suna jin kan matansu domin mata suna da hakki a kansu, su kula da su wajen ba su ilimi. Kuma ina son in ga an samu raguwar mace-macen mata da kananan yara musamman a lokacin haihuwa. Wannan lamari yana ba ni takaici, wato in ga mutum ya yi watsi da matarsa idan tana nakuda ba ya kulada ita.
Ina da burin ganin an samu raguwar yawaitar mutuwar aure a tsakanin ma’aurata. Saboda rayuwar aure ita ce ginshikin rayuwa da tushen kowane irin addini musamman addinin Islama domin Manzon Allah ya ce “Ya jama’ata ku yi aure ku hayayyafa domin ku zama abin alfahari a geri ni gobe kiyama idan ta tsaya.”
Ziyara
A rayuwata na yi yawo na zaga kasashen duniya daidai gwargwadon hali fiye da yadda dan Adam yake tunani. Duk da cewar ni mace ce ba wai ina tafi yawan bude ido ne a duniya ba. Duk zuwan da na yi kasashen duniya yana da sanadi ne da aiki, ko kuma sanadi da ibada. Ba wai na je ne domin kawai in yi kallon duniya ba.
A cikin kasashen duniyar da na ziyarta sun hada da kasar Saudiyya inda na je domin aikin Hajji. Na je kasashen America da Ruwanda da Engila da Pakistan da Chaina da Dubai da Maleshiya da Ethopia da Mali da kuma nan kusa wato makotanmu kasar Nijar.
kasar da ta fi ba ni sha’awa
Daga cikin kasashen da na ziyarta babu kasar da ta fi burge ni kamar kasar Amurka, saboda amanarsu mutane ne da suke da amana da kwatanta gaskiya.Ba don ba su karbi Musulinci ba ,nikan sai in ce sun dace domin duk halayensu nagari suna tafiya ne bisa tsarin koyarwar addinin Musulinci matsalarsu daya ce ba su yi imani ba. Domin a kasar Ba’amurke ne na je sayen tumatiri na ga komai na tumatirin iri daya ne amma farashi ya sha bamban.Da na tambaya sai aka ce min daya na jiya ne, daya sabo ne. Wanda idan a kasarmu ne Najeriya, duk a matsayin na yau za a sayar min. Ka ji gaskiya wadda hakan Musulmi ne ya dace a ce yanayin koyi da haka amma ba ma yi. A gaskiya halayar Turawa tana ba ni sha’awa domin suna da gaskiya wajen mu’amalarsu da jama’a.
Abin da ba na so a rayuwa
Ni abin da ba na so a rayuwata ta duniya shi ne karya, ba na son yaudara kuma ba na son yankan baya, muddin mutun ya yi min daya daga cikin wadanan babu shakka ba zan amince da shi ba.
Abin da nake so
Babban abin da nake so a rayuwata ina son mutumin da zai gaya min gaskiya komai dacinta domin duk wanda ya rasa wanda zai fada masa gaskiya ya yi hasara.A kullum na sa goshina a kasa domin na yi addu’a, nakan roki Allah na ce kada Allah ya nuna mini zamanin da ba zan samu wanda zai gaya min gaskiya ba.
Sutura
Ni a tufafi babu kayan da na fi sha’awa da ya wuce korayen kaya da shudaya .Su ne kayan da na fi sakawa domin duk mace tana da bukatar kwalliya kuma ni mace ce mai sha’awar sanya atamfa.