Hajiya Khadija kassim: Mata a rika kai ajiya bankuna

Hajiya Khadijah Kassim ita ce Mataimakiyar Darakta a Sashin Kare Harkokin Masu Hulda da Bankuna na Babban Bankin Najeriya. Ta bayyana irin nasarorin da ta samu a tsawon kusan shekara 30 da ta yi tana aiki a Babban Bankin Najeriya. Ta yi bayanin yadda take taimaka wa al’umma da kuma karfafa wa mata gwiwa kan […]

Hajiya Khadija kassim: Mata a rika kai ajiya bankuna
Hajiya Khadija kassim: Mata a rika kai ajiya bankuna

Hajiya Khadijah Kasim tare da ’ya’yanta A’isha Yagana, Ummu Kulsoom, Hajara Nana.Hajiya Khadijah Kassim ita ce Mataimakiyar Darakta a Sashin Kare Harkokin Masu Hulda da Bankuna na Babban Bankin Najeriya. Ta bayyana irin nasarorin da ta samu a tsawon kusan shekara 30 da ta yi tana aiki a Babban Bankin Najeriya. Ta yi bayanin yadda take taimaka wa al’umma da kuma karfafa wa mata gwiwa kan mahimmancin sana’a tare da yin ajiya a bankuna.

Tarihina
Assalamu alaikum, sunana Khadija Kassim, ina da shekara 50. An haife ni a layin Sarkin Arab da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato. Na fara makarantar firamare a Seben Day Adbentist a Laranto, bayan na shafe shekara 5 a can, sai na koma makarantar Methodism na yi shekaru 2, inda na kammala makarantar firamare. Daga nan na shiga makarantar sakandire mai suna Sardauna Memorial Islamic College da ke garin Jos. Na shiga wannan makaranta a shekarar 1975 na kammala a shekarar 1980.
Bayan haka, sai na wuce zuwa makarantar share fagen shiga jami’a da ke Zariya, daga nan na samu shiga  Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.  Na yi digiri  a fannin dangantakar kasa da kasa (International Relations). Na kammala jami’a a shekarar 1984.
Na yi hidimar kasa a Hukumar Sadarwa ta kasa a Legas, bayan na kammala hidmar kasa sai fara aiki a Babban Bankin Najeriya. Na fara aikin ne a watan Disamba1985 har ya zuwa wannan lokaci. Na yi shekara 4 a Legas, daga nan na dawo Jos na yi kusan shekara 20. Daga nan kuma aka mayar da ni hedkwatar Babban Bankin Najeriya a Abuja.
Nasarori
A gaskiya mun gode Allah domin tun da na  fara wannan aiki kusan shekara 30 ke nan, amma ba a taba samun mutum da aikata wani laifi ba, wannan babbar nasara ce. Babban Bankin Najeriya ya yaba mini kwarai, bankin ya ba ni lambobin yabo daban-daban.
 kalubale
Yawancin mu mata abin da muka dauka shi ne, idan ana son a san mace ta iya aiki, sai mu ce sai ta yi aiki fiye da maza tukunna. Amma mu mata mun gode wa Allah da muka samu kanmu a Babban Bankin Najeriya, duk matar da take aikinta tsakaninta da Allah, ta nuna kwazo ba za a take mata hakkinta ba. Don haka ni ban samu wani kalubale a wajen aiki ba.
Amma kuma kalubale irin na rayuwa, tun muna kanana mun samu kalubale da dama. Domin a da ba a son ‘ya mace Musulma ‘yar Arewa ta yi karatu, ka ga idan iyayenku ba su tsaya muku ba, babu inda za a yarda ku yi karatun. Na gode Allah domin tun da na shiga makaranta, Allah Ya ba ni baiwa, ina da kwazo da kokari, don haka malamaina suka yi ta karfafa mini gwiwa. Kuma Allah Ya taimake ni iyayena suka tallafa mini har Allah Ya sa na je jami’a, na kuma samu wannan aikin da nake yi.
Yadda nake taimaka wa al’umma
Dole ne mu taimaka wa al’ummarmu saboda wannan matsayi da Allah Ya ba mu, wata rahama ce, ba wai don mun fi kowa ba ne. Don haka duk mutumin da ya yi la’akari da wannan, kuma ya tabbatar yana da imani, ba zai ji dadi ba idan ya ga wasu suna cikin wahala. Dole ne ya tashi ya taimaka gwargwadon abin da zai iya yi. Musamman al’ummarmu a garin Jos, kowa ya san kalubalen da muke ciki.
A yau maganar tarbiyyar ‘ya’ya ma kadai ta ishi iyaye, ga wahalar samun abin da za a iya tarbiyyartar da ‘ya’ya ko kuma ba su ilmi. Saboda haka da Allah Ya kawo ni wannan matsayi, sai na ga cewa ya kamata in hada hannu da sauran ‘yan uwa mu taru mu taimaka daidai gwargwado. Wajibi ne mu tashi mu taimaka wa jama’a ko ta baiwar ilmin da muka samu ne, ko kuma ta abin hannun da Allah Ya ba mu.
kungiyoyin da nake ciki
Akwai kungiyoyin da suka shafi harkokin banki da dama da nake ciki. Bayan haka akwai kungiyoyin taimakon jama’a da dama da nake mara musu baya, kuma duk kungiyoyin da suka zo suka tunkare ni kan abubuwan da suke yi na taimakon al’umma ko na taimakon ‘ya’ya mata, musamman wajen ilimintar da ‘ya’ya mata a kowanne lokaci, ina kokarin hada kai da irin wadannan kungiyoyi don taimaka musu da abin da Allah Ya hore mini.

 Iyali
Allah Ya ba ni ‘ya’ya guda 3, akwai A’isha Yagana da Ummul Kulsoom da Hajara Nana Aliyu-Bima. A halin yanzu ita A’isha  tana karatu a Turai, Ummul Kulsoom da Hajara Nana suna nan gida suna karatu a makarantar sakandire.  Allah ya yi wa mahaifinsu rasuwa.
A gaskiya na shaku da ‘ya’yana, ta haka na iya ba su tarbiyya. Don haka ni a ganina jan ‘ya’ya a jika yana da matukar mahimmanci. Domin za ka san halin da ‘ya’yanka suke ciki. Idan abu ya dame su, su gaya maka don ka san abin da za ka yi a kai.
kasashen da na ziyarta
Albarkacin wannan aiki da nake yi, mun ziyarci kasashe da dama. A kasashen Afrika na je Afrika ta Kudu da Kenya da Ghana, haka kuma na je kasashen Turai kamar Faransa da Ingila da Jamus da Italiya da dai sauransu. Haka kuma a kasashen Larabawa na je Dubai da Saudiyya.
Burina bayan ritaya
To, a yanzu ina noma, kuma burina bayan na yi ritaya shi ne noma. Kamar yadda na fada na riga na fara noma. Daga nan kuma zan ware lokacina wajen ba da gudunmuwa don ilmintar da mata da yara kan irin ilmin da muka samu a wannan aiki.
Abin da nake son a rika tuna ni da shi
Zan so a rika tunawa da ni a matsayin wadda ta tashi ba ta manta da baya ba, kuma  wadda ta taimaki al’umma. Haka kuma zan so a rika tunawa da ni a matsayin wadda ta zauna da mutane lafiya, domin duk wanda ya san ni ya san cewa ni ko wace ce, ko na hadu da shi, ina son mu zauna lafiya mu rabu lafiya ana begen juna. Duk abin da ba na son wani ya yi mini ina kokarin kiyayewa.
Tufafi
Tufafin da na fi so a matsayina na ‘yar arewa Musulma shi ne, tufafi mai kyawu  wadda idan an ga  mace  za a ce ta yi shiga ta mutumci.
Abinci
A cikin abincin da nake so akwai doya da shinkafa, kuma ni mai son shan shayi ne, ban sani ko don ni ‘yar Jos ba ce, domin kowane abinci zan ci, nakan sha shayi. Amma ina cin tuwon masara da miyar kuka ko da miyar dage-dage.
Shawara ga mata
Yanzu lokacin da zaman banza ya wuce, don haka shawara ta ga mata ya kamata su samu sana’a. Sana’ar nan ba lallai ne sai mutum ya fito ya yi aiki a waje ba, ko a gida ne ya kamata mace ta nemi wata sana’a wacce za ta taimaka wa kanta da mijinta da iyalinta. Kuma ina son mata su koyi tattali da ajiya, wannan yana da mahimmanci sosai da sosai.
Yanzu ga tsare-tsaren bankuna nan da muke fada. An kawo tsare-tsare daban daban, mace za ta iya kai ajiyarta kadan-kadan, wata rana in tana neman taimako, za a iya taimaka mata ta karfafa jarinta. Amma a ce mace ta zauna ba ilimi, babu wani aiki da take yi musamman a wannan hali da muke ciki, a gaskiya akwai wahala. Amma ya kamata mata su san cewa duk abin da za su yi, su zama masu ladabi da biyayya ga mazajensu da kuma taimaka wa mazajensu, kuma su tarbiyyantar da iyalinsu domin a samu al’umma tagari.