Hajiya Halima Buba: Yadda nake hada aikin banki da kula da iyali

Tarihin RayuwataSunana Halima Buba, an haife ni a garin Michika da ke Jihar Adamawa a shekarar 1974 . Na yi karatun firamare a Zaibadari Primary School a Michika, sannan na yi Kwalajen ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) a Yola, inda na kammala a shekarar 1991. Na yi digiri na daya da na biyu a […]

Hajiya Halima Buba: Yadda nake hada aikin banki da kula da iyali
Hajiya Halima Buba: Yadda nake hada aikin banki da kula da iyali

Tarihin Rayuwata
Sunana Halima Buba, an haife ni a garin Michika da ke Jihar Adamawa a shekarar 1974 . Na yi karatun firamare a Zaibadari Primary School a Michika, sannan na yi Kwalajen ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) a Yola, inda na kammala a shekarar 1991. Na yi digiri na daya da na biyu a kwas din Business Management a Jami’ar Maiduguri. Na yi hidimar kasa da Bankin Nigerian Edport and Import Bank a Abuja, inda bayan na kammala hidimar kasa na fara aiki da bankin All State Trust Bank, inda na yi aiki tsawon shekara biyu. Daga nan na yi aikin shekara biyu da bankin Zenith B    ank. Na zama Mataimakiyar Manaja a Bankin Inland Bank, a nan ma na yi aikin shekara biyu. Daga nan na zama Manaja a bankin Oceanic Bank wanda daga baya ya zama Bankin Eco, inda na rika samun girma, daga farko na zama karamar Babbar Manaja, zuwa Mataimakiyar Babbar Manaja ta daya ta kasa. Bayan Bankin Eco ya sayi Bankin Oceanic ne aka sake kara mini girma zuwa Mataimakiyar Babban Manaja na bankin, inda nake lura ayyukan bankin a Abuja da kuma sauran jihohin arewa.
Ina da aure da ’ya’ya biyu. Ba na yarda aikina ya hana ni lura da iyalina.
Abin da ba zan manta ina karama ba
Abin da ba zan manta da shi a lokacin da nake karama ba shi ne, rayuwar makarantar sakandare, wato a lokacin da nake FGGC Yola ke nan. Akwai dalibai wadanda suka hada daga kowane yare a Najeriya a makarantarmu, ana kawo yara daga kusan ko’ina na sassan kasar nan. Na hadu da yara iri-iri, kowa da irin dabi’arsa. Na koyi abubuwa da yawa a lokacin da nake sakandare. Ba zan manta da rayuwar makarantar sakandare ba. Nakan tuna yadda muke zuwa wurare yawon kara ilimi a wadansu makarantu, inda muka yi abokai, daga nan muka rika tura wa juna wasiku, kasancewar a lokacin hanyoyin sadarwa na zamani ba su wadata ba. Babu wayoyin hannu.
Burina ina karama
A lokacin da nake karama burina in zama ma’aikaciyar lafiya, wato Nas. Ina sha’awar yadda suke sanya kayan aikinsu farare. Nakan tuna abin da mahaifiyata ta fada mini a lokacin, inda ta ce idan na zama Nas zan rika ceto rayuwar jama’a. Don haka ta ce mini na zabi aiki mai kyawu wanda zai sa in taimaki jama’a, wanda kuma ya dace da mace. Daga baya ne na fara burin in zama ’yar sanda, ban taba tsammanin zan zama ma’aikaciyar banki ba. Bayan na fara girma ne na fara burin in zama ’yar sanda, saboda ina da burin a ce yau ga shi ina bincike kan wani laifi ko wata shari’a. Bayan na kammala hidimar kasa ne sai Allah Ya sa na zama ma’aikaciyar banki.
Aikin banki
Bayan na kammala hidimar kasa ne, sai kawata ta kawo mini ziyara daga Legas, a lokacin tun da nake ban taba zuwa Legas ba, daga nan ta bukaci in bi ta Legas, a take na fada mata hakan ba mai yiwuwa ba ne, saboda ina da yakinin kawuna ba zai yarda in bi ta Legas ba. Daga baya muka kitsa labarin cewa zan je intabiyu ne da Bankin All State Trust Bank, hakan ya sanya ya ba ni wasika in kai wa shugaban bankin, saboda ajinsu daya a makarantar Kings College da ke Legas, bayan mun je ne na ba shi wasikar, inda ya tambaye ni ko ina da sha’awar aikin bankin? Na ce masa eh, inda a nan aka shirya mini tambayoyi cikin ikon Allah na samu nasara. Daga baya aka ba ni takardar daukar aiki, yadda na zama ma’aikaciyar banki ke nan.
Halayen iyayena da na fi dauka
Na fi daukar halayen mahaifiyata, saboda tana nuna damuwa da damuwar mutane, mahaifina mutum ne mai shiru-shiru, amma mahaifiyata ta mutane ce, idan wani bikinta ya taso, ’yan uwanta tun da Legas suke zuwa Yola. Nakan tuna yadda take kyauta, nakan tuna yadda take nuna soyayyarta ga mutane. Idan an yi hutu kullum za a ga gidanmu a cike, ’yan uwa da abokan arziki suna wurin mahaifiyarmu, saboda tana son mutane. Bayan ta rasu ba a samun mutane a gidanmu kamar da.

Farin cikin zama uwa
Duk matar da ta haihu za ta ji wani farin ciki ya lullube ta. A lokacin da na haihu sai na rika ganin kamar ba daga jikina dan ya fito ba, domin na ji yadda ake bada labarin irin azabar da ake sha idan an zo haihuwa. Ni dai ban sha wata wahala ba.
Yadda nake lura iyali da kuma aikin banki
Aikin banki ba abu ne mai sauki ba, ba aiki ne irin wanda za ka je da misalin 10:00 na safe, sannan ka dawo bayan wadansu ’yan awowi ba. Aikin bankin dole ka bar gida da sassafe. Nakan tuna a lokacin da nake rike da mukamin Kashiya, a lokacin babu ATM, don haka aikin ya fi wahala, kwastomomi za su yi dogon layi, kuma dole ka saurari kowa, a lokacin ban sha wahala sosai ba saboda ban yi aure ba. Babu wani nauyi a kaina. Amma da tafiya ta yi tafiya ne, wato a lokacin da na yi aure sai nauyi ya karu, wato dole na lura da gida da kuma wurin aikinka.  A wadansu ayyuka idan kana samun girma aikinka na raguwa, amma a bangaren aikin banki abin ba haka yake ba. Na ba kowane bangare lokacinsa.
Yadda nake hutawa
Nakan huta ne tare da iyalina, wani lokaci mukan je sinima mu kalli fim, sannan tare muke zuwa mu ziyarci ’yan uwa da abokan arziki.
Wuraren da nake zuwa hutu
Ba na sha’awar tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, maimakon in je kasashen waje na fi so in je kauyenmu in ji dadin lokacin hutuna da su. Nakan je kasashen waje idan tafiyar ta zama dole.
Mutane abin koyi
Akwai mutanen da nake koyi da su a bangarori da dama.  Na hadu da wata likita a lokacin da zan je Legas kwanakin baya, makwabciyata ce a cikin jirgi. A lokacin mun tattauna sosai. Mun tattauna abin da ya shafi cutar Ebola, na fada mata likitoci suna iya bakin kokarinsu wajen yaki da cutar, ta ce aikin likitocin ne su tabbata sun lura da marasa lafiya. Sai na ji ta burge ni.
Hajiya Maryam Yunusa ita ce Shugabar makarantar F.G.G.C da ke Yola a lokacin da nake makarantar ke nan, ina koyi da ita. Kyakkyawa ce, tana da fikira da fasaha da kuma basira. Ita ta koya mana yadda za mu rika tafiya da kuma magana. Ta ce mana a matsayinmu na mata bai kamata mu rika yin kowace irin tafiya ba, ta ce za mu daga kafadunmu, mu rika tafiyar kasaita, ta koya mana abubuwa masu yawa. Kullum na tuna sai na yi mata godiya.
Ado
A wurina ado shi ne duk wani tufafi da za ka sanya da zai rufe maka jiki, idan za ka yi ado ba lallai sai ka sanya tufafin da ake yayi ba. Ina son kwalliya da ado amma saboda yanayin aikina, inda ake da tsarin tufafin da ma’aikaci zai sanya, hakan ya sanya nake sanya tufafinmu na gargajiya. Ina son atamfa
Al’ada
Ina son duk wata al’adarmu, tun daga rawarmu da abincin da kuma tufafin da muke sanyawa.
Darussan da na koya a rayuwa
A rayuwa na koyi kada mutum ya fitar da rai idan yana neman wani abu, na koyi in rika karfafa wa kaina gwiwa da cewa ‘eh zan iya cimma burina a kan kaza da kaza’. Idan ba mu tsaya kai-da-fata don ganin bayan kalubale ba, to ba za mu cimma burinmu ba.
Nasarori
Na gode wa Allah a matsayin da na samu kaina. Ba zan bayyana nasarorin ba, saboda ba karfina da wayona ba ne ya kai ni ga cimma su ba, don haka ina gode wa Allah bisa mukaman da na rike, ’ya’yan da ya azurta ni da su da kuma lafiyar da ya ba ni.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Ina so a tuna da ni a matsayin mace mai kamala da yakana, a tuna da ni a matsayin mai son jama’a, wacce kuma ta taimaki jama’a.