Hajiya Hauwa Musa: Lalacewar tarbiyya ba daga karatun boko ba ne

Hajiya Hauwa Musa, gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati ce. Ta yi shekara 30 tana aikin gwamnati kafin ta zama mai taimaka wa Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe Hajiya Ummu Adama Ibrahim Hassan dankwambo, a bangaren harkokin mata da rage talauci. Ta ce lalacewar ‘ya’ya mata ba daga karatun boko ko rashinsa ba ne. TarihinaSunana Hauwa Musa, ni ’yar […]

Hajiya Hauwa Musa: Lalacewar tarbiyya ba daga karatun boko ba ne

Hajiya Hauwa MusaHajiya Hauwa Musa, gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati ce. Ta yi shekara 30 tana aikin gwamnati kafin ta zama mai taimaka wa Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe Hajiya Ummu Adama Ibrahim Hassan dankwambo, a bangaren harkokin mata da rage talauci. Ta ce lalacewar ‘ya’ya mata ba daga karatun boko ko rashinsa ba ne.

Tarihina
Sunana Hauwa Musa, ni ’yar asalin kabilar Terawa ta karamar Hukumar Deba ce. An haife ni a garin Deba cikin shekarar 1965 kimanin shekara 48 ke nan. A garin Deba na yi kuruciyata har na girma aka sanya ni a makarantar firamare, wato Central Primary School a Deba cikin shekarar 1970 zuwa 1977, inda na yi aji bakwai da na gama sai na tafi Sakandaren Gwamnati ta ‘Yan mata a Doma (GGSS Doma) a shekarar 1977 zuwa 1982, bayan na kammala aka yi mini aure. Na fara aiki ne a tsohuwar karamar Hukumar Deba a 1982, sannan a shekarar 2002 zuwa 2003 na tafi ASCON a Badagri a Legas da goyon bayan maigidana da kuma mahaifina.  A lokacin karatu a  ASCON sai kai wane ne ko wane ne ya daure maka gindi. Allah Ya taimake ni sai Ya’u Deba (YD) ya taimaka na samu tafiya inda na yi satifiket a CPA, inda na samu matsayi na farko (distinction) sai suka ba ni damar karo na biyu, wato dai a nan na yi babbar Difiloma (PGD) a bangaren tsarin mulkin al’umma (Public Administration), da ma tsarinsu kuma idan ka samu Distinction za a ba ka dama ta biyu ka yi PGD.
Aiki
Na fara aiki ne a karamar Hukumar Deba daga shekara ta 1982 zuwa 1986, sai na nemi canjin wajen aiki na koma gwamnatin jiha a ma’aikatar yada labarai bangaren Nazari da Fadakarwa (Research and Publicity) har zuwa shekarar 1990. A shekarar 1990 na bar aiki da gwamnatin jiha na kuma sake koma wa inda na baro wato karamar hukuma har zuwa shekara ta 2012, inda a lokacin ne Uwargidan Gwamna Hajiya Ummu Adama Ibrahim Hassan dankwambo ta ba ni mukamin mai taimaka wa mata a bangaren harkokin mata da rage radadin talauci.
kalubalen aiki
Kai a gaskiya na yi fama da kalubale saboda a lokacin da nake aikin ina da aure, ga shi kuma na fara haihuwa kuma mijina ma’aikaci ne, ina bin sa duk wurin da aka yi masa canjin aiki, hakan ya sa na yi ta samun koma baya na rashin samun girma a kan lokaci, bugu da kara ga shi na hada tarbiyyar ’ya’ya da aikin ofis, wanda idan mace ba ta dage ba dole ta fuskanci matsala.
Nasara
Na samu nasara wurin aikina saboda ko da mukamin mai taimaka wa Uwargidan Gwamna da aka ba ni ta dalilin aikina ne na samu, saboda a inda nake aiki a karamar hukuma waje ne da muke cudanya da mutane daban-daban da suka hada da ’yan siyasa da wadanda ba ’yan siyasa ba, ashe kuwa in haka ne na samu nasara ke nan.
Yadda na shaku da ‘ya’yana
 Na shaku da ‘ya’yana da iyalina baki daya domin duk lokacin da kaina ya yi zafi ko a wurin aikina ne har a bangaren da nake S.A su suke kwantar mini da hankali, saboda a wasu lokuta su ne abokan shawarata, suna iya sanin halin da na shiga na dadi ko akasinsa, kuma duk da cewa ni mahaifiyarsu ce  sukan ba ni shawara idan na ga ta dace nakan yi amfani da ita sosai.
Yadda dangantaka ta take da Uwargidan Gwamna
A matsayina na mai taimaka mata muna da kyakkyawar dangantaka saboda ba na mata shisshigi a al’amuranta, na fi tsayawa a kan abin da ta umurce ni, kuma ba na kawo mata son rai a harkokin da ta sani saboda amana ta dora mini, kuma ina son in ga na tsaya iya inda ta tsayar da ni, shi ya sa tun da muka fara aiki ba mu taba samun wata matsala ko sabani na rashin fahimtar juna da ita ba.
kungiyoyi da kasashe
Ina cikin kungiyoyi da yawa, a wasu ina daga cikin shugabanni, a wasu kuma mun yi shugabanci mun sauka, misali kungiyar Mata Musulmi ta kasa reshen jihar
Gombe FOMWAN. A yanzu ni ce Shugabar kungiyar ci gaban Matan Deba, (Deba
Woman Association)  sannan mataimakiyar shugaba ta 1 a kungiyar hadin kan mata ta kasa NCWS, Mamba kuma  a kungiyar Annur Woman Multi-Purpose, ban je wasu kasashe masu yawa a fadin duniyar nan ba amma dai na je Saudiyya da Dubai.
 Burina
Burina shi ne bayan na gama aiki da Uwargidan Gwamna Hajiya Ummu Adama Ibrahim Hassan dankwambo sai na huta, na ba ‘ya’yana isasshen lokaci. Idan kuma gwamnati za ta ba ni dama in sake koma wa aiki a matakin jiha zan ci gaba, amma ba zan koma karamar hukuma ba.

Yawan iyali.
Alhamdu lillahi ‘ya’yana shida, maza biyu; mata hudu. A ciki akwai tagwaye. Biyu daga ciki sun kammala jami’a sauran suna matakin karatu daban daban na Sakandare.
Shawara ga iyaye
A matsayina na ‘ya mace kuma uwa ina mai ba iyaye shawarar su dinga barin  ‘ya’yansu mata suna karatun boko da na addini, saboda ilimi shi ne gishirin rayuwar dan Adam musammam ma ‘ya’ya mata, saboda su ke da alhakin tarbiyya a cikin gida ba uba ba, ina kuma jan hankali wasu iyaye da suke cewa idan ‘ya mace ta yi karatun boko ne take lalacewa ba, ba gaskiya ba ne, lalacewar ‘ya mace ba daga karatun bokonta ba ne ko rashin sa ba ne a, a lalacewa na samo asali ne daga rashin tarbiyya da kuma rashin ilimi, domin yau idan mace ta yi ilimi ta san yadda za ta tafiyar da rayuwarta fiye da wacce ba ta yi ilimi ba, kuma nan gaba wani lokaci zai zo da kafin a auri mace sai an tambayi wane matakin ilimi take da shi sakandare ne ko jami’a saboda namiji ba zai yarda ya auri macen da ba zai yi riba da ita ba wajen taimaka wa gida; shi ya kawo ita ma ta kawo, idan ba ta yi ilimi ba ka ga sai ta yi ta zama a gidansu Allah Ya sawwake. Sannan kuma dora wa ‘ya’ya mata talla bala’i ne domin tarbiyyar mace da farko ya fi lalacewa a wajen talla, ba ina hana iyaye dora wa ‘ya’yansu talla ba ne, a,a, ita uwa ko a cikin gida za ta iya yin jauranta, ana zuwa ana saye ba sai ta dora wa ‘yarta ta fita kwararo-kwararo ba, har ma wata uwar ta ce wa ‘yarta idan ta dawo gida da kwantai za ta yanka ta hakan ba daidai ba ne.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya