Hajiya Halima Bin Umar: Maza ku rika tausaya wa mata
Abinci Ni duk duniya babu abin da nake so a kayan abinci da ya wuce danwaken wake da alkama.Idan zan shekara nawa ina cin danwake ba na gajiya da shi. Sai dai ni ba na sanya magi ko ganye a cikin danwake na fi son na ci shi daga mai sai yaji sai gishiri, haka […]
Abinci
Ni duk duniya babu abin da nake so a kayan abinci da ya wuce danwaken wake da alkama.Idan zan shekara nawa ina cin danwake ba na gajiya da shi. Sai dai ni ba na sanya magi ko ganye a cikin danwake na fi son na ci shi daga mai sai yaji sai gishiri, haka nake cinsa.Idan danwake ya sha yaji ya sha kayan kanshi ya fi komai dadi a wajena.
Haka kuma ina son cin bindin sa, wato jelar sa ko kayan cikin dabba musamman a yi min farfesunsu, ko kuma farfesun kan rago ko na karfasa ko kuma kan sa duk wadannan nakan ci su ba tare da na gaji ba.
Yawan iyali
Gaskiya ina da ‘ya’ya bakwai amma na rabu da mahaifinsu wato mijina na farko ke nan yau ina da shekara 52 da haihuwa a duniya.
Abin da ba na so
Abin da ba na so a raina shi ne, ba na son in ga mata suna shan wahala misali daukar ruwa ko noma ko itace musamman a kauye, mazaje ba sa tausaya wa mata. Wasu mazajen ma har dukan mata suke yi tamkar sun samu jakai. Idan na je kauye na ga matan karkara suna shan bakar azaba saboda tausayinsu, wasu lokutun da dama nakan yi hawaye saboda tausayinsu ganin irin halin kuncin rayuwar da suke ciki.
kalubale
Na fuskanci kalubalen rayuwa, musaman a lokacin da nake aiki a KNARDA mun yi aiki da wani mugun mutun da ya rika batamin aiki. A gaskiya ban ji dadin aiki da shi ba saboda mugu ne ba ya son ya ga na iya aikin saboda yana zargina wai ina yi masa asiri, zan kore shi. Ba na nan ya sha shiga ofishina ya balle ofishina ya duba akwatin ofishina wai yana neman inda na ajiye asirin da yake tunanin na yi masa har sa ida ta kai muka yi fada ni da shi na gaya masa cewar in shi jaki ne bai san abin da yake yi ba ni na san me nake yi. Na ce masa aikina ya ishe ni ba ni da burin hada aikina da na sa ballantana har na yi masa asiri a kore shi kamar yadda yake tunani. Daga nan ne na samu sauki. Amma da kullum sai ya balle min dirowa yana neman inda na ajiye asirin da bokayensa suke yi masa karya ina yi masa ba ma maza ba.