Hajiya Hindatu Umar Abdullahi: Taimaki mutum a lokacin da ya dace

Hajiya Hindatu Abdullahi ta kasance tsohuwar ma’aikaciya wadda ta rike mukaman gwamnati daban-daban.A yanzu ita ce Darakta ta Ma’aikatar Ilimi da ke Abuja.Haka nan kuma a bangaren sarauta ita ce Ayyanar Daura a jihar Katsina. Daga Binta Aminu Saleh Tarihin rayuwataSunana Hindatu Umar Abdullahi an haife ni a garin Daura da ke jihar Katsina .Kuma […]

Hajiya Hindatu Umar Abdullahi: Taimaki mutum a lokacin da ya dace

Hajiya Hindatu Abdullahi ta kasance tsohuwar ma’aikaciya wadda ta rike mukaman gwamnati daban-daban.A yanzu ita ce Darakta ta Ma’aikatar Ilimi da ke Abuja.Haka nan kuma a bangaren sarauta ita ce Ayyanar Daura a jihar Katsina.

Daga Binta Aminu Saleh

Tarihin rayuwata
Sunana Hindatu Umar Abdullahi an haife ni a garin Daura da ke jihar Katsina .Kuma daga cikin masarautar Daura na fito.Ina daya daga cikin mata kalilan da suka sami damar yin karatun boko a wannan gari namu.Na fara karatu a makarantar firamare ta Daura ‘1’ a shekarar 1963 .Na tafi Makarantar Sakandare ta ‘Yan mata ta Kankiya a shekarar 1970.Daga nan kuma sai na tafi Makarantar Share Fagen shiga Jami’a da ke Zariya a jihar Kaduna.A shekarar 1977 na tafi Jami’ar Bayero da ke Kano inda na yi karatun digiri a fannin harshe Hausa.Na yi hidimar kasa a makarantar Horar da Malamai ta Minjibir da ke jihar Kano.
Aiyukan da na yi
Na fara aikin koyarwa a wannan makaranta da na yi ta Zaria wato Makarantar Share Fagen shiga Jami’a.Na bar wajen lokacin da aka kirkiro sabuwar jihar Katsina daga tsohuwar jihar Kaduna a shekarar 1988.Saboda haka sai aka mayar da mu jihar Katsina mu je mu yi aiki. Sai aka ba ni shugabancin makarantar ‘W.A.T.C’ da ke Dutsin- Ma.Bayan ’yan watanni sai aka canza ni na koma shugabar waccan makaranta da na yi ta sakandare ta ’yan mata ta Kankiyi.A wannan shekarar ta 1988, lokacin Gwamna Kanal Abdullahi Sarki Mukhtar ya kawo ziyarar aiki wannan makaranta,ya yaba da yadda ake gudanar da makarantar.Bayan kwana biyu aka ba ni Kwamishinar Watsa Labarai da aikin Laburare ta wannan Jiha, na yi mamaki matuka,amma kasancewar mutum musulmi mun san komai daga Allah yake.Ana nan kuma sai na sami canjin aiki na koma Kwamishinar Ma’aikatar Walwalar Jama’a da Matasa da Wasanni.Na rike Ma’aikatar Ilimi na wani dan lokaci,ina kula da Ma’aikatar Watsa Labarai kuma ina kula da Ma’aikatar Ilimi,lokacin da Kwamishinan Ilimi ya yi wata ’yar tafiya.Bayan an yi canjin Gwamna kuma mun dan fara aiki da shi sai aka sauke mu .Saboda haka sai na koma Ma’aikatar Ilimi aka ba ni wani ofis na Babbar Ma’aikaciya mai kula da Ilimin Mata.Bayan wata biyu sai aka ba ni matsayin Mukaddashin Daraktan Ilimi a shekarar 1990 . A shekarar 1993 aka ba ni shugabancin Makarantar ‘Yan Mata ta Bakori ta Gwamnatin Tarayya,domin an sami wata ‘yar matsala sai aka ba ni shekara biyu in je in yi wannan aiki.Bayan shekara biyun sai aka ce sai in ci gaba da wannan aiki.Sai aka mayar da mu karkashin Ma’aikatar Ilimi ta Gwamnatin Tarayya.A shekarar 1998 lokacin Shugaban kasa Abdussalam Abubakar aka nada ni Kwamishinar Zabe,ta Jihar Edo.Da ikon Allah muka yi wannan aiki muka gama lafiya.Daga nan kuma sai aka dawo da ni Kwamishinar Zabe ta Abuja(FCT). Lokacin maigirma Obasanjo sai aka canza Kwamishinonin Zabe ,saboda haka sai na sake dawo wa Ma’aikatar Ilimi.Sai aka ba ni Mataimakiyar Darakta a nan hedikwata.Na zauna a ofishin da yake kula da Ilimin Mata da Yara ‘Yan mata,na zauna a ofishin da yake kula da Ilimin Makarantun Sakandare na Jihohi da Makarantu masu zaman kansu,na zauna a karkashin fannin Kula da Ilimi na bai daya.Na yi aiki a ofishin da yake kula da Ilimi na Musamman ,da tafiya ta mika, sai na zama Darakta.Sai aka kai ni Ma’aikatar kula da ba da Tallafin Karatu.Sai aka dawo da ni sashen kula da Ilimin Makarantun Gaba da Sakandare.To a nan nake a yanzu cikin ikon Allah,kin ji tarihina.
Sarauta
A tsarin Masarautar Daura, kamar yadda tarihi ya nuna mace ta yi sarautar Daura wato Sarauniya Daurama.Saboda haka har yanzu mata suna da matsayi a sarautar Daura. A shekarar 2012 aka nada ni Ayyanar Daura domin killace wannan suna na Ayyana. Na karba na rike ,har yanzu ina rike da wannan sarautar.Wato Ayyana ita ce wadda ta sauki bakonta Bayajidda kuma ta karrama shi kamar yadda tarihi ya nuna.Domin ganin muhimmancin rawar da wannan tsohuwa Ayyana ta taka a tarihi, ya sa Masarautar Daura ta ga bai kamata a bar wannan suna haka ba. Daga kaina aka fara wannan sarautar. A yanzu haka ina da matsayi a cikin hakiman kasar Daura.

Abin da yake faranta min rai
Zama na Shugabar Makarantar ‘Yan Mata a Bakori ya sa ni jin dadi kuma na yi alfahari da kaina.Domin kuwa lokacin da na je makarantar duk al’amura sun tabarbare, da al’amarin mutum ne, sai a ce a shekaru shida ma ba za ta gyaru ba.Amma bayan zuwana da shekara daya ko biyu,komai ya canza.
Abu na biyu kuma shi ne zamana a jihar Edo a matsayin Kwamishinar Zabe.Domin kuwa komai ya tafi cikin nasara da ikon Allah.
Hada aiki da aikin gida
Duk macen da kika gani ta hada aiki ko karatu da aikin gida kuma ta sami nasara, ba karamar jaruma ba ce.Na yi aure, ina shekara ta biyu a Jami’a,na sami ciki, na haihu ga jarrabawa ga aikin gida. Da na fara aiki ma abin haka yake.Hada wadannan abubuwa ba karamin abu ba ne.Kafin ki fita sai kin tabbatar kin shirya abincin maigida.Idan kin tashi sallah to ba za ki koma barci ba.Idan kin idar da sallah maganar kicin ce.Idan kin fita da rana ta yi za ki fara tunanin gida.Bari in fada miki idan na dawo gida a kicin nake jefar da mayafina da jakata sai dai a dauke a kai min daki.Bayan aikin gida kuma ga kula da ’yan’uwa da abokan arziki.
Iyali
A yanzu ina da ’ya’ya biyar,hudu maza,mace daya.Duk sun gama karatunsu na digiri ,karamin ne kawai yake makarantar sakandire.
Burina ina karama
Da,burina in zama malamar asibiti wato Nas .Abin da yake ba ni sha’awa shi ne kayan da suke sakawa fari da ‘yar hular nan.Bayan mun gama sakandire sai mu shida muka sami shiga makarantar koyon aikin jiyya,amma Babana ya fi so in tafi Jami’a,har mun yi jarrabawar farko bayan sati goma,kuma sai sakamakon jarrabawarmu na makarantar sakandire ya fito sai Babana ya ce in zo in tafi Makarantar Share Fagen shiga Jami’a.Amma kuma ni ma a lokacin sai na ga aikin Nas bai dace da ni ba.Domin kuwa a tsorace nake,kullum sai na yi mafarkin mutuwa saboda ga mu ga dakin marasa lafiya.Ga shi kuma ina sha’awar aikin.

Yadda nake hutawa
Mukan dan tattaka mu motsa jiki da safe ,nakan dan zauna in huta in yi karatu kuma nakan saurari kade-kade.
kasashen da na ziyarta
Alhamdulillahi, mun yi tafiye-tafiye da yawa ta bangaren maigidana da kuma ta bangaren aiki da kuma ta bangaren ni kaina.kasar Saudiyya da ma burin kowane musulmi ne ya je.Mun je Dubai, mun je katar.Na je Turkiyya ,na je Astaraliya, na je China, na je Uk, na je Amurka , na je Kanada, na je Faris.Wadanda zan iya tunawa ke nan.
Nasarori
Na ce miki ka hada wadannan abubuwa guda biyu ,gida lafiya gurin aiki lafiya,ai maganar nasara ta kare.
kalubale
Wato kalubalen shi ne musamman idan ka sami kanka maza da mata suna karkashinka,sai ka yi namijin kokari,ka nuna ba ka gaza ba.Domin ko ya ya aka sami dan akasi sai a ce ‘Ai dama mace ce’.Ban taba samun wannan ba,amma ina gaya wa zuciyata cewa ina da shi,amma kada in bari ya fito.Saboda maza suna ganin mata ba za su iya ba.Sai nake kokarin guje wa wannan gazawar.
Darasi
Duk abin da za ka yi ,ka yi saboda Allah. Kuma ka taimaki mutum a lokacin da ya dace.Kada ka nufi kowa da mugun abu,to ko da wani ya nufe ka da sharri ba zai ci nasara ba.Kuma na koyi zama da mutane daban-daban.
Mutanen da nake koyi da su
Akwai mutane uku,mahaifiyata da mahaifina da kuma maigidana.Dukkansu halayensu ne ya ba ni ginshikin tarbiyya.Mahaifina yakan yi wasa da mu amma ba ya son wargi.Ni ce babba a gidanmu,mahaifina yakan nuna wa kannena girmana.Mahaifiyata kasancewar ni ’yar fari ce, ba ta sakar min fuska ba.Na san inda zan ajiye jakar makarantata na san inda zan dauka.Kuma da aka yi mini aure sai mijina ya ci gaba.Domin shi ba a fada da shi komai sai ya ce ‘A yi hakuri’.Saboda haka wadannan su ne ababen koyi a wajena.
Yadda na hadu da maigidana
(Dariya)lokacin da muka hadu gaskiya ba maganar aure,maganar aiki ce.Daga baya kuma abubuwa sukan faru saura kuma su zama tarihi, sai Allah ya kawo auren.
Burina
Shi ne in ga na yi ritaya na bar aiki lafiya domin in ci gaba da kara mayar da hankali ga ibada ,kuma mu yi fatan cikawa da imani.
Shawara ga mata
Mu yi kokari mu san cewa yanzu lokaci ya wuce,dole mata mu fita mu nemi ilimi kuma mu sa ido ’ya’yanmu su yi ilimi.Abin da ya sa na ce lallai mace ta yi karatu shi ne,lokacin da muka bude makarantar mata a gidanmu sai muka sami wasu dattawa mata ba su san tsarki da alwala da salla ba.To wane addini mutum yake yi?Lallai ne mu nemi ilimin boko da na addini.Mutane sukan hada ilimin boko da gurbacewar dabi’a da al’ada,wannan ba dai-dai ba ne.Ilimi nutsuwa yake karawa,idan kuwa aka sami akasi to mutum shi ya so.